Hausa Novels

Rana Daya Book 4 Halima K/Mashi

rana daya book 4 halima k/mashi
Written by Aishat

Barka da isowa wannan shafin namu na littafan hausa novels inda muka kawo muku littafin rana daya book 4 halima k/mashi.

Rana Daya Book 4 Halima K/Mashi

Cikin zafin rai Shatima ya isa gurin da Salma da ke tsaye tana cika tana batsewa. Ya zabga mata mari, ya sake zabga mata a dayan gofen. Salma ta gigice, ta ce,In ba ka sona iyayena suna sona ba sai ka kashe ni ba. ka sake.

Ya sake kai wa bakinta kwabda, ta fadi Kasa bakin ya fashe jini ya soma tsiyaya. Shatima ya ce, “Kin dade ba ki tafi ba, kin ji ko? In ki ka sake magana sai na sumar da ke Ya fice bai bi ta kan kayan da ya zube a kofar daki ba, ya nufi dakin Aliya yana huci cikin tsananin bacin rai.

Aliya ta tare shi da sannu, amma ganin ya kasa amsawa sai ta fahimci yana cikin bacin rai, don haka sa ta aje ruwa a gabansa ita ma ta samu guri ta zauna.

Salma kuwa tana tashi ta shiga bandaki ta sa ruwan dumi ta wanke jinin da ke zuba.

Lebenta ya kumbura suntum, jini kuma bai tsaya ba, ta ce,Ai yau komai dare sai na tafi”

Ta dauki jaka da akwatinta daidai an tada sallar magriba ta san Baba maigadi yanzu ya tada sallah, ta yi ficewarta. Ba ta yi nisa a layin ba ta samu dan acaba ta tare ta nufi titi.

Ta dan jima kafin ta samu motar zuwa Zaria. Da ta sauka ta sake daukar dan acaba zuwa gidansu. Maman Nana makociyar Nafisa ta shigo gidan da sallama, Nafisa ta amsa tare da fadin,Har kin dawo?”Maman Nana ta ce,

“Ai kin san asibitinbabu layi, kana zuwa za ka ga likita, ina su Nana suna ta yi miki rashin ji ko?” Nafisa ta ce,Suna can falo suna kallon carton da su Ashraf”Ta ce,

“To bari tunda ba su ji zuwana ba in je in gama aikina”Nafisa ta ce,

“To ga makullin can”

Ta nuna mata shi a windon kicin, har ta juya sai kuma ta dawo tana cewa,

“‘Au! Maman Ashraf ina ta zuci-zuci in fada miki wata magana, amma ban san yanda za ki dauki abin ba Nafisa ta ce,

“Haba Maman Nana, inda zaki fada min ko mene ne kawai ki fada min”

Ta ce,Ban fada miki da wata manufa bá,

sai don ki yi saurin daukar mataki, amma cikin nutsuwa da hikima ba wai tashin hankali ba”

Nafisa ta zaro ido,Mene ne don Allah?

Ki fada min”. Maman Nana ta ce,

“A’a kar ki daga hankalinki, shekaran jiya waccan na dawo gidan Maman Sabir naga mijinki ya sauke wannan yarinyar Zinatu shine nike son ki fada masa ba yarinyar arziki ba ce.

Duk namijin da ta dafe masa sai ya yi kamar ya zauce don sonta. Ta yi aure sau biyar duk wanda ta aura sai ta sa ya rabu da iyalinsa sannan ta ki zama, sai ya sake ta. Yanda ki ka san annoba haka ta zama a layin nan”

Nafisa ta ce, “Na shiga uku, to ni Baban Ashraf in ya ce zai so ta ai mun bani, mu hudu ne fa, wa zai saki?”Maman Nana ta ce, “To nan bala’ in yake,ko mutum ba ya neman mata in har ya hadu da Zinatu zai fara. Tana da kyau kamar aljana, ga ta fara tas, ga diri ta iya gayu sosai. Sai dai fa akwai shiga malamai”

Nafisa jikinta har rawa yake, ta ce,

“Ya je Kaduna zan ma jira ya dawo kuwa? Ina jin a waya zan kira shi”‘.Maman Nana ta ce, “A’ a ki dai bari har ya dawo din sai ki nutsu ki yi masa magana cikin lumana” Nafisa ta ce,

“To shi kenan, na gode Maman Nana”

Rana daya book 4 Page 2

Nafisa ta samu guri ta zauna cikin damuwa, in Shatima neman mata zai fara lallai za a samu katuwar matsala. Ta tashi ta dauko waya da nufin kiranshi, amma sai ta tuna fa tana cikin damuwa da zakuwar ya dawo.

