Connect with us

Kanwar Maza Book 3 Page 1

Hausa Novels

Kanwar Maza Book 3 Page 1

Barka da zuwa shafin mu na hausa novels inda muka kawo muku littafin Kanwar Maza Book 3 Page 1

Kanwar Maza Book 3 Page 1

Kanwar Maza Book 3 Page 1: A hankali ya rufe datarsa, ya yi shiruu yana tunanin mai ya yi wa mutane haka, da har wasu suka sanya rayuwarsa a gaba suka mayar da ita hanyar su ta neman abinci.

A hankali ya ajiye wayar ya kunna motarsa ya tafi.

Baba uwani ce durƙushe a gaban Mummy, jikinta sai rawa yake yi, Mummy ta dubi baba uwani ta ce “Uwani me ki ke nufi ne? Ƴan kwanakin nan duk wasu ayyuka da na sakaki ba kya iya yi mini, sannan babu wani rahoto da ki ke kawo mini”

“Tuba nake ranki ya daɗe, ayi mini afuwa, ayi mini aikin gafara”.

Ta ɗan ja numfashi ta ce “Yarinyar da aka ce ta zo da ɗan wurin Adam an ce ta na zuwa gidan nan haka ne?”

Baba uwani ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Wallahi ba na ce ba uwar ɗakina, kin san yaron ko fito da shi daga sashin giwa ba ayi, babu wata hadima da aka amincewa zuwa in da yaron yake, ciki har da ni, dan haka ba na ce ba, amma akwai wata yarinya da take yawan zuwa, ban san alaƙarsu ba, amma zan iya cewa ita ce dan kuwa kwanaki na ji an ce za a kaita wurin mai girma turaki, amma abun da ya sa ban gazgata ita ce ba, yarinya ce fa sosai bana tunanin ita ce”.

“Ba tunaninki nake son ji ba, abu ɗaya zan saka ki, daga yau idan ki ka sake ganin ta zo, ki yi gaggawar zuwa ki sanar da ni, bana son ta zo ta bar gidan nan ba tare da na sani ba”.

“An gama ranki ya daɗe, in sha Allah zan sanar da ke”

“Saura wannan karon ma ki tsaya shashanci, tashi ki bani wuri ” jiki na rawa baba uwani ta tashi ta bar ɗakin.


Jamil ne zaune a turakar turaki, bayan sun gaisa, ya ɗan gyara zama ya ce “Allah ya taimake ka, wata magana nake son mu tattauna idan babu damuwa”
Turaki ya jinjina masa kai ya ce “Ina sauraronka”.

“Dama na ce game da riƙon ɗan wurin aisha, a hannun giwa yaron zai zauna kenan su cigaba da riƙonsa?”.

Turaki ya ce “Eh, wannan hukunci in da zai zauna mahaifinsa ne yakamata ya yanke, ya rasa matarsa bai kamata ɗan kuma a saka masa ido a kan sa ba”

“Amma, ba kwa tunanin yana da kyau a sanya ido, idan maganar aure ta taso ya auri wadda za ta riƙe yaron da amana ta kula da shi?”

“Adam ba ƙaramin yaro bane ba, na san zai samo mace mai mutunci da kirki, ba zai auri wadda za ta cutar da yaron ba”.

Jamil ya sake gyara zamansa ya ce “Amma ina ganin ku yakamata ku zaɓo wadda za ta maye gurbin aisha, kuma a ganina Samha ita yakamata ta maye gurbin aisha, a wannan karon yakamata a ba ta wannan damar”

Turaki ya ɗan yi shiru yana nazarin maganarsa, ya ɗago ya ce “Ka zo da magana kai ma, amma ka bari zan yi tunani a kai, kuma zan yi magana da shi in sha Allah, Allah Ya sanya hakan ya zama alkhairi”

“Amin ya rabb, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana”

Turaki ya jinjina masa kai tare da ɗan yin murmushi.

Duk wani ƙoƙari da dagewa, rumaisa tana yi wurin ganin ta kawar da tunanin sabir daga zuciyarta, amma abu ya ci tura, kullum sake jin ƙaunarsa take da tunanin sa a cikin zuciyarta.
Idan ta tuno da maganganun adam sai ta ji ina ma za ta iya zuciya, ace ko kallon sabir ba zata sake yi ba, balle ta ɗauke shi, amma ina sai ta ji ba zata iya ba, yanzu ma kawai daurewa take yi.
Gashi yanzu an ƙara mata tsaro, wataran mai sunan baba da kansa yake makaranta, islamiyya kuma tare da su huzaifa suke tafiya dan haka ba damar satar hanya. Haka za ta ɓoye ta yi kuka wasu lokutan dan tana kewar sabir sosai da sosai.

