Hausa Novels

FURAR DANK’O 8 Hausa Novel

hausa novel
Written by Aishat

Barka da isowa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin FURAR DANK’O 8 by byllin abdul.

FURAR DANK’O 8

Farrr Mawaddat tai idonta a lokacin irin na wayayyun mata shagwaɓaɓɓu kuma ta ce, “Yaya mizai hanani iyawa. Matarsa bata gabana dan na ita zan auraba ai, kasancewarsa ba ɗan kowa ba, yawan ƴaƴansa duk baya gabana shi dai ɗin nake so ni dai. Idan kuma ban sameshi ba zaku iya rasani. ” cikin sauri Alh. Sulaiman yace, “A’a rufa mana asiri Kandala, indai Isma’il ne ki ɗauka kin samesa an gama”.

Taji farin ciki da jin furucin yayan nata ƙwarai da gaske, dan tasan zai mata ɗin kamar yanda ya faɗa. Sai dai mi koda Alh. Sulaiman ya tunkari Daddy da batun sai ya nuna shi sam baya ra’ayin ƙara aure, matarsa ƴar uwarsa uwar ƴaƴansa ta wadatar da shi”. Ran Sulaiman ya ɓaci, amma sai ya danne kawai.

Bai so Mawaddat taji wannan al’amari ba sai dai tama riga taji su da kunnenta, wannan yasa ta tada hankalinta matuƙa. Tare da tunkarar mahaifinsu a wannan karon kai tsaye. Shi Alhaji Garko harga ALLAH yayi farin ciki, dan Isma’il Jiƙamshi yarone haziƙi mai hankali da tarin nutsuwar da kowane uba zai so haɗa zuci’a da shi, amma bazai masa dole ba zai dai masa irin na manya.

Dan haka ya sallami Mawaddat akan cewar ta jirashi zaiyi magana da Daddy. Mawaddat tayi farin ciki, dan haka ta koma gefe sauraren mahaifinta, sai ma nemar aiki da tayi a inda Daddy yake dan kawai ta dinga ganinsa a kusa da ita.

Alhaji Garko bai samu damar yin magana da Daddy ba har tsawon watanni kusan biyu saboda busy da yay da ga shi har Daddy ɗin. Mawaddat taso sake tunkarar mahaifinta da batun sai dai bata samu zama da shi ba saboda yay busy da yawa ƙasar ma ba sama yake ba.

Amma tanata fakonshi. Ranar wata Lahadi data shiga a tarihin da Garko family bazasu taɓa mantawa da ita ba ta riskesu a ƙarshen wannan sati da ake saka ran dawowar Alhaji Garko daga dogon fatauci da ya tafi. Wato autar wannan zuri’a da kowa ke ma gata da tattali da ƙauna da tausayin halin da take a ciki mai kimanin shekaru tara a duniya Sultana aka wayi gari wani azzalumi yay mata fyaɗe, sai gawarta aka tsinta a can farkon layi ƙasan wata bishiyar dalbejiya na ƙofar wani gida.

Wannan al’amari ya girgiza wannan gida tare da mamaki matuƙa akan tayaya Sultanar ta fita daga gida har hakan ta faru?. Dada dai tasan ta tafi islamiyya da ake kaita a mota a ɗakkota, ta kuma tabbatar da ta dawo gab da magrib, daga nan bata sake ganinta ba a tunaninta ta kwanta ne a ɗaki, dan yanayin jikinta na masu sikila yasa bata da kwaramniya sam.

Sai da kusan sha biyu taje leƙata sai ta samu ɗaki wayam. Da farko bata damuba ta shiga kwala kiran masu aikinta da tambayar Sultana. Sai dai amsar ɗaya ce su basu sani ba, dan tunda ta dawo islamiyya basu sake ganinta ba.

Cikin ƙanƙanin lokaci Dada ta birkita lissafin kowa na gidan, dan gaskiya ALLAH ya jarabcesu da ƙaunar Sultana matuƙa, kodan tazo a ƙarshe ne batare da tunanin zuwan nata ba. Iya bincike babu Sultana a cikin gidan, dan haka nema ya koma har waje bisa zargin ko sanda ake sallar magrib ta silale ta fita duk da kowa yasan hakan ba halin yarinyar bane.

Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga ta an ganta, sai dai cikin jini kuma babu rai. Hakan bai hana a garzaya da ita asibiti ba, inda a gwaje-gwajen farko doctor ya tabbatar musu fyaɗe akai mata, amma ta farfaɗo daga doguwar sumar data tafi. Hankalinsu ya tashi, sai dai jin tana raye yasa sun ɗan ji sassauci.

Alh. Sulaiman ne ya kawo police aka tattare duk ma’aikatan gidan zuwa police station. Harda kukansa kamar wani ƙaramin yaro, bayan lokacin har Auta an haifa masa Tajuddeen. Bin cike iya bincike ba’a gane komai ba, inda Sultana da ake tunani da murnar ta fara samun lafiya a wani dare tabar duniya.

Dan haka kawai aka samu tana fisge-fisge da girgiza irin na firgitar wanda ya tsorata, duk da tana yin hakan dama tunda abin ya faru sai na ranar yafi na kullum. Da ƙyar doctor suka iya kwatanta ceto numfashinta, da ga ƙarshe dai tace ga garinku nan. Mutuwar Sultana ta zama kamar wata mutuwar babba a gidan, dan kowa ya koɗe ya jeme saboda kuka, sai dai halin da Mawaddat ta shiga yafi na kowa a gidan.

Har asibiti ta kwanta na tsawon kwanaki kafin ta dawo dai-dai. Watanni sun ɗan sake shuɗawa har zukata suka haƙura da shiga dangana game da Sultana, yayinda jami’an tsaro ke cigaba da bincike, sai dai maimakon a cikin gidan sai hankalinsu ya fara karkata waje akan cewar ƴan hamayyane kawai sukai hakan.

A ranar da Sultana ke cika wata biyu a cikin ƙasa Mawaddat ta tunkari Daddy da al’amari mai firgitarwa game da abinda ya faru da Sultana, inda ta nuna masa video data ɗauka a lokacin suna a cikin ɗaki tare da Alh. Sulaiman ga Sultana yashe cikin jini.

Tare da ɗakko masa zancen da ya san bayan Alh. Sulaiman da shi sai UBANGIJI kawai suka sani, wato ɓatar maƙudan kuɗaɗe a hannunsa wanda yayanta Alh. Sulaiman ɗin ya ranta masa ya biya batare da sanin mahaifinsu ba har yanzu.

Iya ƙoƙarin yayi danta fahimci gaskiyar al’amurin amma ta nuna sam bata da wannan lokacin, sai ma barazana data fara masa na in har bai aureta ba to lallai zata fallasa wannan video a gidansu dan kowa yasan yanda akai suka rasa Sultana.

Hankalin Daddy ya tashi matuƙa, sai dai Mawaddat ta masa mugun ƙullin da yay imani da in har bai aikata yanda take so ba tofa lallai bashi da wata mafita. Dole badan yaso ba ya amsa mata, tare da tunkarar mahaifinsu Alhaji Garko da batun yana son aure Mawaddat.

Alhaji Garko yayi farin ciki, yayinda Dada tai tsalle ta dire tace sam bata yarda ba. Ankai ruwa rana sosai game da wannan aure, dan an samu rabuwar kai wasu na goyon bayan Dada, wasu Alhaji Garko da Mawaddat.

Inda dai daga ƙarshe bayan an cuɗa an cuɗo ALLAH yay wannan aure da babu wanda yasan manufarsa sai ALLAH sai kuma su ma’auratan.

Mawaddat ta shiga gidan Daddy da gigiwar izza da gadara, inda daya motsa zai taka mata birki tamai barazana da wannan video recording da maganar kuɗaɗe. Hankalinsa a tashe yake, yayinda Mommy da Uncle Yousuf suka kasa fahimtar halin da yake a ciki lokacin duk da yanda yake son fahimtar da Mommy amma sai kishi ya rufe mata ido ta kasa fahimtar ba dukiya ko wani matsayi bane ya sashi aikata yin auren ma kansa balle biyema iskancin Mawaddat a gidan. (Wannan shine kuskuren Mommy.

Mata ya kamata mu dinga sanin kowanne yanayi da mazajenmu suka shiga koda akan mace ne. Mu dinga sassauta kishi a wasu gaɓoɓin rayuwa dan wani abun kanzoma bawa ba yanda ake kallonsa ba.) Daddy yata gwada son sace camara ɗin nan daga wajen Mawaddat sai dai a ankare take da duk wani motsinsa.

