Hausa Novels

Yadda Naci Yayata

yadda naci yayata
Written by Aishat

Yadda Naci Yayata

yadda naci yayata: Raheela tacigaba da zance zuci gani haka ba Zai fishe ta ba yasa ta share hawaye ta, bacci yayi awo gaba da ita.

Da gudu na’eema tashiga falon tafada jikin umma hajara tafashe da kuka umma tace oh ni hajara ina zan saka kaina da wannan masifa da takunno kai a gida na to kuma yanzu me faru ki ka shigo min falon da gudu kina kuka”?

Na’eema takara fashewa da wani sabon kuka tare da cewa ki dubi girma’n Allah umma ki ceto rayuwata daga afkawa halaka umma ni kadai ki ka haifa in na mutu bakida wasu ‘ya’ya da za ki kalla a matsayin ke, ki ka haifa ki taimake ni umma kar narasa yaa amar wallahi umma ina sonshi ina yi masa mahaukaci SO da zuciyarta, bata iya jure ganisa da raheela umma in har narasa yaa Amar nima za ki rasa ni domin zan sha ”poison” na kashe kaina a firgice umma hajara tadago na’eema, ta wanka mata mari tace kan’ki daya na’eema da zaki kashe kan’ki akan wani banza” to ki kwatarda hankalinki domin ni uwa ce mai son farin ciki ‘yarta koda ace zan dawo yawo tsirara a gari sai na kwanto miki soyayya’r amar kuma nayi alqawali sai na tarwatsa rayuwar raheela tun tayi sanadi zubar hawaye ki yadda ki kayi kuka akan Amar ita ma sai tayi kuka akansa so nake ciwo zuciya yazamo shine, ajali’nta don haka maza share hawaye ki ciki’n tsanani jin dadi na’eema ta share hawaye tace umma yanzu ya za’ayi saboda banaso na bude idanu na nagansu tare”?

Umma hajara tayi dariya mugunta tace sha kurumin’ki na’eematu boka duguzuu shine mai magani ‘ya’ya iska na’eema tayi murmushi tace da kyau umma so nakeyi raheela tagano cewa tayi babba kuskure naso abunda nakeso tagano cewa ba’a tabani a kwana lafiya Umma tace to ki bude kunne ki da kyau ki saurare huduba da zanyi miki na’eema ta gyara zama tace na bude umma wani kafiri murmushi umma tayi daga bisani tace daga yau karki kuskura ki kara shiga “side” din fateema ki kuma tataro duk wani abu da ya kasance mallaki ne ki baro bangare kaaka kidawo nan da zama inaso ki daura gaba da mutane gidanan domin ba kauna sukeyi ba kuma banaso ki kara kowace irin hulda da raheela tsakani ki da ita kiyayya ce mai zafi, na’eema tace angama umma hudubar ki ta zauna a kwakwalwa ta saboda yanzu babu saura kaunar raheela a zuciyata asalima jin nakeyi kamar na daba mata wuka a kaho zuciya umma hajara tayi murmushi jin dadi tace tashi maza ki je ki tataro kayanki na’eema ta yatsine fuska tace tun yanzu umma? Eh mana ae ba’a bori da sanyi jiki na’eema ta mike tanufi “side”din kaka….

Kaitsaye na’eema tashiga falon kaka, gani babu kowa a ciki yasa ta wuce “bedroom” din kaka taya tayi tsaye sakamako, hango raheela kwance tana bacci taja tsoki mtsss…a baiyane tafara magana banza munafuka maciyiya amana raheela da ke ta shara baccin ta bata masan tana yi ba na’eema jin takeyi kamar tashake raheela ta mutu kowa ya huta,cikin zafin rai ta bude “wardrobe” da karfi tasoma kwaso abinda yake mallaki ta, ta jingewa kasa, yanayi ta tamkar na mai tabin hankali karar budewar “wardrobe” ne yayi sanadiyar falkawa raheela, cikin tsananin mamaki ta ke kallon na’eema, da ta iya bude bakin’ta dalilin nauyi da yayi mata ga kuma wani masifafe ciwo kai da ke barazana, tsaga mata kai tace lafiya yaya na’eema ki ke kwashe kayanki”?

Gyaran Nono Da Tumfafiya

Banza tayi da ita tamkar bataji tambaya da tayi mata ba tadauko katuwar “trolley” dinta tasoma dibar kayan da ta jinge kasa tana zubawa ciki’n “trolley” da sauri raheela tasauko bisa gado ta riko hannu na’eema fuskar’ta dauke da tsantsan damuwa, tace dan Allah yaya na’eema kiyi min magana me ke faruwa ne”?