Yau asabar tana ta shirin tahafiz, mama ta ƙwala mata kira tana daga ɗaki.
Rumaisa ta shiga ɗakin, mama ta miƙa mata waya ta ce “Gashi Gwaggo ce za ta yi magana da ke”.

Rumaisa ta karɓi wayar ta kara a kunnenta ta yi shiru.

“Hello rumaisa”

“Na’am”.

“Ja’ira ki na ji na ba zaki yi magana ba”

Rumaisa ta ce “Ina kwana”

“Lafiya ƙalau, ya ki ke ya ƙarfin jiki?”

“Na ji sauƙi ai, har na koma makaranta ma”

“Ahh to Alhamdilillah, ya firgitar da ki ke yi fa cikin dare kin daina?”

“A’a ina yi wataran”

Gwaggo ta ce “Subhanallah, ki din ga addu’a sosai da sosai, dama zama a cikin wannan dajin ai dole ki yi gamo, wataƙila ma kin kwaso makarai. Zan saka a haɗo miki magunguna, a haɗo miki da kayanki a kawo miki”.

Da sauri rumaisa ta tari numfashin Gwaggo ta ce “A’a gwaggo, kar a kawo mini kayan nan yanzu, ki ɗaure mini su, ki ɓoye su sosai, kar ki bari wani abu ya same su, zan gaya miki lokacin da za’a kawo mini”

“To shikenan babu damuwa in sha Allah, zuwa sati mai zuwa zan aiko miki da magunguna”

“Ni fa lafiyata ƙalau, ba wasu aljanu da na kwaso”

“Idan ma kin kwaso ai ke ba zaki sani ba, kuma idan aka kawo magani ki ka ƙi yi, da kaina zan zo har kanon na zane miki jikinki”

Rumaisa ta yi shiru, gwaggo ta gama maganganunta, ta miƙawa mama wayarta ta ɗau jakarta ta fice zuwa makaranta.


Ringing ɗin da wayarsa take yi ne ya sanya shi farkawa daga baccin da yake yi, a hankali ya yi miƙa ya buɗe idonsa, ɗan guntun tsaki ya ja, dan ya ji haushin katse masa barcin da aka yi.
Ya miƙa hannu ya ɗau wayar, ya ɗaga ya saka a kunnensa.
“Assalamu alaikum warahmatullah, barka da safiya”

“Yauwa barka” ya amsa murya can ƙasa.

“Ya gida ya ƙoƙari”

Cikin ƙosawa ya amsa da “Alhamdilillah, waye?”.

“Khalifa Usman wakili ne, na kiraka ne domin yi maka ta’aziyya tare da jajanta maka abun da ya faru da kai”.

“To ka saɓa lamba, ba wanda yakamata ka kira ɗin ka kira ba”

Khalifa ya ce “Na sani, ba Mahmud Sharif Galadima ba ne?”

“Eh, Adam sharif galadima yakamata ka kira”

“Ba laifi bane idan kai ma an yi maka ta’aziyya ai, abun da ya shafi adam ya shafeka”

“Kai ka ga, abun da ya shafe shi shi ya shafa, ku je can ku yi abun ku, don’t ever involves me, ba na son fuska biyu, wataƙila da har zuciyarka da gaske ka ke ka kirani ka yi mini ta’aziyya sai in amsa maka, amma kowa ya san abun da yake tsakaninsa da mahaifinkaa da kai kanka, jiya mahaifinka yayi masa ta’aziyya a kafafen watsa labarai, kai kuma yau ka kirani wai kana yi mini ta’aziyya bana son munafuncinku na ƴan siyasa, kar ka sake kirana” ya yi tsaki ya kashe wayar ya ajiye.
Ya tashi zaune yana mamakin tsabar rashin kunya na wasu ƴan siyasar, ya san da biyu ya kira shi, ba dan Allah ba.

Ya miƙe ya shiga banɗaki domin ya yi wanka.

Ya gama abun da yake yi, ya fito ya shirya, ya fita falo domin karya, a falon ya tarar da Samha da Fauziyya ga ruky da Mummy sai hira suke yi, kuma da alama hirar ta su na da alaƙa da takawa.

“Wai ku ba ku da wata magana sai ta mutum ɗaya? Look for something else mana, kowa adam adam ku bar shi ya ji da abubuwan da suka dame shi”.

