Hausa Novels

Sanadin Makwabtaka Page 1

sanadin makwabtaka page 1
Written by Aishat

Barkanku da zuwa shafin karatun littafan hausa novels inda zaku karanta littafin sanadin makwabtaka page 1 by Oummu Imam.

Sanadin Makwabtaka Page 1

Unguwa ce mai dauke da Manya manya had’i da K’ananun Gidaje,sai dai kana kallon yanayin gidajen zaka fahimci cewa ba tsohuwar unguwa bace,don sam gidajen basu ji jiki ba,wasu gidajen Sababbi ne yayin da wasu kuma baza’a kira su da sabbi ba,ba kuma tsofaffi bane,akwae Manyan gidaje masu kyau wad’anda da ka kalla zaka fahimci masu gidajen nada arziki,yayin da wad’ansu kuma ke nuni da masu su,masu rufin asiri ne.Yanayin layin ba hayaniya sosai akwae mutane jefi-jefi,kallo daya zakae ma layin ka fahimci akwae masu arziki had’i da masu rufin asiri a wurin.

Wata mota ce k’irar Corolla S Navy blue ta shigo layin da matsakaicin gudu, K’irrrrrrr! Motar taci burki batare da shiri ba sakamakon wasu yara mata da basu wuce shekara 13 zuwa 14 ba, da suka shigo hanyar da gudu daga Lungun dake a bangaren dama,d’aya cikinsu na dauke da farin matsakaicin Bokiti mai d’auke da wani abu ciki hakan na nuni da tallah take yayin da dayar da ta biyo ta ita bata dauke da komae,lungun da ke opposite da wanda suka fito suka shiga a daidai nan kuma d’ayar yarinyar ta samu nasarar kamo hijab din yarinyar dake dauke da bokitin talla,tura ta tayi jikin bango tana kokarin 6arar mata da abunda take sayarwa, ita kuma ta rik’e bokitin gam.

Shi kuwa na cikin Motar still yayi da alamun bacin rai a fuskarsa yadda yaran suka fad’o masa all of a sudden,ba don Allah yasa bai gudu sosai ba da horrible accident ya faru a wurin don gaba dayan su zai dauke su da motar watakil ma ya take su,dan tsaki yaja”Mtsww”A hankali ya waiwaya yana kallon lungun da yaran suka shiga,hango su yayi sai faman kici kici suke alamar dai fad’a suke ga d’ayar yarinyar mai sanye da riga da skirt na atampa kanta d’aure da kallabi wanda daga bayan kallabin yayi tudu sosai alamun dai tana da gashi mai yawa ga gyalenta kuma daure a k’ugunta sai faman kokarin ganin ta 6aro da bokitin dake kan dayar yarinyar da ta matse a bango take.

Ganin yadda ta dage bilhakki sai ta 6arar ma d’ayar abunda ke cikin bokitin yasa shi sauke gilashin motar a hankali,”ke,ke” Ya fara k’okarin yima yarinyar magana sai dae ko waiwayo inda yake batayi ba,tunani yayi kilan bata ji shi ba hakan yasa ya k’ara dan daga murya duk da bai so hakan b “Kee sake ta!” ya kara fada,tana jinsa tayi burus da shi,yarinyar mai talla ce tace”ke Fatuu baki ji wancan mai motar na cewa ki kyale ni bane”kara k’ankame bokitin tayi ita kuwa wadda aka kira da Fatun ganin ta kasa 6aro da bokitin yasa ta fara dukan yarinyar don tasan in tayi hakan dole ta saki bokitin ai.

