Hausa Novels

Soldiers family page 21&22

Soldiers family page 21&22
Written by Aishat

Barka da zuwa wannan zuwa shafin namu na littafan hausa novels inda a yau muka kawo muku Soldiers family page 21&22 by autar alheri.

Soldiers family page 21&22

Tag: Soldiers Family Page 21&22

Jalaludeen da Al,Hassan agaba se abbe da mama abaya.. perlon cike yake da ahalin Alhaji shuraim suna meeting saka makon auren da aka d’aurawa samarin gidan ba bu shiri… Alhaji Imran ne ya d’ago yana amsa sallamar da sukayi aiko yayi Ido 4 da abbe arazane ya mik’e yana fad’ar Habeeb…hakan yasa gabaki d’aya mutanen dake perlon suka d’ago suna kallan k’ofar dan gaskata abunda sukaji abbansu na fad’a.

Aiko dai shid’inne ba wani ba kamun suyi wani motsi tuni Alhusain da Suhaif sunkai bakin k’ofar suna k’ara ware idonsu Dan sunkasa gasgata abunda idonsu kegani…ganin sunyi tsaye sunka cewa komai yasa Jalaludeen cewa abbe nefa dagaske suhaif bawaniba aikamun yarufe Baki Suhaif ya rungumeshi yana fad’ar, “abbe dagaske mafarki najeyi ko gaskiya?” Yaya jalal “abbe wlh abbe ne abbe ne Husain zokaga…”cikin sauri Husain ma ya rungumeshi tare da fashewa da marayan kuka yana k’ara shigewa jikin abbe d’in hakan yanad’asu duka yarunguma Yana share k’walla..kamun yasakesu Yana nufar Yan uwanshi da suka zo gareshi cikin farin cikin sake ganinshi araye suka shiga rungumarshi dukkansu d’aya bayan d’aya suna hamdala ga ubangiji talikai…sunjima ahakan kamun Alhaji Jameel ya kama hannunshi ya kaishi har inda habibbty kezaune tana sharar k’walla.

Duk’awa yayi ahankali yace yace habibbty na tare da fad’awa jikinta yakankameta sosai ajikinshi Yana sauke numfashi itama habibbty hakance takasance agareta wani irin farin ciki takejin kanta aciki marar misaltuwa gata ga hasken idaniyarta yadawo..sunjima ahakan kamun kowa yasamu wuri yazauna anasake gaisawa.. Jalaludeen ne yakama hannun mama dake rakub’e gefe yazo ya zaunar da ita kusan abbe Yana fad’ar abbe kaga su Abba kamanda y’arka ya fad’a cikin tsokana… murmushi abbe yayi yaname kamo hannun mama ya rik’e Gam tare da cewa, “ba,abunda zesa namanta y’ata Jalal ina sane da ita…se alokacin kowa ya kula da Mama” Aiko Ido ya koma kanta musamman samarin gidan domin wani Dan iskan kallo shareef da Najeeb ke jifanta dashi na tsantsar barinkanci…agefe d’aya Kuma Fahad ma yakafeta da Ido ko kiftawa Babu karshedai kasa hak’uri yayi yace Yaya jalal wacece wannan black Beuty d’in?

Hararasa yayi kamun yace k’anwata ce domin Yar abbe ce…Masha Allah cewar habibbty kamun race Yar albarka zonan inganki kinji? Bamusuko mama tamik’e dudda yanajin yadda idanun wayannan mayun keyawo akanta..kusan habibbty tazauna taname sinnarda kanta ak’asa.

Kowa shiru yayi yanata kallon abbe se,a lokacin yakulada Babu sauran yaransu Kuma Babu ammy kallon sulaiman yayi yace “”inasu Yusuf da Alyasat Lateep ko suna London ne? “” Aa abbe sunan barana kirasu” ya fad’a tare da barin perlon

