Hausa Novels

Yar Sadaka Book 2 Complete Hausa Novel

yar sadaka book 2 complete hausa novel
Written by Aishat

Tag: yar sadaka book 2 complete hausa novel, Year sadaka book 2 complete, Year sadaka kashi na biyu.

Yar Sadaka Book 2 Complete Hausa Novel

Alhamdulillah God has brought me back to health. I’m sorry, I’m sorry, I’m not like that, even though some of you know about my loss.

Bismilaahir_Rahmanir_Rahim

Yar sadaka book 2 page 1️

Haba mana yarinya Se San jikin tsiya mama ta fada tana ture Yasmeen dake kwance bisa cinyanta’ qara rungume mama Yasmeen tayi tana turo baki tare da zuba Mata shagwaba tace’ mama Allah kaina ke ciwo jinake kama bazan iya rabuwa dake ba mamana ta fada fuskanta dauke da damuwa.

Murmushi me kayatarwa mama tayi tana niyyan Magana daddy ya shigo dakin d sallama Yana cewa’ uwar amarya kina inane? ya Zaki zo daki ki kwanta keda ‘yarki kubar jama’a”

Sannu da zuwa daddyn Yasmeen mama ta fada tana murmushi’ wallahi kaga tin dazu nake fama da ita taqi dagani Se faman shagwaba take kama wacce zatasha nono.

Dariya daddy yayi Yasmeen Ko ta safke Kanta qasa tana murmushi.

Kallan mama daddy yayi yace’ hajiya Tashi Yan daurin auren Sunfara shigowa nasan zaku gaisa’ dasauri Yasmeen ta tashi tana mejin farin ciki Dan dama abinda takesanji Kenan tin shigowan daddy da dariya ta fita a dakin daddy ya bita da kallan Yana cewa’ ‘yar lele yau baza’a kula daddy ba?
Murmushi mama tayi tana yafa mayafinta tare da kallan pink shadda dake jikinta tana cewa’hubby duba kaga yadda take neman batamin Kaya kai mashkur ya hadu da aiki’ zaro Ido daddy yayi Yana cewa wanne irin aikine haka?
Aiki Dai irin wanda kuke sani kaida ita ‘ inbadan yanada hakuri ba ai watarana zaneta zeyi idan tace wannan shagwaban zatayi masa’ dariya daddy yayi yace’ haba dai nima ban zaneniba balle Shi ya tabamin yarinya.

Girgiza kai mama tayi ta Fito a dakin Jin ana buga kofan’ tana fitowa taga aunty maryam tsaye jikin kofan’ dasauri tace lah aunty maryam kunzo?sannunku da zuwa.

Eh Kya tambaya kinsa mijinki da ‘yarki a daki kinbarmu’ se faman jiranki muke jama’a duk sun taru’ murmushi dauke a fuskan mama tace ayi hakuri aunty kinsan halin Yasmeen wallahi Duk ita ta batamin lokaci.

Uhmn zaku Dena wannan abun daga Ku Har ita’ tinda Shi aure ba wasa bane’ ita Dai mama batace komai ba tabi Bayan aunty maryam suka fito’
Tinda suka fito’maroka da  makida suka fara Mata kirari nan take ta bude jaka tana raba musu kudi.

Jikin Yasmeen a sanyaye  ta Shiga cikin dakinta’ Bata Ko Kalli su mubeena da zee tare da sauran kawayenta da tin shigowanta suke faman tsokalantaba’ kan gadonta Na alfarma ta fada tare da rumgume pillow tana juyi.
Dariya suka sa kafin mubeena ta matsa kusa da ita tana cewa’ hy kawata menene abin rumgumar pillow aita pillow ta qare tafada cike sa tsokala.
Dukan wasa Yasmeen ta kai Mata tana cewa’ ni da Allah ki kyaleni’wallahi Duk wani iri nakeji kinga tin dazu mashkur ke kirana nakasa dauka.

Wanne irin Abu kikeji haba amarya’ ke Duk fa wayan amarya’ se ansha manta zee ta fada tana Mata gwalo.