Badi’atu tana kwance a kan gadonta,zazza6i ne a jikinta rijib, mijin ya shigo ya dube tà,badi’atu wai har yanzu jikin?”Ta ce,

“Eh don Allah a kai ni asibiti Bari Maman Kausar ta gama ku je Badi’atu ta ce,

“Haka jiya ka ce za mu je tare da ita, ta ce ta yi baki sai haka na kwana da ciwo. To ni kawai in ba za ka kai ni ba, ka min kwatance Ya ce,Yau za ku je insha Allahu, jiya ma don tayi baki ne”Badi’atu ta koma ta kwanta,Ya ce,

“To ni zan fita, sai na dawo”

Don haushi ba ta tanka ba. Maman Kausar ita ce kishiyar Badi’atu, kuma ita ce za ta raka ta zuwa asibiti Badi’atu ta sauko da kyar ta yi wanka ta canza kaya, ta kwanta a kan kujera a falonta tana jira. Sai sha biyu da kwata mai aikinta Sahura ta shigo,

“Amarya wai ki fito in ji Maman Kausar Badi’atu ta tshi tana ganin jiri, a haka ta nufi gurin mota. Bayan motar ta samu a bude,nan ta shiga ta kwanta. Maman Kausar ta waiwayo, “A’ a tashi zaune, bana son langwai Badi’atu ta ce, “Gaskya jiri nike gani ba zan iya zama ba Ta ce,

“To ki sani ko mun je ba zan iya kama ki ba, gara ma kin karfafa jikinki”

Ta dubi mai aikin,Sahura shigo sai’In sauke ki bakin kasuwa ki sai min nama, ki wuce gidan Anty Baby zan biyo in dauke ki

Da yake asibiti ne mai zaman kansa suna zuwa suka ga likitan, anyi gwajin jini nan take dana fitsari. Ciki ne babu tantama, likitan ya bara shawarwari da kuma magungunan da ya rubuta.Suka fito a zaton Badi’ atu a bi a sai magani tunda ya ce ya ba ta kudin, sai ta ga tunda suka fito Maman Kausar ta hau yin sabgarta.

Sun je gidan Anty Baby sun shantake, ita ga zazzabi ga yunwa ba ta ci komai ba, don ba ta karya ba, gashi ba a sai mata magani ba, sannan suka wofintar da ita a falo tana jin irin zagin da suke yi mata, wai don tana da ciki ta lankwashe sai shagwaba take yi.Na ce, to da

‘ya ya gidan ba haihuwar fari ba ce bare a ce za a yi na marmari. Shima ya shigo da rawar kai tun jiya, wai a kai ta asibiti, nace bai dai wuce ciki ba, don haka ba kanta farau ba, na yi bala”in taka masa birki” Tana jin Anty Baby din tana fadin,

“Kin kyauta, gara dai ki rike ajinki, kuma ba a raina kishiya komai kankantarta, bugu da Kari kina da daurin gindi a gurin uwar mijinki”

Suka kuma sa dariya, maman Kausar din ta ce, Tabdi! To ba ita ba ko shi sai Hajiya ta Saba mishi a kaina bare wata ita Sun jima dai suna zantukansu kafun ta ji tace. “Ga cikon kudin kayan nan Ta kawo wasu,

“Wannan ma da cewa ya yi mu sai magani amma ba ‘zan siya ba, takardar zan kai mishi”

Badi’atu ta ce, “Lallai na shigo matsala”.Ta mike ta je kofar,

Tace Maman Kausar don Allah kizo mu tafi, yunwa nike ji kuma kin dai ji likita ya ce in sha magani Ta fito fuska a daure,

“Ki je ki tari abin hawa in kin matsu, ni sai sun gama girkinsu naCi Zan tafi Badi”atu ta mike ta dauki jakarta a tsakar gida ta tambayi Sahura mai aikin

Maman Kausar, sunan inda za ta ce a sauke ta. Ta fada mata don haka ta wuce abinta. Ba ta sha wahala ba ta je gida, tana shiga wayarta tana ringin ta ciro, mijin nasu ne ta yi zaton zai ji ya jikin ko sun dawo, ko dai wani abu makamancin haka,amma sai ta ji ya rufe ta da fada, wai kan me za ta taho don sun biya gidan yayarta? Badi’atu ta rasa me za ta ce; sai kawai ta saki kuka.

Ya ce,To mene ne na kuka daga magana?”