Gaban Mummy ne ya faɗi, yaushe Mahmud ya fara damuwa da lamarin adam?.

Fauziyya ta ce “Kawai muna ɗan yin hira ne a kan yadda abubuwa ke ta faruwa da shi, social media ma sai zancen ake yi”.

“Ni ma yanzu wannan yaron ya kirani, ɗan gidan wakili wai yana yi mini ta’aziyya, na ce kar ya sake kirana bana son munafunci da fuska biyu”.

Waro ido Samha ta yi ta ce “Khalifa wakili kuma?”.

“Shi fa, kar ma ya kuskura ya sakani a shirmensu ni buɗe masa aiki zan yi, rukky kawon breakfast zan karya”

‘Mai wakili yake nufi da kiran Mahmud a waya wai zai yi masa ta’aziyya?’ Samha ta tambayi kanta.

Tashi ta yi da sauri ta ce ta na zuwa, ta fice ta bar sashin zuwa harabar gidan, ta kira Khalifa a waya.

Sai da ta kira shi sau biyu sannan ya ɗaga.

“Wai me kake aikatawa ne da ka ke ɓoyewa?”

“Kamar me fa?” Ya tambaye ta cikin ko in kula.

“Kai ka ke sponsoring ake ɓatawa adam suna a gidajen jaridu ko?”

“Meye shaidarki na ni nake hakan?”

Cikin fushi Samha ta ce “Waye idan ba kai ba?”

“A tunaninki ni kaɗai ne maƙiyin adam? Ai ba mahaifina kaɗai yake da burin tozartawa ba, dan haka bani da lokacin sponsoring ɗin wasu gidajen jaridu su ɓata masa suna”.

“To me kake nufi da kiran ƙaninsa wai kana yi masa ta’aziyya, shi ma janyo shi zaka yi cikin tsiyar ta ka?”

“Wow, kuna tare kenan few hours da kiransa har kin samu labari”

“Ka ga, kashedi zan yi maka, kar ka kuskura ka sanya Mahmud cikin shirmenka, na san ba zai wuce an ce maka baya shiri da shi da adam ba, amma ka sani har abada jini ya fi ruwa kauri, adam jininsa ne kuma ko ba jininsa bane ba, Mahmud ba irin wanda zaka yi wasa da su ba ne ka cimma burinka”.

Khalifa ya yi dariya ya ce “Jini ya fi ruwa kauri, wane irin jini ne tsakanin ki adam da har ke ake wasan da ke? Ko daa yake wata kusan ta fi wata ai, and ba ke zaki gaya mini abun da yakamata na yi ba da wands ba zan yi ba, ina da abun yi yanzu, see you later” ya kashe wayar sa.

Ajiyar zuciya Samha ta yi ajiyar zuciya cike da takaicin biye wa Khalifa tun a farko.


Rumaisa ce zaune da wandon uniform ɗin islamiyya a jikinta, sai vest tana suyar wainar fulawa ita da Abdallah.
Ta ce “Yaya Abdallah ka san me nake sha’awa?”.

“A’a sai kin faɗa” yayi maganar yana zuba ƙullin wainar a kasko.

“Ina so in ji na ce basir ne da ni, ya tayar mini”

Tsaki ya ja ya ce “Mahaukaciya ba zaki yi hankali ba, kin san meye basir ciwo ne fa”.

“Eh, kawai dai burgeni yake yi, idan na ji an ce ina da basir”

“Sai ki yi ta yi ai, ba ki san masifar da ke cikin sa ba, ki je ki ji da yawon gudawarki da ki ka saba ba yau ba gobe, ya fiye miki alkhairi a kan ace basir ne da ke”

Tura baki ta yi, ta saka hannu ta gutsuri gefen wainar fulawa ta saka a baki, Abdallah ya ce “Kin ci a taki”

“Ƴar wannan ɗin?”

“Eh, uban wa ya ce ki ci ba a raba ba?”

Ta miƙa hannu ta ce”To bari na cinye guda ɗayan na ci a tawa” ya buge mata hannu ya ce “Baki isa ba uwar son zuciya”

Sallama suka ji, suka amsa gaba ɗaya, maman habiba ce, rumaisa ta gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska, tare da tambayarta ina mama.

Rumaisa ta ce “Mama tana cikin ɗaki ki shiga”

Bayan ta shige, Abdallah ya kalli rumaisa ya ce “Ina fatan ba wani laifin ki ka aikata ba?”

“Ni ba abun da na yi”.

“Wallahi idan ƙararki ta kawo sai kin daku?”
Shiru ta yi masa ta hau lasar yaji.