Hararan zee tayi kafin tace’ ni mijina ba jarababbe bane kima dena wannan zancen’ hhhhhh suka sa hewa tare da dafawa da junansu’ haushine ya isa Yasmeen ta rashi da gudu ta fita a dakin ganin Suna neman sata kuka’ dakin mama ta Shiga anan ta kwanta tayi lamo tana tinanin abin kaunarta miji agareta mashkur.

___________

Zaune take a daki ta rasa abinda ke Mata dadi’ haka Kawai takejin zuciyanta Na harbawa da sauri da sauri’
Ya Allah nijlah ta furta a fili tare da dafe Kanta tana cewa’ Wai meke faru dani’ kusan minti shida ta dauka zaune tana nazari’ ta Zara a wanne gurbi ya kamata ta ajiye mashkur’ lamarinsa da tinaninsa Na damunta musamman a ‘yan kwanakin nan Bata da aiki Sena mafarkinshi hannu biyu tasa ta dafe Kanta tanasan yin Kuka sedai Bata ga amfanin yin Hakan ba Dan ita a tinaninta sotake ta manta da wani mashkur ta dauka sabuwar rayuwar data zo Mata sedai Duk da haka takasa samun sukuni Har Seda hawaye masu zafin gaske suka zubomata.
Motsin shigowa dakin da’ake qoqarin yine yasata saurin goge hawayen ta zubama kofa ido.

Mujaheed ne ya shigo fuskansa dauke da murmushi’dubanta ya Shiga yi Yana qoqarin gano damuwa dauke a fuskanta.
Murmushin dole nijlah tayi sabida bataso ya gane wani Abu ya dameta da nacin tambaya’ Bata ida tinanin ba Mujaheed ya qaraso saitin inda take.

Kallanta yake cike da tausaya tare da matsananciyar soyayyarta’ ganin irin kallan dayake binta dashine yasa nijlah saurin juya masa Baya taba cewa’ ni ni.

Dariya yayi ya samu guri kusa da ita ya zauna’
Yaya dai baby? Jikin ne naga kin dawo daki ke daya?
Turo masa Dan qaramin bakinta tayi’ kafin tace’ ah ah’ naji sauqi hutawa Kawai nakesanyi.

Bega munintaba sema wani irin kyau yaga tayi masa nan ya karyar da kai Yana cewa’ Nima nagaji kinga semu huta tare Ko babyna?
Zaro Ido nijlah tayi kafin ta murguda masa baki tana cewa’ wa ni’ Allah babu ruwana kaima ka tafi dakinga kafin aunty husna taganka.

Cike da shagwaba Mujaheed yace’haba baby kin manta gobe e yanzu kinzama mallakina to menene abin gudu ya fada Yana janyota jikinshi.
Lamo nijlah tayi a faffadan qirjinsa tana shaqar dandadan kamshinsa’ sedai Duk da haka Bata iya sakewa sosai ba sabida tinanin mashkur daya addabi zuciyanta.

Sun kai minti biyu a haka kafin nijlah tayi qoqarin janye jikinta’
Kallanta Mujaheed yayi yace’ baby yanaga Duk jikinki yayi sanyi Ko Dai bakisan aurena Ko Kuma Dan bakiji nace za’ayi wani shagalin biki bane yasa Duk kika lanjaremin.

Girgiza masa kai tayi kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallansa tace’ haqiqa Mujaheed inasanka some tsanani sedai akwai wani kulli Wanda bansan ta yadda Zan kunce saba’ bisa ga wannan dalili yasa’ kasa qarawa tayi ta fashe da Kuka.
Dasauri Mujaheed yay Kanta Yana cewa’ wannan wanne irin kulli ne? Nijlah kisani ayanzu kin wuci komai kinfi karfin kowa da komai dan Zan iya mallakawa mutum kudi adadin gashin ragumi akanki da Duk Wanda ya tabamin ke’ nijlah ki gayamin namiki alqawarin sunce wannan kullin Duk kuwa da girmansa.

Tashi nijlah tayi ta Dan matsa daga kusa dashi tana cewa’ Kash Mujaheed abubuwa da yawa kudi basa iya maganinsa Nima Ada nayi wannan tinanin irin Naka a lokacin da naira biyar kemin wahalar samu’ Se daga Baya nagane kudi ba komai bane illah wata hanya ta Bata idan har mutum be bisa ta hanyar data dace ba.
Kai nijlah Wai Dan Allah yaushe Zaki sauko kidenamin irin wannan kalaman’ kullum baki da aiki saina dagawa kanki hankali’ Toni kinga ki yadda a daura auren idan yaso daga Se ayi komai.