“Sannunki y’ammata cewar shareef Yana kallon mama… d’agowa tayi taga yadda yaketa wani lashe Baki Yana k’ib,k’ibta Ido Aiko tazabga mishi wata uwar harara kamunta mayarda kanta k’asa batareda ta,amsaba..Ido ya zaro yace fa dariya sukayi lokaci d’aya ganin yadda tawani taderai…suhail yace gaskiya abbe wannan Yar taka akwai tsiwa batasan gidan sojoji tashigo bane inda za,agyra Mata zama…ah,ah fa bawanda zetab’amun y’a tinyanzu ma gara kusani…Zaid ne ya balla Mata harara shima yanajan k’aramun tsaki dominsha yatsani reni…ungunan Zaid dady yafad’a Yana Ware masa hannuwa dukkansu sukayi dariya kamun wani yace wani abun Sega sulaiman da lateep sunshigo yusif na bayansu warin ihu Lateep yayi Yana zaro Ido tare da fad’ar abbeee dak’arfin gaske hakan yasa Alyasat daya tsaya waya shigowa perlon babushiri..shiko Yusuf mutuwar tsaye yayi yamakasa cewa komai ganin dagaske abbenne gashi har Lateep yaje wurinshi yasa shima yaja kafafunshi ya,Isa dukkansu rungume abbe suna kukan farin ciki shiko se shafa bayansu yakeyi Yana murmushi.

Alyasat kuwa yakasa motsi tunda yashigo perlon kallan abbe kawai yakeyi lus of control gawanu mugun bugawar zuciya dayakeji tinda yadunfaro perlon….ganin yak’i shigowa Kuma yak’i komawa yasaka abbe mik’ewa dakanshi yazo wurinshi tare da riƙoshi yace yaron ammy nine fa ko baki farin cikin ganina ban..tinkamun yak’arasa Alyasat ya bashi wani kyakkyawan hug meratsa zuciya matse abbe kawai yake ajikinshi Yana jujjuya Kai kamar ze maidashi ciki kusan minti 5 ahakan seda yusif yace bro karka ballamana abbe fa wannan matsa haka…seda yabawa kowa dariya kamun alyasat yad’an d’ago abbe daga jikinshi yana hararar yusif kana yace abbee cikin wata raunanniyar murya..na,am yaron ammy Kuna lpy?

Shiru yayi Yana kallan abbe Jin tambayar dayayi masa kamun yasakeshi yanadanyi baya kad’an tareda kafe abbe da Ido cikin kallon tuhuma wa mahaifin nashi kana yace abbe dama kana Raye kabarmu? Abbe aina kaje duk tsawon shekarunnan? Abbe kasan awanne Hali ammy take? Abbe kasan wani abun mukeji aranmu Idan muka bede ido bamu gankaba why abbe why? Sekuma ya dafe zuciyarshi…cikin sauri abbe yak’arasa gareshi tareda rikoshi yace alyasat Ina ammyn ku? Miyasameta? Minene yafaru bayan barina gida? Shiru alyasat yayi Yana kallon mahaifin nashi kamun yarik’o hannunshi kawai suka fita daga pert d’in ganin hakan yasa duk mutanen wurin suka mara musu baya Jalaludeen ne ya kama hannun mama Yana fad’ar muje k’anwata ahakan suka fito suna boye dasu abaya har pert d’in ammy bedroom d’inta yawuce dashi har bakin bed d’inta inda take kwance kamar matacciya domin rayuwarce kawai ajikinta..

Karb’e hannunshi yayi d’agana alyasat Yana tallabo baiwar Allah kamun yace innalillahi wa innailaihhiraji un alyasat miyasamu ma,Isha? Mike faruwa ne Wai ? Yafad’a dagarfi tared a fashewa da kuka me cinrai… habibbty ce tad’afashi tana fad’ar kayi hak’uri habibullah daga ranarda aka wayi gari baka d’aga wannan lokacin mukarika ganin chanin abubuwa awurin ma,Isha sedai ba Wanda yakawo komai aranshi saboda atinanin mu damuwar rashinkace sai dai Ashe abun ba hakan bane domin se gaba yakeyi bayan wata biyu da tafiyarka ma,Isha Takoma azaune Bata iya komai ai anmata muskarta kawai zaka kallan kagacewa ita me lafiya ce ahakan aka duk’ufa nema Mata magani ba asitin da yarannan Basu kaitaba Amma abun yaci tura dak’arshe Kuma ciwon yak’ara tsanan izuwa yadda kaganta ayanzu..tinda habibbty tafara magana wurin yayi tsit ana saurararta ba,abunda ketashi adakin se kuka abbe Dana Al,Hassan gabaki d’aya zuciyar kowa tayi rauni.

