Hausa Novels

Rana Daya Book 3 Chapter 1

rana daya book 3
Written by Aishat

Barka da isowa wannan shafin namu na littafan hausa novels inda muka kawo muku littafin rana daya book 3 chapter 1 by halima k/mashi.

Rana Daya Book 3 Chapter 1

ALhaji Isa ya shiga cikin Falon yana kiran, “Hajiya!” Badi”atu ta fito daga dakinta tana yiwa Alhajin sannu da zuwa ,sannan ta ce, “Yaya Mustapha ya kai ta Kaduna”.

Ya kalli agogon bangon falon tare da fadin, Nan da Kaduna shine har yanzu sai ka ce wadanda suka tafi Abuja?

Badi’atu ta ce, “Sai da suka yi sallar azahar sannan suka tafi” Ya ce, “Kai Hajiya tana da shiririta sosai. Ni da muka yi da ita za su tafi tun safe?”

Ya ja tsaki tare da fadin, “Yanzu dubi fa shida saura, kuma ta san ina azumi, Badi’atu ta ce, Ga shayinka can yanzu na gama dafawa, na sa a flask” Ya ce shayin ne kadai matsala ta kenan?

Tana sani na tsani in dawo ba ta gida. To wai su nawa suka yi tafiyar ne? Badi’atu ta ce, Su dama ya nufi dakinshi yana fadin, Bari in kira ta Daidai wannan lokacin Shatima yana tsakiyar falon cikin tsansnin damuwa, da tashin hankali. Minti daya tak din da Hajiya ta ba shi ne ya yi mugun tsorata shi.

Sam ba ta ba shi isasshen lokacin da zai yi tunani ba. Ya nufi kujera da nufin zama ko zai samu basirar shawo kan matsalar. Don rudewa sai ya kai zaman kafin ya isa kujerar. Hakan ya sa shi zubewa a kasa

Salatin da ya ji dakin ya dauka gaba daya ne yasa shi lunshe ido, tare da fatan Allah ya sa mafita ce wannan Ya saki jikinshi tamkar wanda hankalinsa ba ya tare da shi Nan duk suka yi kansa suna kiran sunansa. Hajiya tana fadin, “Na shiga ukuna! Shatima don allah ka tashi! Ku debo min ruwa

Mama ta ce, “Tsaya mu gani ko dai juwa ce ba suma ba ne? Aliya da su Amna sai nanata sannu suke yi.

Hajiya ta dibi ruwa ta wanke mishi fuksa tare da fadin, Sannu Shatima, ka tashi don Allah duk yana jinsu, ko babu komai sanyin ruwan ya rage masa zufar da take tsiyaya a jikinsa. Sannan ya sauke wata irin ajiyar zuciya.

Mustapha cikin bacin rai ya ce, “Ban ga dalilin yin wannan zantukan ba tunda ba su ne suka kawo mu ba”

Shatima kuwa addu’a yake a cikin zuciyarsa,yana kiran sunayen Allah tsarkaka. Fatanshi Allah ya

fidda shi cikin wanna fitina. Miyan bakinshi ya tsaya cak! Lokacin da ya ji muryar Hajiya tana maimaita ya wartsake a yi ta ta kare, don ba zan bar wannan damarba.

Mama tace, “Haba Hajiya! Don Allah ki bar wannan maganar, a bi komai sannu Alhaji ya yi ta duba wayarshi a daki, sai ya tuna tana mota inda ya jona ta a caji. Ya cire kayanshi ya maida jallabiya mai gajeran hannu, sannan ya fita.

Missed calls ashirin na Mustapha ya gani, Tsoro ya kama shi, tare da fargaba suka darsu a zuciyarshi. Tuni ya raya cewa sun yi hatsari ne. Cikin rawar hannu ya bi kiran.

Da sauri ya daya, Alhaji don Allah ka kira Hajiya yanzun tazo tana ta fada da abubuwa a gidan ga shi nan har Ya Shatima ya fadi!

“Faduwa?” Alhaji ya tambaya da karfi. Mustapha ya ce, Faduwa kuwa, yanzun haka ba ya cikin hankalinshi Alhaji ya ce, “Ai babu batun kira, bari kawai inkira Babanku Musa muzo gidan

Mota ya fada a hakanshi, sannan ya kira layin dan uwansa Alhaji Musa. Lokacin da Alhaji Musa ya daga wayar Alhaji ya kusa fitowa daga layinsu. Alhaji Musa ya ce, ga shi a Jaji sun z0 duba jikin Alhaji Yakuba abokinsu, wanda ya hadu da ciwon mutuwar Barin jiki.

Alhaji ya ce, “Gani a hanya, jira ni a titi zan dauke ka mu wuce” Alhaji Musa ya ce, “Ina zamu  Wuce!?”

Alhaji ya ce, Kaduna gidan Shatima, Hajiya Amina da suka je dubiyar jikin Nafisa ta tada musu wata fitinar. Ga shi can an ce jikin Shatima ya tashi har ya fadi yana da rai ko ya mutu ma? Ni ban sani ba”

Gudu sosai Alhaji ke yi, cikin mintuna ya iso Jaji, ya dauki Alhaji Musa ya kuma daukar hanya Cikin lokaci kalilan Shatima yana jingine da kujera kanshi yana cinyar Aliya wadda wadda idanu suka yima jajir don kuka.

KARANTA: 

Rana Daya Book 3 Chapter 2

Rana Daya Book 4 Halima K/Mashi

Leave a Comment