Ganin hakan yasa mutumin cikin motar fitowa,Wow! Masha Allah, Wani Kyakkyawan Mutum ne mai dan tsayi sai dae ba irin tsawon nn sosae b, sai dai kana kallonsa zaka shaida dogo ne,kalar fatar sa kuwa fara ce irin farin nan mai kyau mai tafia bai d’aya ba wai irin wanda zaka ga wani wuri yayi dan ja-ja ko yalo-yalo ba,gaba daya fatar shi sumul take,yana da matukar kyawun Fuska wadda da idanu sun kalli fuskar zasu shaida hakan,sumar kansa nada dan tsawo wadda take a nad’e yayin da daga tsakiya ta dan fi gefe da gefen tudu,sam bai tara kasumba ba sai dai akwae sumar kad’an zagaye da fuskar har zuwa saman dan madaidaicin bakinsa wanda labban sa suke kalar peach mai duhu,sanye yake cikin Suit Navy Blue yayin da yar cikin take Black color,Wuyansa na sanye da Necktie kalar suit din wato navy blue wanda yake kwance ak’asan bakar collar din yar cikin,k’asan necktie din kuma an rufe shi data saman ta hanyar sa Ma6allan rigar wad’anda suke bakake masu kyan gaske,hannunsa na sanye da Wrist watch silver mai d’an duhu kai da gani kasan zai yi kudi Agogon, yayin da K’afafunsa kuwa ke sanye cikin wasu dakakkun Takalma cover shoe bak’ak’e, ba k’aramin haduwa yayi ba,ba kamar da kalar fatar sa take fara sai yayi kaman ba irin mutanenmu ba na nan,yadda suit din suka amshi jikinsa cib ya bayyana sam ba ramamme bane yana da cikar kira ba kaman Kafadunsa da suke da fadi,da ka kalli kayan jikinsa da kuma motarsa zaka fahimci yayi shigan da ake kira too match,

Ya mayar da Kofar motar ya rufe da hannunsa daya tafiya ya fara yi majestically,da ganin yadda yake tafiyar za kai tunanin irin mutanen nan ne masu ji da isa,gefen su ya tsaya fuskar nan a tamke cikin dan daga murya ya fara yima yarinyar magana”Sake ta!”burus tayi sai ma k’eya da ta kara juyo masa,cikin 6acin rai da daga murya yace”Am i not talking to u, idiot.” ya fada a dan harzuke,jin yace mata idiot yasata juyowa a fusace ta fara magana cikin masifa”Ni ba idio……sam ta kasa k’arasa maganar sakamakon hada ido da mutumin dake a tsaye fuska a d’aure,kwarjini yayi mata sosai,

“Get your hands off her”ya fada fuska a daure,a hankali ta saki Yarinyar mai talla da alama ta ji abunda ya fada da turanci,d’an ja da baya tayi kad’an,kasa-kasa tace “Don kana da kyau zaka wani daure ma mutane fuska ni ba ruwana da kyaun ka ehe” Still yayi yana kallon yarinyar don yaji duk abunda tace,lallai yarinyar bata da kunya ya ayyana a ransa,”Wuce kibar wurin nan before I slap ur face”ya fada tare da nuna mata hanya da hannu,A hankali ta fara tafia cikin lungun tana turo baki tana waiwayen su,kallon yarinyar da ke dauke da bokitin talla yayi”Wuce ki tafi” ya fada yana nuna mata hanyar da suka fito “To”,ta fada tana gyara Yellow din hijabinta da ta cukwikwiye ta fara tafiya,shima juyawa yayi ya nufi inda motarsa take,

“Wayyo Allahna! ta 6arar man da Awara…!” Yarinyar ta fasa kuka tana fadi da sauri mutumin ya juyo,da wani irin expression yake kallon yarinyar da ta 6arar da awarar,Ashe ba tafiya tayi ba tana ganin ya nufi motarsa ta fito da sauri tasa hannu ta ture bokitin Awarar,ganin yadda yake mata wani irin kallo yasata jin tsoron shi rugawa tayi a guje cikin lungun ita kuwa mai awarar muryar ta kawai ake ji sai faman ihu take tana fadin”Wllh bazan yarda ba sai an biyani gidanku zan biyo ki,Muguwa,Azzaluma kawae”d’aukko bokitin tayi wanda ya rigada ya fashe ganin haka yasa ta sakin wani sabon kukan.

A hankali ya juya ya koma inda take tsugunne tana d’ibar awarar tana zubawa cikin bokitin sai faman kuka take,tsayawa yayi a kanta,d’ago kanta tayi cikin kuka tace”kagani sai da ta 6arar mn da awarar ko,kuma wllh bashin waken soyan da mai Innarmu ta amso sai na sayar za’a kai kudin gashi ma har bokitin ya fashe wllh gidansu zani sai an biya ni” ta k’arasa maganar da matsanancin kuka.

