Gyaran Jiki

Maganin Dadewa Ana Jima’i

Maganin Dadewa Ana Jima'i
Written by Aishat

Maganin Dadewa Ana Jima’i

Maganin Dadewa Ana Jima’i: Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matukar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kadai bace take samar da morewar zaman aure, saduwa itace akan gaba.

Wannan yana nufin cewa koda mace tana da ladabi da biyayya, iya magana, iya girki, iya kwarkwasa, iya kwalliya, tsabta da sauran abubuwan kayatarwa na zaman aure, to, dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta.

Haka nan kuma koda namiji yana da kokarin samar ma matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan kayatarwa na zaman aure, to, dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa.

Bisa wannan dalilin ne maza suke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.

Abinda Ake Nufi Da Gamsar Da Juna Wajen Saduwar Aure

Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin musulunci (Islamic clerics), da na halayyar dan-adam (psychologists) sunkai sun komo game da ma’anar gamsarda juna a wurin saduwar aure.

Amma duk bayanansu sun tattara ne akan cewa ma’anarsa itace a samu natsuwar da zata gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan bukatar hakan ta taso.

Da wannan ne wasu da yawa daga cikin mazajenmu suke daukar cewa mutum ba zai iya gamsar da iyalinsa ba sai:

1. Idan yana da al’aura mai kauri, ko tsawo, ko kuma duka biyun.

2. Idan yana dadewa wajen saduwa

Hakan ne ya baiwa wasu kamfannoi masu sarrafa magungunan bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samarda magunguna iri-iri wadanda aka ce suna baiwa namiji karfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata.

Abin yayi yawa sosai, ta yadda masu wadannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.

RABE-RABEN Maganin Dadewa Ana Jima’i Na Chemist Dana Gargajiya

Magungunan sun kasu kamar haka:

1. Kwayoyi (drugs): wadannan sune magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun hada da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu.

2. Mayuka (creams): wadannan sune magungunan da ake shafawa. Suma suna da yawa, kamar Maxman Delay cex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.

3. Allura (injection): wadannan sune magungunan da ake yin allura dasu. Suma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.

4. Tiyata (surgery): wannan shine aikin yanka mazakuta da ake yi a dakin tiyata domin a kara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). Anfi yinta a kasashen turawa, kuma tana da tsada sosai.

5. Jike-jiken magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi yafi yawa a cikin al’umarmu. Suma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilimin kimiyya basu cika yarda da tsabtar wadannan magungunan ba, haka kuma basu yarda da sahihancin ka’idar amfani da su ba (dosage).

Tasirin Maganin Dadewa Ana Jima’i

Masu amfani da wadannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan baya rasa nasaba da abubuwan da ake hada su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, fenugreek, maca da sauransu.

Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya karuwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa dadewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum.

Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in baiyi amfani dasu ba. Assha! Kaga kenan matsala ta auku.

Sirrin Gamsar Da Mace Wajen Saduwar Aure

Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar damu yadda za’a gamsar da mata wurin saduwa:

نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ

“matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda kuke bukata, kuma kuyi wasanni dasu (a lokacinda zaku sadu dasu)”, Baqarah: 223.

Kenan idan mutum yayi wasaanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita.

Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa dadewa ana saduwa shine kwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya bane, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17.

Idan ta kai minti 20, to, tayi yawa domin zata iya sanya ni’imar matar ta dauke, daga nan sai ta fara jin zafi, kila ma ayi mata rauni.

Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na fada bane, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba.

MENENE ABUN YI?

1. Matsalar kankancewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to, ya kamata ya tuntubi likita domin a dora shi akan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, wadanda idan illarsu ta taso bai san yadda zai magance ta ba.

2. Idan ba ya zama dole ba, kada ka saba ma madam da dadewa ana saduwa, domin idan ka daina dadewa daga baya, to, akwai matsala fa.

3. Ka karfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda qur’ani yayi umurni.

KARANTA: Maganin Qarin Hips (Mazaunai )

1 Comment

Leave a Comment