Acan waje kuwa jalaludeen ne kefamada mama akan tashigo cikin gidan ammafa Abu yaci tura domin takafe kabb wuri d’aya Kuma yayi maganar duniya takasa Koda dogon motsi…abunda Jalaludeen baisani ba miyagun aljanun da suke part d’in ammy ne suka hanatashiga wanine daga ciki yarik’e ta domin tabbas tashiga gidan za,asamu matsa babba akan aikinsu…shiko jalaludeen ganin yayi da k’arya yayida gaskiya tashiga Taki se kawai yazaro wayarshi yakira alhassan domin layinshine akai hakan kawai yaji baze iya d’ayawa yabartaba Don yakira abbe garaya Kira wani agayawa abben.

Kamar Kuma yasan abunda kefaruwa domin wannan hatsabibin aljanin dagawarshi kawai yake jira yad’auketa…bugan duniya yayi Alhassan be d’auki wayaba se kawai yakira najeeb Yana d’agawa yace najeeb gayawa abbe fa zaraah Tak’i shigowa..”okay kawai yace tareda juyawa yace abbe Yaya Jalal yace Wai zaraah Tak’i shigowa…kowa dake wurin kallunshi yayi alyasat Kuma seda zuciyarshi tabuga kamar zata balle tafito fili sabida kawai wannan sunan da,akira atake yaji yatsani me sunan dudda besan kowacece ba Amma dajin yadda zuciyarshi ke bugawa yasan Babu alkairi atareda ita..

Wacece zaraah? Zaid yafad’a azafefe domin yayi tinanin marar kunyar yarinyar Nance dasukazo da,ita…shiko abbe ajiye ammy yayi tareda Kama hanyar fita hakan yasa Yusuf Sulaiman Fahad Lateep Najeeb din duk sukabi bayanshi Abba ma hakan dady kuwa habibbty yake rarrashi yayinda papu kezaune perlo suka wuceshi domin tin farko beshiga bedroom d’in ammy ba.

Suko suna fitowa abbe yayi wurinda take tsaye k’ik’am kamar andasata yace zaraan Abba miyasa bazaki shiga gidan abbankiba nanne gidana zumushiga kinji yafad’a Yana kamo hannunta Amma yajishi k’age koma duk zancenda yakeyi ko gizau batayiba..shiru yayi Yana kallon ikon Allah dudda yasan ba,ita kad’ai takeba Amma yasan bazasu hanata shiga gidanshiba tinda da saninsu yazo da ita hasalima da hannunsu suka bashi ita..shiko Jalaludeen kallonta kawai yakeyi domin Beman artabon da bibibo yayi dasu ba a lokacin da suka harbi abbe.

Kowa dai awurin yayi shuru masujin haushi naji masu mmki nayi Zaid da yafito daga baya shida alyasat dukkansu tsaki sukaja shidai gogan zagawa kawai yayi yawuce yayi da Zaid yadaka mata tsawa Yana fad’ar keeeee Wai wannan wanne iskancine abbe sa,ar wasarkine Yana magana kinyi banzadashi? Allah Idan nazo wurin Sena ballaki kana nashigo dakai dak’arfi…”no bro karka dajeta aibakuwa ce kawai kad’aukota dai kasan Abbi bazeji dad’i ba cewar Ameer dashi isowarshi kenan…Aiko gadan gadan yanufeta Jalaludeen naganin hakan yace Kai Zaid dakata banasan shirme…kafin yarube bakinshi kawai sukaga anyi samada ita dak’arfi irin anjefarda abun d’innan…dukkansu Ido suka zaro suna bud’e Baki madu kalima nayi masu salati nayi domin sunsanda tafad’o k’asa to seta kakkarye wannan muguwar jifa kamar wadda aka jefar cikin tashin hankali abbe ke fad’ar, “innalillahi wa innailaihhiraji un….”

KARANTA:

SOLDIERS FAMILY page 9

SOLDIERS family page 7&8

Soldiers family page 5&6

Soldiers family page 15&16

Leave a Comment