Ciki’n bacin rai na’eema ta buge mata hannu tadaka mata tsawa cikin tsabar masifa da bala’e tace dallah ki saurara min haka nan ko kina tsanmani banida masaniya dangane da zago kasa’n da ki ke yi min”?

Cikin rashin fahimta inda zance’ta yadosa raheela tace ni fa yaya na’eema kina kara jefani ciki’n rudani saboda ban fahimce manufar wannan zance naki mai kama da halshen damo ba, na’eema taja tsoki kamar za ta gutsiri halshen’ta hade da cewa kada Allah yasa ki fahimta abu daya nakeso kisani raheela banza irinki bata esa tarabani da Yaa Amar domin abin abaiyane yake duk fadin matawalle family ba wanda baida masaniya ni yaa Amar yakeso ba ke inda ma wani kulle-kulle ku ka kulla ke da munafukar uwar’ki to ta Allah bataku ba, domin ni da yaa Amar mutu karaba ne takalmin kaza nan gani nan bari dukiyar uban wani tana karasa zanceta taja “trolley” din’ta da karfi tafice daga daki’n yayida tabar raheela tsaye ciki’n wani hali, hawaye na zuba akan fuskar’ta, ta durkushe a tsakiyar daki takara fashewa da sabon kuka kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, tasoma sabbatu, buri ka yacika yaa Amar shikenan karabani da ‘YAR UWA TAA” ka hadasa gaba a tsakani mu me nayi maka yaa Amar da ka zabi wannan hanyar don ka musgunawa rayuwata”?

Jin andafa kafada ta yasa tajuya gani kaka tayi tsaye fuskar’ta dauke da damuwa da sauri ta mike tsaye tafada jikin kaka tasaki kuka mai tsuma zuciya mai karatu, ciki’n sigar rarrashi kaka take bubuga bayan’ta da kyar kaka ta rarrashe ta tadaina kuka, kaka ta zaunar’da ita a gefe gado tasoma tambaya’r ta dalilin kuka’nta raheela ta kwashe iya abunda tasani tafadawa kaka kowane su yayi shiru sai kace masu nazari daga bisani kaka tayi murmushin takaici, hade da cewa babu zance yaudara a ciki’n zance da amar yafada miki da gaske ne yana sonki raheela saidai ni kaina ina mamaki wannan halaya ta Amar iya abunda nasani kowane dan-Adam yana kokari yaga ya kyautatawa abinda yakeso sabani amar da yake munanawa abinda yakeso yana farantawa abinda bayaso rai tabbas raheela” amar yana son’ki so da shi kan’shi ba zai iya misalta shi, ba a tsorace raheela tace haba kaka miyasa wannan karo ki keso ki goyi bayan yaa amar”? duk fadin gidanan ba wanda baisan yaa amar ya tsaneni baya sona wannan al’amari a baiyane yake kaka.

Kaka tace ba tsanarki yakeyi ba raheela son’ki ya ke yi wallahi amar yana tsanani son’ki soyayya’r da amar yake miki tasamo asalin tun daga ranar da ki kazo duniya ni shadace akan haka, ki yarda da ni raheela kinsan bantaba fada miki karya ba kuma kinsan ina adawa da duk wani abu da yayi yunkuri shiga tsakani ki da farin ciki ki, amma azahari gaske inaso ki da amar domin amar yar.o ne nagari kuma kowace uwa tanaso ‘yarta ta aure miji nagari shiyasa nake miki sha’awa kasancewa da amar.

Raheela ta turo baki tace wallahi kaka banaso shi na tsaneni shi don haka kifada masa ya kyale ni yaje ya rungume me sonshi, kaka tayi zugun tana kallon raheela daga bisani tace dama abinda nake yiwa amar gudun kenan tsuntsu da yaja ruwa shi ruwa kan doka wannan shiri sa ne shi, kuma yasan yadda zai gyara kayansa.

Raheela ta tabe baki hade da miqewa tsaye tace dan Allah kaka kije kidawo da na’eema ki kuma fada mata cewa ni banaso yaa amar shi kadai ne yake shirme sa. Kaka ta galla mata harara tare da cewa ae bani nakori ta ba da zanje nadawo da ita, raheela tayi kasa da murya tace dan Allah za kije ba don halina ba kaka taja tsoki mtsss….ta mike tafita tabar ma raheela daki…

Raheela ta mara mata baya sai faman yi mata magiya takeyi ciki’n fushi kaka tace wai ke wace irin maya yarinya ce”?