“Is okey,just leave the rest” Ya fada,dagowa tayi tana kallon shi da alama bata fahimci mi yace ba,”tashi kibar sauran, baki ga yayi k’asa b” Ya fad’a gently, mik’ewa tayi tana ta sheshsheka cigaba da magana yayi a hankali”Miya hada ki da ita? “Wllh ba abunda nayi mata kanwata ta tare rannan wai sai ta bata alakoro ita kuma tace bazata bata b,shine ta buge ta,kuma ta d’ebi awarar,da Innarmu taji shine taje gidansu da kanta don ayi mana tsakani don ba lokacinne na farko ba da take taremu tace mu batan,to shine aka bugeta yau tana ganina tace tunda Innarmu tasa aka bugeta sai taja mata asara sai dai in tasa a kasheta,ba yad……..”its okey”ya katse ta, da alama ya gaji da sauraronta,”Ina ne gidan ku? ya tambayeta a takaice,”Acan layin baya muke gidan Alhaji Sani karofi anan babanmu yake gadi cikin gidan muke acan baya”takae maganar tana goge kwallan idonta.

“Shi abun naki na nawa ne? ya tambaya.”Awarar dubu da dari biyar ce gashi ta zubar da ita duka yar kadan ce bata baci da k’asa ba,inaga ma ko ta d’ari biyu bata wuce ba,wllh gidansu zanje sai anbiya mu ta k’ara fashewa da kuka,da alama taji zafin abun sosai, Sigh yayi kafin yace”You know what,ku kyaleta kawae tunda bata jin mgn in kun k’ara zuwa kun kai karanta zata k’ara zubar maki da abu,calmly yayi maganar,Hannu yasa a cikin aljihun wandon suit din jikinsa bak’ar Wallet ya fiddo mai kyaun gaske ya bude,Kudi ya kirgo sababbi fil kamar lokacin aka buga su,mik’ama yarinyar yayi wadda ke tsaye ta kafe sa da idanu tasa hannu da sauri ta kar6a,aje fasassan bokitin tayi a kasa ta fara kirga kudin dubu ukku ta gani da tsananin mamaki ta d’ago lokacin har ya juya da sauri tace”Yallabai kudin sunyi yawa ai” Hannu yad’an daga ba tare da ya juyo ba yace”ku siya sabon bucket da sauran” ya cigaba da tafia wurin da motarsa take,
Mai tallan kuwa har lokacin juya kudin take da mamaki hakanan bai santa ba ya bata har dubu ukku da sauri tabi bayansa tana fadin “Yalla6ai,yalla6ai…” lokacin har ya kama k’ofar motar zai bude jin yadda take ta faman kiransa da yallabai yasa shi juyowa”What again? Ya tambaya da kosawa,”umm dama²…. ta kama inda-inda sakamakon kafeta da ido da yayi,ya lura da yadda ta dabarbarce,dan sakin fuska yayi yace”Uhum ina jinki dama me? Dama so nike in tambayeka in innarmu ta tambayi wanda ya ban kudin wa zance mata? ta k’arasa maganar tana sunnar da kai k’asa”just tell her wh….ki fada mata abunda ya faru kawai”ya juya zai shege cikin motar, da sauri tace “ai tana iya cewa k’arya nike ni na tsara hakan kullum tana ce mana kar wani ya bamu kud’i bamu san shi b,ko yace zai siye mana yayi mana abunda bai dace ba”ta gama maganar kanta a kasa,
d’an murmushi yayi na gefen fuska wurin ya lotsa alamar yana da dimple,yaji dadin maganar da tayi ko ba komai hakan ya nuna rashi ne yasa suke tallan ba wai ra’ayi ko son kudi na wasu iyayen, Juyawa yayi yabude motar ya shige ya jawo kofar ya rufe,tana dai ta kallonsa don gaba daya komae yayi burgeta yake sai da yayi ma motar key kafin ya bude Glove box din gaban motar kudi ya kirgo dubu biyu juyawa yayi ya mik’a mata da d’an murmushi a fuskarsa yace “ki hada da wannan ki kai ma Mom din naki” Maida hannunsa yayi ya murza key din jikin motar tana dai ta kallonsa da tsananin mamaki sai da motar ta tashi sannan glass din murfin motar ya fara rufewa sama a hankali juyawa yayi ya kalli yarinyar da har lokacin take tsaye tana ta faman binsa da idanu “Ki ce ma Mom din naki dan gidan HAJIYAR SENATOR ne ya baki” daga haka ya ja motar fuuuu,

