Hausa Novels

Kwai Cikin Kaya Book 2 Complete Document

kwai cikin kaya book 2 complete document
Written by Aishat

Barkanku da zuwa shafin karatun littafan hausa novels inda zaku karanta littafin kwai cikin kaya book 2 complete document.

Kwai Cikin Kaya Book 2 Complete Document

Kowa yana cike da murnar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni, ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata aiki a randa ta dawo.

Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata suma suna tayata dariyar.

Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a
yanzu. Sai da muka gama dariyar sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai
nazama dss a yanzu.

Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.

“Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi’a, kamanta ALLAHN daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi, ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa, kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna ALLAH yafi
sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini aunty Shahudah…….”

Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty
Shahudah gidan. ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.

Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai kecin raina, akwai wani
abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.

Yau data kasance juma’a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima ya dawo, kowa yay
murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace.

Nidai ina daga baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako
sunana a cikin zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama Mom.

Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna zaune ne muna cin abincin dare. Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina yakamata na basu waje su gana da mahaifansu.

Duk da kasancewar asabar ce babu aiki ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci azkar nai karatun Qur’ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.

Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom. Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da aƙidar rashin son takura.

KARANTA: Gidan Uncle Page 11-20

Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan.

Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.

A daren jiya juma’a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso gidansu Jawaad, cewar
Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.

Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.

Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da tunaninsu bai taɓa kawo musuba
anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.

Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu gungun ƴan ta’adda
da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami
nasarar kama wasu a cikinsu, yayinda wasu suka gudu.

Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis da gajiya, ga yunwa dake
cin hanjinsu ta bala’i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu.

Rose cema dai kawai ta kasa juriyar
kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad
ma baiso akai aikin da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.

A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban
ne ya bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.

Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin hankalin da ake ciki a
gidan nasu. Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga ƙololuwar tashin
hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar tai bala’in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata
lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan
ƙarfe kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.

Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin su amso, abinda yasa
ba’aje tun jiyaba saboda ba’a nan cikin gari bane, inda ya baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka maidashi
asibitin can garin.

Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa, dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso, kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da boko keda tsada da daraja kuwa……

Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke- koke na ƙaruwa, babu shiri na dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne. Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom.

Zuciyata tai masifar harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin. Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin zuciyata aduk sanda
ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga karanto addu’a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.

Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga sashin ne nakai idanuna kansu
tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da
yay face-face da jini, alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai
rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na fashe da kuka mai cin rai da zuciya.

WASU NA KARATUN

Yar Sadaka Book 2 Complete Hausa Novel

Littattafan Hausa Novel Complete

Karanta Kalaman Soyayya

1 Comment

Leave a Comment