Hausa Novels

Ruwanzuma Hausa Novel Complete

hausa novel
Written by Aishat

Ruwan Zuma Hausa Novel 1

Tabbas soyayya wani farin cikine da ke haskaka zuciyarda babu yaudara aciki tamayardakai tamkar wawa ko akiraka mai rangwaman hankali  dan kawai kayi linkaya a ciki gashi bata duba kankanta ko tsufa bare tacemin nayi kankanta da inyi soyayya da irinki

haka tashigeni babu ko tausayamin dukda yayata tana matsayin kawarki

tahanani sukuni bare tabarni inyi karatunda ke gabana kullum ina tambayar yayata lafiyarki tun inajin shakka da kunya har yakaiga idan kuna waya nakancewa agaisheki antyna bata kawo komaiba saboda azatanta kema amatsayin anty na daukeki haka na daddage ina ziyartar gidanku haka kawai ince antyna tana gaisheki

bana bukatar kicedani zauna domin kuwa kyautar alawa zan baki najuya nakoma dan nasamu farin ciki sai kuke maida abun wasa har kukancewa jininmune yazo daya shiyasa nake hidimta miki

naso indannewa zuciyata in takura mata tadaina matsa miki amma nakasa saboda bazuciyata kadaiba nikaina inasanki gashi kuma nayi rashin sa a farkon soyayyata nafara da wacca ta girman taya zan furta miki nafara da kaimiki letter bayan kin karanta afusace kika juyo nikuwa atsorace nace aikoni akai wajanki

cillominda takardai kikai kikace naje na mayarmai babu abunda kika sanya agaba samada karatunki

sannu alhuda huda haka nafada azuciyata da ina sauraranki wannan da ninace nina aiko kaina inajin ball zaki dani da kafarnan taki abun takaici da ban haushi kaina zan lallaba da kikace bakya sona? Kokuwa kezan bawa hakuri da kika hau tutar fushinki haka na dinga rayawa a zuciyata sai kawai naji sautin muryarki kinacewa nayakuri tareda sanya kalmarda tafi bani haushi a karshe wato(kaninki) tabbas nina jawa kaina danaji ina kaunarki mezai sani inje in kai zuciyata inda abar rainawace agareki

kodayakema so baruwanshi dawani kin girmeni nida nakesoma wataran inzama angonki jinai ina wani bubbudewa kamar nazama angon.. sai kuma c

 

Ruwan Zuma Hausa Novel 2

 

Tabbas naso ace tsorona yayi kaura daga zuciyata kodan in sanar miki gashi kuma kawarki anty tace batayadda za ai tayimin campaighn agunki dabarace tafadomin babu tsoro ko fargaba naje gun kawarki antyna kenan tana zaune tana chatting da mijinda zata aura kamar yadda nake fata wataran na aureki

zamanayi kusada ita tareda fadin abokina yace yanasanki dasauri afusace tajuyo tanashirin wanke fuskata damari zatanta ita nake nufi abayaninki nan na warware mata komai amma tambayarda tayine yasa nakasa kara furta koda sunanki wane abokinnawane da wannan rashin kunyar koda yakema in fadamin sunanshi tayimai warning karya kara kallanki fada take tanata tada jijiyoyin wuya nikuwa azuciyata ina fadin duk bakin cikinki saina auri kawarki sauri nayi nabar wajan tareda sanyawa araina dole gobe zani wajanki Allah Allah nake washegari tayi domin kawai inje insameki shiri nayi na musamman domin har azuciyata nayi shirin ayita takare kisan ina sanki wata luntsumemiyar mota nagani akofar gida can kuma nahango kina zaune atareda wani akan kujerarki sauri nayi na wuce nashiga gida kina kiran sunana azuciyata ina mayaudariya mezanyi miki kunjinida wautata saikace na furtamata tayarda kuma nakamaki kina zancenki ba a dadeba kika shigo kika rike hannuna kina kanina menayi maka cikin lallabawarki nikuma bakin cikine ya turnikeni saboda kalmar kaninda naji daga bakinki dama shawara zamuyi dakai kaga wancan daya fita cewa yayi yanasona da aure nikuma nafisan rayuwar farin ciki nacemai yabani kwana biyu zan bashi amsa nikuma kaine abokin shawarar da zaka yankewa zuciya abunda take ciki wani dadi naji tareda gyara zaman mugunta domin inyi bayani yadda zan siye zuciyarki tunani mezan fada tagane cewar dani tadace musamman wajan sanyata farin ciki shin fada mata sunana zanfarayi kokuma ince inasanki

bazan iya rasakiba kuma ga dama tazo miki da zakiyi ra

 

Ruwanzuma Hausa Novel 3

 

Tabbas naji dadi musamman ma da kika daukeni abokin shawararki domin hakanma wani matsayine da mutum sai kin yarda zaki sashi a zuciyarki tambayarda nafara mikine da kuma amsarda kika bani yasa naji zuciyata kamar ta buga saboda bakin ciki kina sanshi azuciyarki..?

murmushi kikayi kika gyada kai alamar eh fa ya mamaye zuciyarki jinai kamar na dakko hannu na wanka miki mari kigane yadda naji zafin kalamanki amma sai kika katseni da cewar dukda kina sanshi har yanzu baki gama yarda dashi ba azuciyarki wani farin ciki na shiga tareda cije baki domin nasamu hanyarda zan kwaceshi daga gareki nishawarata bakowa yake zuwa da dankareriyar mota domin zai yaudareki

yawancinsu ta aroce kokuma masu gyaran mota suzo da ita dan su burgeki burinsu wataran tsautsayi yasa kishiga motar sukaiki wani waje su tozartaki wasuma yan yankan kaine zasuzo ahaka kamar mutanen kirki saboda ance dole sai sunnemo kyawawa irinki nikuma gashi banaso narasaki magana nake fada fada kekuma kin nutsu kina kallona kinata mamaki

ban tsayaba nacigaba da cewa irinsune masu shan magani suzo sunata hauka amota su cuci kyawawa irinki suyaudareku kuyi aure bayan anyi kigane mashayine ya cire belt yaita dukanki

baki dakatardaniba saida nagama tsaf sannan kika jiyo da bacin ranki nan nafara tunanin anya acikin maganata banyi wata maganarba kamar ince inasanki katsemin tunanina kikai da sassanyar muryrki dan kanin babartawa kake cewa dan iska ko saboda kaga nayi bakin ciki

to wannan ba irin wadancan bane dan kudinsane motarsace kuma babban malamine dazaisani farin ciki kodan saboda nace banasan abokinka kake so karama inbar farin ciki amma ya kake gani nifa banasan auran ustazannan kuma wai kika kara tambayata abun bkin ciki bansan wace amsa zan bakiba nayi hanyar waje kka biyoni kina bni hkr Kayakuri kaga kainefa zaka bani shawara domin ina jinka kamar wani bangare

2 Comments

Leave a Comment