Maman su habiba ta ɗan daɗe, sannan ta fito, mama ta rakota sai dai fuskar mama babu walwala, ruma sai da ta ɗan tsorata ta yi zaton ko ƙarar ta ta maman su habiba ta kawo, amma bayan tafiyarta ta ji shiru mama ba ta yi mata faɗa ba.

Amma gaba ɗaya maman ta sauya, damuwa sosai ta bayyana a kan fuskarta.
Rumaisa ta ce “Mama ƙarata a ka kawo miki ne? Wallahi ban yi wa kowa komai ba”

Mama ta ce “A’a ba ƙararki aka kawo ba”

“To menene, na ga ba kya son yin magana”

“Bakomai”.
Gaba ɗaya suka lura da yadda mama ba ta walwala, duk wanda ya tambayeta menene sai ta ce bakomai, mai sunan baba kawai ta iya gayawa abun da yake damunta.

Washegari da safe, bayan tafiyar rumaisa makaranta, jikin mama ya tashi, sai da aka kai ta asibiti likita ya dubata, sannan suka dawo gida.

Kusan kwanaki biyu kenan mama babu lafiya, babu walwala har rumaisa ta fara koke-koke.

Cikin ƙarfin hali mama ta ce “Ba zaki yi mini Addu’a ba sai ki sakani a gaba kina kuka?”

“To ba kin ƙi gaya mini abun da ya same ki ba?”

Mama ta ce “Ai na ce miki bakomai, amma shikenan tun da ba zaki yi mini Addu’a ba”.

Rumaisa ta cigaba da kukanta, yayin da mama ta samu bacci. Wayar mama ce ta fara ringing rumaisa ta ɗaga sai ta ji muryar ammi.

Suka gaisa ammi ta ce “Rumaisa ina maman taki?”

“Bacci take ba ta da lafiya”

“Subhanallah, meya sameta?”

“Taƙi gaya mini” Rumaisa ta yi maganar tana fashewa da kuka.

“Ya salam, yi haƙuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta ji sauƙi, ki daina kuka kin ji ko?”

Rumaisa ta amsa da “To”.

Lokacin islamiyya ya yi aka gama girki, rumaisa ta ga abincin ba nama ba kifi, ba salak, ta ƙi ci, ta je ta shanye youghurt ɗin da aka sai wa mama ta kasa sha. Ta saka uniform ta tafi islamiyya.

Da yamma ta yi suka dawo daga islamiyya, mai wanke-wanke ya kama, mai ɗora girki ya ɗora.

Rumaisa na yin sallama ta tsaya a tsakar gida ta ce “Me nake ji haka kamar warin daddawa?”

Huzaifa ya ce “Mama ce ta ce tuwo take sha’awa, shi za ayi yau”.

“Taɓ mama ba ta da lafiya amma ta rasa mai za ta ci sai tuwo?”

Abdallah ya fito daga kitchen ya ce “Uban me ya hana ki cin abincin rana?”

“Abinci ba kifi ba nama, ba salak kawai tsuransa ni ba na ci”

“Iyeee ashe da gaske Huzaifa yake, ɗazu mai sunan baba ya tambayi abincin waye Huzaifa ya ce naki ne kin ce ba zaki ci ba ba kifi ba nama, ya ce zai gamu da ke idan ya dawo”

“Ku dai kullum burinku ku ga mai sunan baba yana tagayyara ni, ai shikenan”

Ta shiga ɗakin mama da sallama, “Mama ya jikin?”

“Da sauƙi, shi ne ki ka ƙi cin abinci ko ruma, ke idan baki samu abun da ki ke so ba ba zaki ci ba ko?”

Rumaisa ta girgiza kai ta fara cire kayanta.

Sallama aka yi mama ta amsa, rumaisa ta shiga uwar ɗakin mama da gudu, dan ta tuɓe daga ita sai phant za ta canza kaya.

Ammi ce ita da iman da Nusaiba, iman na rungume da Sabir.

A gurguje rumaisa ta canza kayan ta fito tana tsalle.

“Oyoyo yau ammi ta zo gidanmu”

Murmushi ammi ta yi tana faɗin “Ƴar gidan ammi, maman sabir”

Ta durƙusa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska.

Mama ta ce “Bisimillah ku zauna”

Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska.
Ruma ta ce “Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?”

“Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya”

Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna.
Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan.

Ammi ta ce “Ke maman sabir ya ki ka bar ƴan maza da aikin gida?”

Ruma ta ce “Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su. Ammi wannan wacece?” Ta yi maganar tana nuna iman.