Badi’atu cikin kuka ta ce,Gaskiya ni ban san ya ku ke so da ni ba, Ta kai ni ta aje ga ciwo likita ya ce in ci abinci in sha magani, sai kuma mu je mu zauna kuma bayan ina jinsu suna ta yi da ni Ya Ce,

“To yanzun-kin ci abincin?”Ta Ce,

“Tea na sha kuma fa ba a sai maganin ba”.Yace,Ta fada min kudin sun kare, inna dawo zan sai maganin, don Allah ki ke  karfafa jikinki ciki ba ke ce farau ba”Cikin jin haushi tace,Ai ko a gurina sabon abu ne tunda ban.taba yinshi, ba?”

Ta kashe wayar ta kwanta tana ci gaba da kuka. Wani sashe na zuciyarta tana fadin, tun yanzu zan soma ganin sakamakon kin bin shawarar iyayena?

Na shiga uku ni Badi’atu!” Sai ko da ya dawo da yamma sannan ya amshi takardar maganin ya je ya siyo, lokacin tana kwance kan abin sallah tunda ta rarrafa ta yi sallar la ‘asar ba ta iya tashi ba. Ya ce, “Sannu, ya jiki?”

Ba tare da ta dago ba ta ce, Umhum”Ya ce, Bari in siyo miki maganin Ta dago kai,

‘Don Allah ka zo min da abin da zan ci, yunwa nike ji” Ya ce, “A’a ga abinci ba za ki girka ba?”Ta ce,Dubi mana yanda jikina ya yi laushi, ba zan iya aikin komai ba”Ya ce,

“To ni zan yi miki girkin kenan? Kin san dai ba zan sa Maman Kausar ba, tunda kowa da gurinsa badi’atu ta ce,Ni ban ce ka sa ta ko kamin girki ba, in ba zaka samo min ba ka barshi”Ta soma kuka,Ni kawai ma ka kai ni gidanmu”

Jin haka sai ya ce,To kiyi shiru, ina zuwa Ya fice da sauri. ya kawo mata sakwara da nama da kuma magani, ta ci ta koshi ta sha magani.

Also Read: Wata karuwa Hausa Novel By Oum Hairan

Rana daya book 4 page 3

Ya dauki take away din ya fita da shi kar maman Kausar ta gani. Badi’atu ranar ba ta yi bacci ba tana tunanin lallai ta fado cikin matsala. Ba dai har za ta soma karbar hukuncin kin yarda ba abin da iyayenta suka so ba, domin ita ta soma yin da ta sani tun yanzun,. Wa za ta tunkara da matsalarta?

 

Salma ta sauka a kofar gidansu ta ciro dari biyu ta ba dan acaba ya ba ta canji, jan akwatin tayi ta nufì cikin gida. Lokacin karfe tara sauran yan mintuna, Inna ta shiga bandaki ta ji karar jan akwatin. Da sauri ta fito don ta ji ko karar menene. daidai lokacin Salma ta saki akwatin a tsakar gidan ta nufì daki da son kuka.

 

Cikin sauri da faduwar gaba Inna ta aje buta ta bi Salma daki tana fadin,

 

“Lafiya! Bikin ne ki ka zo tun yau? Ta saki zancen ganin Salma tana kuka. Ta kunna makunnar wutar dakin haske ya gauraye dakin. Inna ta kalli fuskar Salma a razane ta ce, “Hatsarin mota ku ka yi?”Salma cikin kuka ta ce,Shatima ne ya doke ni” maganar yasa Jikin Inna ya dauki rawa,Duka kuma wane iri? Me ki ka yi masa haka?”

 

Salma ta ce,Wai kawai don nace sai ya sake ni, shine ya yi min duka” Inna ta fusata cikin bacin rai ta ce,Tashi ki koma dakinki ba ni da masaukinki. Tuntuni baki san ba ya sonki ba sai yau?”Salma ta ce,Inna..Ta katse ta,

 

“Tashi da Allah ki fice min a nan, in ma ba za ki koma dakinki ba, to ki nemi gidan wata uwar duk irin karamcin da wannan yaron yake mana ba don son naki yake mana ba? Shekaran jiyan nan ya turo wa Yayanku Auwal kudin sadaki na auran nan nashi.

 

Hayarmu kwanan nan ya biya da guntu-guntu saboda hidima da ta masa yawa, amma wai ki bude baki ki ce ya sake ki saboda gata da ya miki yawa? Ai dukan da ya miki ya yi kadan tunda ya bari ki ka iya fitowa da Kafarki, da karya ki ya yi sai ya fi burgeni

 

Haushi ya sa Inna ta kai ma Salma dundu Itare da fadin,Fice min

 

Salma ta tashi ta dauki jakar tana sabon kuka, har ta gota akwatinta Inna ta ce,

 

“Dawo ki dauki kayanki, wane shegen ne za ki bar maWa?”Salma ta jakar tana rusa kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa. Inna tana biye da ita tana fadin,Je ki duk inda za ki?’