Wannan rashin zuciya naki yayi yawa, to ba inda zan je don ni ba shashasha bace irin’ki in har ke damu da rashin ta sai ki tatara komaitsa ki, ki koma bangare su da zama. Raheela ta bata fuska tace Shikenan kaka ki sha zaman ki yaa amar dai ne nace banaso shi duk mai daukar zafi da ni yayitayi ni ko a jikina, tana karasa zanceta batare da tajira jin ta bakin kaka ba taficewar’ta.

“side” din mamee tanufa a falo tarar’da mamee zaune tana kallon tashar sunnah tv raheela tayi sallama mamee ta amsa mata “direct” ta zauna kusa da mamee ta dan kwato da jikinta a jikin mamee tace wash….Allah na nagaji mamee ta tabe baki tace, da ki kayi aiki me”? Raheela ta Yatsine fuska tace aiyuka da yawa mamee ta ture tace ke dagani banaso shiririta duk wanda aure ki yana da aiki, ciki’n shagwaba raheela tace nifa mamee danki zan aura.

Mamee tayi dariya hade da cewa dadi na da ke raheela rashin kunya mu ae ba mahaukata bane da za mu hada ki aure nazeer, raheela ta tunzire baki tace wai saboda me”? Mamee tace saboda daga ke har shin din bakuda ta natsu raheela ta tintsire da dariya tace kai mamee yanzu kallon motsatsu ki keyi mana”? Mamee tace kwarai kuwa” raheela takara tintsirewa da dariya har tana fadawa jikin mamee, sallama amar ce takatsiwa raheela dariya da takeyi ta wani bata fuska shima batare da ya kalle ta ba ya kai zaune, mamee tace kawo maka abinci ne”? Amar ya shafi sumar kan’shi wanda ya zame mishi dabi’a daga bisani yace banaji yunwa a koshe nake.

Raheela ta mike tsaye tace mamee na tafi sai anjima, zan dawo nayi miki gyara “wardrobe” mamee taja tsoki tace nasan halin ki raheela ni da kara ganinki sai kuma gobe ko don kin fahimci nafiso naki da na na’eema, ne shiyasa ki ke mini yawo da hankali raheela tayi dariya tace Allah mamee zan dawo mamee tace adawo lafiya raheela tafice daga falon, amar da ke lumshe da idanu kamar mai bacci ya bude idanu shi, shima ya mike tsaye hade da cewa mamee inaso kiyi min dambu nama in tafi da shi, mamee ta tabe baki tace yakamata kayiwa kan’ka fada ka ajiye iyali haka nan amar dan murmusa batare da yace da mamee komai ba yafice, raheela na fita daga falon mamee tanufi “garden” ta nemi kasan “grass carpet” ta zauna har cikin zuciya’ta tanaso taje tabawa na’eema hankuri ta kuma fada mata ita bataso’n yaa amar saidai tanaji tsoro masifar umma hajara domin kuwa tono silili Za tayi mata wanda janyo kowa yagama Jin amar yace yana sonta kuma hakan zai iya kara haifar da gagarumar matsala mtss….taja tsoki yaa amar yacuce ni, ya jefani cikin damuwa ina zaman, zama na ciki’n kwanciyar hankali ni da ‘YAR UWA TAA gashi ya haddasa mana gaba ko me zai faru in na’eema tafadawa umma hajara ni yaa amar yakeso ba ita ba.

Gaskiya yaa amar mugu ne duk wa shekaru nan yasan ni yakeso miyasa yake nuna min zallah kiyayya yake kuma nunawa na’eema tsantsan so”? Tun lokacin da raheela tafada kogin tunani amar yake tsaye a bayan’ta gani ta tsunduma da yawa yasa ya karyo ganye bishiya mangwaro ya aza mata bisa wuya, a firgice ta mike tsaye tana kurma ihu Amar ya kyakyace da dariya daga bisani ya tsagaita da dariya da yakeyi yace ya akayi ne “baby naa” wannan ihu duk na menene”? Kallon tsana raheela tafara aika masa daga bisani ta ja wani wawa tsoki tajuya da suna tafita daga “garden” din ciki’n zafin nama yariko hannuta…

KARANTA: Wayyo Gindina Hausa Novel

Leave a Comment