Kwai Cikin Kaya Book 2 Complete Document

“Hajiar Sanata! Yarinyar ta maimaita da mamaki had’i da rike ha6arta da hannunta daya,sai kuma ta saki wata irin dariar farinciki da sauri ta juya komawa tayi inda sauran Awarar ke a zube k’asa tace “bari in kara dan kwashe wadda batayi k’asa sosae ba da ansa cikin mai k’asar zata fita ko mu sai muci” a saman marfin bokitin ta zuba mai kasar,mikewa tayi da dan gudu-gudu ta koma cikin lungun da suka fito tun da farko.

Yarinyar data 6arar da Awarar ce ta lek’o da kanta daga cikin zauren gidan da ta 6uya,round face gare ta mai dauke da madaidaicin hanci mai dan tsawo tana da dan kumatu,idanuwanta kuwa suna da dan girma sam baza’a kira su da k’ananu ba,tana da gashin gira wanda yake kwance lub haka kuma gashin idonta nada tsawo gazar-gazar bakinta madaidaici ne le6anta na k’asa nada dan fad’i sosae,kalar fatar ta kuwa fara ce sai dai ba sol ba,Amman kana kallonta zaka kirata da fara, sai da ta waiwaya hagu da dama ta tabbatar ba kowa kana ta fito,cikin sand’a take tafiya tana yi tana waiwaye har ta iso bakin lungun daidai inda ta 6arar da awarar,tsayawa tayi tana kallon sauran awarar dake a k’asa, Kafarta tasa tana tattake awarar tana cewa”Gobe ma ta kara sawa a doke ni” ta fada a fili tana mummurguda bakinta gefen kumatun ta na lotsawa sosae alamar tana da dimples, jin k’arar mota ta taho a bayanta yasa tayi saurin juyawa hadi da d’an tattare Skirt dinta da hannayenta biyu tana shirin rugawa ganin ba motar mutumin d’azun bace yasa ta saki skirt dinta tace “In ma shine yazo banjin tsoron sa koda kuwa Aljani ne ehee” ta fad’a lokacin da ta fara tafia ta miki hanya tana yi tana waiwayen bayanta tana watsa hannuwa gami da turo baki,

Yar tafiya tayi kafin ta iso bakin wani Gida wanda keda shafen plaster ba fenti a jikin bangon gidan daga gaban gidan akwae k’atuwar kwata wadda ke zagaye da gaban gidajen layin saidai a rufe take da slabs daga d’an gefen kofar shiga gidan akwae Kiosk a saman rufaffiyar kwatan gaban gidan,shiga cikin zauren gidan tayi wanda keda K’ofa da kuma Window a cikinsa da alama irin d’akin zauren nan ne,

A bakin kofar shiga cikin gidan ta tsaya,dan leka cikin tsakar gidan tayi wanda yake wayam ba kowa,dawo da kanta tayi cikin zauren ta rik’e habarta da hannunta na dama tunani ta shiga yi “Ba’a kawo karar tawa bane?kodai sun zo har sun tafi” jinjina kai tayi a fili tace”Inma an kawo k’arar tawa nasan abunda zance,cewa zan yi tsokanata tayi,ta kuma yiman daria harda gwalo wai sun sa an bige ni” ta k’arasa maganar tana faman mummurguda baki dimples dinta na lotsawa,
A hankali tasa k’afa cikin gidan mai dan matsakaicin girma wanda kasan shi ke malale da siminti gaba daya,d’akuna biyu ne a cikin gidan wanda kofofin su na kallon juna,dakin da ke a bangaren dama babban daki ne yayin da na bangaren hagun k’arami ne a jikinsa kuma kicin yake wanda shine a farko in ka shigo gidan daga bangaren hagun,sai dan fili wanda da gani wurin yin Wanke-wanke ne a gefe daga tsakiyar filin akwae yar Bishiya,daga nan kuma sai Band’aki da ke a can gefe bangaren da kofar shigowa take,