Don ta ji Salma na fadin, “Ni ba zan koma can gidan ba” . Tana fita Inna ta sa sakata. Salma ta fi minti bakwai tana kuka a kofar gidansu, har sai da ta ji idanunta suna radadi,sannan ta fara tunanin zuwa gidan Yaya Hadiza.Ta tare mashin ya dauki kayan ta hau.

Har ya yi kwanar gidan yaya Hadiza sai kuma ta kalli layin su Hajiya Kaka, ta ce da mai mashin ya juya ya shiga layinsu Hajiya Kaka.

Har sun kulle gidan ta yi ta bugawa,

Salihu matashin da ke gidan dan dan uwan Hajiya kaka ne, tuni yake gidan zaune yana karatu. Shine ya fito ya bude kofar. Ganin salma ya cika da mamaki, yana fadin, “Anty lafiya na ganki haka?” Ta ce,’

“Salihu dauki mu je ciki. Kaka ta yi bacci ne?”Ya ce,Ba ta yi ba, don yanzun na kai mata manzafi da ta sa na siyo mata Ya dauki akwatin yana fadin, “Anty kunyi hadari ne?”Salma ta ce, Humm”

Maryama tana shafa ma kaka man zafi suka ji sallamar Salihu, tare suka amsa, ya shigo da akwatin hannunsa. Kafin su ce ta wane ne, Salma ta shigo. Duk da kallo suka bi ta, ta zauna a bakin gado. Hajiya Kaka ta ce,

“Kamar Salamatu nike gani fuska kumbure, ko dai idona ne Maryama ta ce, Ita ce, ko hatsari ku kayi?»Salma ta soma kuka tare da fadin,

“Ba hatsari. ba ne, Shatima ne yayi min haka”. “Shatima?” Kaka ta nanata cikin mamaki.

Salma ta ce,Dukana ya yi, kuma na je gida Innarmu ta koro ni”.Hajiya Kaka tace, “Maryama tashi ki debo mata ruwan dumi ta shiga bandaki ta dan gasa fuskar tata.

Salihu kai kuma zo ga dari biyu canjin da ka kawo min yanzun ka siyo mata maganin ciwon jiki”Ya ce, TO”.

Ya fita yana tambayar kansa dalilin da Shatima ya yi wanna danyen aikin.

Bayan ta dan dumama fuska, Maryama ta hado mata shayi ta sha, sannan ta sha magani.Kaka ta ce, “Kwanta, za mu yi magana da safe”Shatima ranshi ya baci karshe, ya shiga dakin Aliya ta ganshi tamkar an jeho shi. Ta dube shi,Yanzun ka shigo?”

Ya ce,Je ki kwaso min jakata a kofar yarinyar can Salma yake nufi ta sani, kuma tunda ta ganshi rai bace, to lallai wani abu ya afku.

Ta kwaso kayan idanunta na kan falon Salma wanda yake a hargitse. Ta dawo dakin ta ci gaba da ririta shi, aka kai ruwan wanka, aka hada abinci, har ta samu ya sauko amma har yanzu bai ce mata komai game da Salma ba.

Ga shi tana son jin abin da ya faru. Ya dauki Abulkhairi ya fita ya nufi grin Amna, ya je ya duba su sannan ya dawo.Ta ce,Na ga falon Salma a hargitse,lafiya dai ko?”Ya ce, “Kila tana kwalema ne”.

Sha dayan dare da mintuna Shatima harya yi shirin kwanciya duk iyaka kokarinshi na son share Salma ya kasa, domin ya ga jinin bakinta a hanninshi. Ya aje turaren da yake fesawa na bacci, ya nufi fita.

Aliya dake kwance a kan gado ta dago ta dube shi. Fita za ka yi baban Abulkhair?Ya ce,”Yanzun zan dawo”

Tana jin fitarshi ta taho sadaf! Sadaf!! Taleka ta windo, sashen Salma ya nufa. Kamar ta fita ta bi shi, amma tana tsoron kada ta fita shi kuma ya juyo. Dole ta daure ta ci gaba da tsayuwa a gurin. Yana shiga ba ta falon, ya shiga.

Wasu Na Karatun: Sakayya Hausa Novel By Garkuwa

1 Comment

Leave a Comment