Shiru tayi tana kallansa kafin Tayi Magana yayi saurin katseta’ kinga nijlah kefa yarinya ce Babu abinda kika sani game da aure kibari adaura auren Na tabbata sekince kinyi auta da ba’a daura mana aure tin tini ba’ nizan kula da rayuwarki Zaki Zama tauraruwa cikin dukkan Matan Duniya Zan mallakamiki komai nawa Zan zame Miki mijin tace Se yadda kikayi dani’ wallahi shekarunki bazasu sa na wahalar dake ba nidai burina Na mallakeki ki Zama tawa ta Har abada.

Sosai kalamansa suka shigeta Har saida fararen hakoranta suka bayyaba’ Duk da gabanta Na faduwa Amma Hakan be hanata amincewa da maganan aurensu ba nan suka zauna Yana Mata Hira masu Dadi tare da Mantar da ita ita din wacece.

_______

Zaune suke a babban falo kowa kagani kasan Yana cikin farin ciki’ abincine Kala da Kala iri da iri kowannensu da Wanda ya zuba Duk da ba wani ci suke ba.

Aunty lateefah ce tashigo cikin falon da lemo a hannunta kusa da mummy ta zauna tana cewa’ Mummy me zakici a zubamiki kafin anjima gidan ya cika da ‘yan biki nasan lokacin Babu abinda Zaki iya chi?
Murmushin kasaita mummy tayi tace’ah ah lateefah ni yau kobanci komai ba cikina ze kasance a koshi sabida na auren da auta macen data dace ba Wanda ya daukomana ba.
Uhmn hakane mummy Wai Haryanzu ba’aga nijlah ba?
Inako za’aganta lateefa aimu wannan ba qaramin farin muka samu ba Dan da tana nan da ba’ayi auren nan ta Dadi ba Dan muddin mashkur Na ganinta baze taba nutsuwa ba.

Dariya lateefa tayi tana cewa’ gaskiya ne mummy ni abinda ke bani mamaki Wai ace yarinya qarama kama nijlah Har tasan wani Abu Wai Kishi kai mudai Babu abinda zamuce se godiya ga Allah.

Hakane kinga Tashi gasu Mami sun zo ki kaisu daya falon sabida nan akwai wadanda nake jira.
Dasauri lateefa ta Tashi tana musu sannu da zuwa.

Ango ango kasha kamshi irin wannan daukar wanka haka’ murmushi mashkur yay Yana cewa kaga tin dazu nake Kiran mutumiyar Bata amsa ba Ko ina ta aje wayan.

Dariya Nasir yayi yace’ kaima kasan Yasmeen da rawan kai Na tabbata tana tare da kawayenta Suna tsara yadda partyn gobe ze kasance.

Eh Kuma hakane Sai kuma yayi tsaki Yana cewa’ kasan Allah Nasir naso ace nijlah Na nan za’ayi wannan partyn da Kaya iri daya zamu saka itama tasan tayi aure.

Zaro Ido Ahmad yayi dake zaune gefe besa musu baki ba Se yanzu yace Aiko da ankarma Mata abanza’ meyasa Haryanzu ka kasagane haukan kishin Yasmeen Sai kace ba’a gabanka take wasu abubuwan ba?

Yauwa Ahmad gayamasa Dai cewan Nasir Yana mamaki.

Tabe baki mashkur yayi a hankali Kuma ya bude baki yace……

Idan Baku mantaba nagayamuku ‘yar sadaka book 2 Na kudine Dan haka nakeso kubani hadin kai gurin karanta qarashen wannan labari ta hanyar amana’ banaso Duk Wanda ya Biya kudin karatu ya fitarmin dashi idan akayi haka Zan dakata da rubutu’ idan kinsan Zaki fitar Ko Zaki siya ki zageni Dan Allah karki siya masoya Kawai nake buqata.

KARANTA: FURAR DANK’O Chapter 1

1 Comment

Leave a Comment