“Ƙanwar takawa ce, ita ce ƴar autana”

“Tubarkallah mai kyau da ita” iman ta yi murmushi ta ce wa ruma “Ina wuni?”

Ruma ta zaro ido ta ce “Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo”. Dariya suka yi mata ammi ta ce “Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce” ruma ta yi dariya ta ce “Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni”.

Ammi ta ce “Yau ba zaki ɗau sabir ɗin ba?”

“Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake ɗaukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne”

Ammi ta ce “Subhanallah, me ya yi miki?”

“Ƙyaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi” ta ɗauke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma baƙa ƙirin ta cika masa kai. Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama.

Wata irin razana iman ta yi da ya shigo ɗakin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba.

Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya durƙusa ya riƙe mata kunne ya ce “Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?” Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce “Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili”. Ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya ɗau sabir a kan cinyarta ya yi waje.

Ammi ta din ga murmushi, gaba ɗaya rayuwar rumaisa burge ammi take yi.

Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba.

Ammi ta dubi mama ta ce “Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma”

Mama ta ce “A’a, jinina ne ya hau”

“A tunanina zuwa yanzu mun zama ɗaya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki ɓoye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu’a”

Mama ta nisa ta ce “Babar ƙawar rumaisa ce ta zo, take gaya mini maƙwabtana na ta yaɗa jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne kaɗai ya san yadda muka yi da ɗan”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, maƙwabta kuma?”

“Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun ɓata mini sunan ƴa, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki”.

Ammi ta ce “Wallahi ba sai kin faɗa ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi haƙuri basu isa su ɓata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama” shigowar rumaisa ɗakin ce ya sanya ammi sauya maganar.

Suka miƙe zasu tafi, rumaisa ta ce “Ammi, an ɗora mana abinci fa, ku tsaya a gama”

Ammi ta ce “Tuba muke, muna sauri ne, ayi haƙuri” rumaisa dai ba haka ta so ba.

Suka fito zasu tafi, mama ta ce ina ga mai sunan baba yana waje da sabir.

Suka fito aikuwa yana wajen, ammi ta ce “Iman karɓo sabir”

Jikinta har rawa yake yi, saboda gaba ɗaya mai sunan baba tsoro yake bata.

Kamar munafuka sai sunkuyar da kai take, ta miƙa hannu za ta karɓe shi, amma shiru bai bata shi ba.
Sai da ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, gabanta ya sake faɗuwa, har numfashinta ya tsaya na wucin gadi.

Ganin yadda ta tsorata ta rikice, sai da ya bawa mai sunan baba haushi, shi ba dodo ba meye na wani tsorata.

Ammi ta saka sidi ya buɗe booth, ya ɗebo cartons na lemo da kayan marmari, na dubiyar mama.

Ammi ba ta tsaya ba, dan ta san mama cewa za ta yi yayi yawa, suka shiga mota suna ɗaga musu hannu.

Tun da suka tafi ammi take saƙawa da warwarewa a zuciyarta, dole mama ta shiga damuwa, babu uwar da za ta ji daɗin a ɓata sunan ƴa a cikin unguwa dan wannan kawai sai ya hanata auruwa.

Suna tafe Nusaiba da iman na ta yi wa rumaisa dariya, yadda take gudanar da al’amuranta da yadda yayyenta ke kula da ita.

Tun a hanya ammi ta kira adam a waya, ta ce idan an yi sallar magariba tana son ganinsa.

Kamar yadda ta buƙata ya je ya sameta, ta idar da salla tana lazumi, bayan ta kammala ta dube shi ta ce “Mai ka yi wa rumaisa ne? Take cewa da tana da zuciya ba zata sake ɗaukar sabir ba?”

Ya kalli ammi ya ce “Wani abun ta ce na yi mata ne?”

“Ba ta ce ba, amma abun da ta faɗa ya tabattar mini da wani abun ka yi mata”

“Ba wani abu bane ammi, na mata gargaɗi a kan zuwa gidan nan ne? Idan aka fuskanci wacece, za’a iya ƙoƙarin citar da ita ko cutar da sabir ta hanyar ta”.

“Na ji, yanzu ba wannan ba ma, wata shawara na yanke a matsayina na uwa na kira ka na sanar da kai, ba dan kana da hakki a kan abun ba ma sai dai ka ji na zartar”.

“Wane hukunci kenan?”

“Ina son ka auri rumaisa!!!”

Kanwar Maza Book 3 Page 1

KU KARANTA:

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Hausa Novels

To Top