A magana ta gaskiya a zamanshi da Mawaddat bai taɓa jin sonta ba kona yini ɗaya, dan ko’a harkar auratayya ita ke kiɗanta ke rawarta game da shi. Sai dai yana yin dauriyar sauke hakkinta har ALLAH yasa aka samu cikin Lulu, sanadin cikinne ma yasa shi ɗan fara sassauta zuciyarsa.

Hatta da son ƙyautatama Mommy idan yay niyyar yi Mawaddat kan masa barazana, ga shi Mommy taƙi fahimtarsa, a kullum kawai tana kallon yana cutar da rayuwarta saboda ya auri ƴar masu kuɗi ƴar ogarsa.

Ana baifi sati guda a haifi Lulu ba a wani dare yana tsaka da barci Mawaddat ta tashesa. Hakan ba sabon abu bane da take masa, sai dai kuma bayan tashinsa cikin ɓacin rai ya fahimci tashin yau yasha banban da wanda take masa a baya.

Dan a mamakinsa ma sai gata durƙushe gabansa a ƙasa tana hawaye da neman gafararsa akan duk abinda ta aikata masa.

Ta ce, “Isma’il dan ALLAH ka yafe min, nasan na aikata abubuwa masu yawa a gareka tare da tilastaka aurena badan kaso hakan ba. Na kuma azabtar da matarka itama ta hanyoyi da dama. Ba komai ya jawo hakan ba sai ɗunbin so da ƙaunar da nake maka har ƙasan zuciyata.

Duk da inajin kishin matarka banso shigowa cikinku ta wannan sigar ba. Sai dai komai ya canja a dalilin wannan video na fyaɗe da kukaima Sultana kai da Ɗan uwana Sulaiman da kuma kuɗin daka salwantar a Companyn mahaifina bisa son zuciya kamar yanda ma samu labari.

A ranar da kukaima Sultana abun nan nayi kuka kamar zan mutu tare da jin tsanarku irin wanda ban taɓama wani mahaluki a duniya ba, na saƙa abubuwa daban-daban akan ku a ciki harda shafe numfashinku a bayan ƙasa. Sai dai zuciyata ta gargaɗeni da yin hakan tare da bani shawarar na dafaku da ranku cikin ruwan sanyi.

Na fara da kai ne ta hanyar maka barazana harka aureni, tare da nisantaka da matarka da nasan kana matuƙar so da ƙauna. Da farko naso na haɗa harda Yousuf, sai dai nutsuwarsa da hankalinsa yasa naji tausayinsa nama tsaya masa akan ya tafi makaranta dan bana son yaga abinda na tanada muku.

Burina sai na gama da kai sannan na koma kan rayuwar ɗan uwana Sulaiman shima, daga ƙarshe na fallasaku a idon duniya ku kunyata. Sai dai duk wannan lissafin nawa ƙaddara ta canjashi Isma’il a dalilin wannan cikin da ya shiga jikina a mistake, sau biyu ina yunƙurin zubar da shi amma hakan ya gagara, a karo na biyun ma sai likitoci suka tabbatar min idan na sake zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Wannan yasa na haƙura na barshi badan naso ba.

Sai dai kuma kana naka ALLAH na nashi, tashi kuma itace gaskiya. Wlhy Isma’il a ƴan kwanakin nan inajin kamar barin duniya ke gabatoni. Ji nake kamar bazan yi rayuwa mai tsaho ba. Shiyyasa na shirya faɗa maka gaskiya da neman afuwarka.

Tare da baka shawarar kaima ya kamata ka fito ka sanarma iyayenmu gaskiyar al’amurin game da abinda kuka aikatama Sultana kai da Sulaiman koda bazaka faɗi maganar kuɗaɗe ba. Ku karɓi kowane irin hukunci hakan zaifi zama masalaha a gareku da zuri’arku gaba ɗaya”.

Sosai jikin Daddy ke rawa a wannan lokacin, ya kama kafaɗun Mawaddat ya tadata daga durƙushen da take ya rungumeta a jikinsa. Sai kawai ya samu kansa da sakin kuka. Itama saita shiga tayashi. Sosai sukai kukansu kafin su zauna dan bata jurar tsaiwa yanzu. Suna zaune a tsakkiyar gadon suna fuskantar juna hannunsa cikin nata ya ce.

KARANTA: FURAR Danko Hausa Novel Complete

2 Comments

Leave a Comment