Shiga tayi cikin gidan a hankali tana yin sand’a “Daga ina kike? Aka jefo mata tambaya daga bayanta,cikin yar razana ta juya,wata farar dattijuwar mata ce mai dan tsayi,sam bata da jiki sai dai ba siririya bace sosae tana da tsagun yan baka a bakinta,tsaye matar take da buta a hannunta da alama daga band’aki ta fito “dake nake Fatuu” ta k’ara fada da muryarta irin ta fulanin da suka ji hausa sosae,in’ina fatun ta fara yi,ta rasa mi zata ce don tunani take ko an kawo karar abunda tayi ma mai tallar Awarar nan,”Halan kina can wurin jawo man fitinar da kika saba ko” ta k’ara jefo mata tambaya,da sauri fatun tace “A’a gwaggo..” tana ta faman zare ido “to ki fadan ina kika je don na lek’a neman ki da kaina baki a waje” Goggon ta fada ta kafe ta da idanu,”Umm… gidan Hajiyar Sanata naje gaishe ta” taba gwaggon amsa da alamun rashin gaskia a fuskar ta,”Allah yasa da gaske kike don banga ranar da garin Allah zai waye har rana ya fadi baki jawo mun fitina ba” jin hakan yasa fatun gane ba’a kawo k’arar abunda tayi ba” da karfin gwiwa tace “Allah gwaggo daga can nake fa” gwaggon tace”to wannan d’amarar da kika ci da gyalen ki ta mene?” “ba komai kawai gyalen ne ya ishe ni yana ta fad’uwa shine na kulle shi anan” tayi maganar tana kokarin kwance gyalen daga kugunta,

gwaggon taci gaba da magana”Ai in ance kisa hijabi sai ki k’iya sam bakya son sa hijab ke kinfi son gyale gashi ko yafawar ma baki iya ba kullum yana ruke a hannu ko daure a k’ugu,to ina amfanin hakan in anyi magana kice ke baki saba sa hijab a kauye ba” ta karasa maganar tana shiga cikin gidan,

“Allah gwaggo hijab din shak’e ni yake fa, ni ban saba sawa ba,acan ruga fa wani lokacin ko gyalen ma ba sawa muke ba” ta karasa maganar da sigar shagwa6a tana bin bayan gwaggon “Ai sai ki tayi tunda anfad’a maki nan ma kauyen ne, da kina son sa hijab din ai da yanzu kin saba dashi yaushe rabon ki da kauyen kusan shekara ta ukku kenan fa, kawae dai kin fi son kisa gyalen yadda zaki ji dadin nemo man fitina,Kullum cikin daukko man magana kike nikam na fara gajiya wllh kuma zan yi maganin ki indai baki bari ba tunda na lura sam duka bai maki” ta k’arasa maganar lokacin da ta iso bakin kofar dakin da ke a bangaren dama, d’aga labulan kofar tayi ta shige harda butar da ke a hannunta,ita kuwa fatun labulan kofar da ke kallon wadda gwaggon ta shiga ita ma ta daga ta shige,dakin baida girma sosae, akwae Gado irin na karfe mai spring yana da bakin fenti da katifa wadda aka rufe da tsohon zanin gado,A bangon dake kallon gadon kuwa wardrobe ce mai gida biyu da kananun gidaje a kasa suma guda biyu,ta dan ji jiki sannan yar madaidaiciya ce ba mai tsawo ba,a samanta akwae jakunkuna,daga gefen ta kuma dressing mirror ne kalar ta shima karami ne wanda hannuwan drawers din jikin shi wasu duk sun balle haka mirror din jiki dan guntu ya rage,akwai leda shimfide a dakin wadda ta ji jiki don duk wasu wurare sun farfashe,Saman gadon ta fada hadi da fadin “Washh” sai kace wadda tayi wani uban aiki banda neman rigima,tunani taci gaba da yi “ko sai yaushe zasu kawo kara tan…” k’wafa tayi a fili tace”Allah yasa su kara sawa a doke ni wllh nasan abunda zan yi masu….”Muryar gwaggon tace ta katse ta”fatuu fito ki tankade man garin can na cikin kicin yamma tayi in samu in daura girki……,Fatuu ko bakya jina ne wai? cikin d’aga murya tace “Ina ji fa,gani nan fitowa..” mik’ewa tayi ta nufi k’ofa sai faman k’unkuni take tana jujjuya kai alamar bata son yin abunda aka sata yi.

KARANTA: Gidan Uncle 2 Complete Hausa Novel

1 Comment

Leave a Comment