Hausa Novels

Rayuwar Mace Hausa Novel

hausa novel
Written by Aishat

Rayuwar Mace Hausa Novel

RAYUWAR MACE by Hafsat Rano

Free Page  (1)

Sanye take da hijabi ruwan toka dogo har kafarta, kanta a k’asa sanda zata wuce ta daidai majalisar mazan wadda kullum sai ta bi ta wajen idan zata je islamiyya tana kuma jin yadda suke maganar ta a kullum idan tazo wucewa, tun abin na damun ta har ta iiik ya dake makale a kafadarta ta jingine ta a wajen ta nufi dakin nasa kirjin ta n I’m aw dukan uku-uku.

Shi kadai ne a dakin daga gani ya gama shiryawa fita zai kasuwa, tun bayan da manyan yayanta maza suka taso sai ya zama ba kasafai Abban yake fita ba sai ya dau kwanaki yana gida yana hutawa.

“Sannu da hutawa Abba.”. Tace tana neman waje ta rabe dan ta riga ta san kwanan zancen, ya kwana biyu be mata maganar ba shiyasa ta dan samu nutsuwa a kwanakin.

“Yawwa Asma’u, an dawo!?”

“Eh Abba.”

“Toh Madallah, sannu da dawowa.”

“Yawwa.” Ta amsa a ciki tana sake lankwasa kafarta

“Kina jina ko,akwai wani da yazo ko kuwa har yanzu dai?”

“Babu kowa Abba.” Tace a sanyaye dan tuni har yar karamar kwalla ta soma taruwa a idon ta.

Shiru Abban yayi be tanka ba, tamkar me tunanin abinda zai ce, bayan wasu yan dakiku ya kalle ta sannan yace

“Ko dai kina korar su ne Ma’u?”

Da sauri ta girgiza kai hawayen da take kokarin rikewa suka sakko. Kura mata ido yayi sosai sannan ya soma magana a nutse cikin son kwantar mata da hankali

Kanta a kasa tana jin Abban har ya kai karshe, cikin nutsuwa tayi masa godiya sannan ta mike ta baro dakin zuciyar ta na sake tsinkewa. Idan tace bata damuwa da rashin aure tayi karya. Tafi kowa son ganin tayi auren kamar yadda yake burin duk wasu iyaye da zarar yar su ta kai munzalin aure! Tabbas tasan duk wasu iyaye da yar su ke gaban su basu da kwanciyar hankali har sai sun ga sun aurar da ita gudun magana da abinda ka iya zuwa ya dawo. Amma kuma abu guda da mutane suka kasa ganewa shine, aure, haihuwa da mutuwa duk lokaci ne mutum be isa ya bawa kansa ba idan ba har lokacin ne yayi ba.

Da yan yatsun hannun ta, take kokarin kirga adadin kannenta da akayi wa aure kamar yadda ta saba a kowanne lokaci, ta riga ta san adadin su sai dai kirgawar na sake tabbatar mata da dole ne mahaifin ta ya dinga tunasar da ita a kowanne lokaci. Duk da shekarun ta ba wai sun ja sosai bane dududu a yanzu ne ta cika shekara ashirin da biyar sai dai yanayin yadda ake musu aure da kananun shekaru ya saka ake ganin ta tsofe a gida. Kannenta biyu da akayi wa aure karshe ,shekarar su sha bakwai dan haka idan zaa hada su da me shekara ashirin da biyar toh fa tabbas dole a dinga yi mata kallon taki aure.

Bata san kalar matsalar ta ba, dan ba zata iya tuna lokacin da wani ya tare ta ko a hanya bane. Ta kan zauna tayi ta tunanin ko dai ba zata taba aure ba a rayuwar ta? Kila bata da rabo shiyasa hakan ta kasance dan bata zargin kowa balle tace ko wani abu akayi mata. Ta bar hakan a matsayin wata jarrabawa ce a gareta wanda take fatan cinye wa.

Daga labulen dakin Ummah tayi, ta leko da kanta tana karantar yanayin ta kafin tace

“Ya kamata a dora girkin rana lokaci yana tafiya kafin yan makaranta su dawo.”

Da toh ta amsa ta mike, ta chanja kayanta zuwa karamar riga da skirt ta saka hula a kanta ta nufi kitchen rik’e da wayar ta a hannu, tana zuwa ta ajiye a saman cabinet ta dora ruwa a babbar tukunya sannan ta fito da kayan miya daga cikin ledar su ta soma gyarawa.

Maganar Abba taji a tsakar gidan nasu yana yiwa Umma magana akan dalilin dawowar sa bayan fitar sa kenan bata jin ma ya bar layin na.

“H pollo upar fa mun hau titi sai ga kiran Yaya Asabe wai gasu nan zuwa gidan da wata muhimmiyar magana, dole nace ya juyo my dawo dan bansan wacce magana ce ba.”

” Gaskiya kam, toh Allah yasa muji alkhair”

Umma tace tana bin bayan sa suka shiga falo. Daina aikin gabanta tayi ranta na sake jagulewa jin Hajiya Mama zata zo, Itace mutum ta farko da abban su yake jin maganarta fiye da ta kowa a duniya, duk wani abu da tace masa toh fa an gama shi, ko da kuwa baya so zai amsa mata. Su biyu iyayen su suka haifa itace kuma take masa role din uwa dan tun yana karami iyayensu suka rasu suka barsu su biyu.

Turo gate din gidan yayi daidai da tsayawar bugun zuciyar ta, ta window din kitchen din da hange su suna shigowa ita da shi yana rik’e da handbag dinta ya makala ta a kafadar sa kamar wani mace. Daf da zasu karaso wajen kitchen din tayi saurin dukawa saboda kar su ganta, tana jin sanda Umma ta fito tana musu sannu da zuwa Abba na tsaye daga bakin falon sa fuskar sa na nuna jin dadin ganin Yayar tashi.

“Sannun ku da zuwa.” Abba da Umma suka dinga jera musu har suka dangana da falon sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta cigaba da aikin ta a nutse.

Tana cikin aikin wayar ta dake sama tayi kara, ta dauraye hannun ta a sink ta jawota tana kallon wayar, kawarta ce Safiyya take kiranta, ta daga tana saka wayar a handsfree ta ajiye ta suka koma magana.

Maganar da yaji ya sakashi dawowa da baya zuwa kitchen din, ya tsaya daga kofar yana kare wa halittar ta kallo wadda take sanye da dogon skirt da riga. Motsi taji, ta waigo sai kawai taga mutum tsaye a bayan ta har ya iso daf da ita yana kokarin taba ta.

“Lafiya!?” Tace tana matsawa da sauri har tana neman gogar tukunyar miyar dake saman gas din.

“Fine Baby, kin hadu.” Yace cikin muryar sa ta yan duniya, kallon sa tayi daga sama har kasa, zuwa kunnensa dake sanye da dankunne sai wani jibgegen takalmi da yake jibge a kafar sa, wandon sa irin wanda yake a yagen nan ne ta tsakiya sai askin kansa da ya kara nuna mata ainihin shi din waye.

Yaya Adam ne, tilon namiji a yaran Hajiya Mama kuma shalelenta, tun suna yara Allah be hada jinin ta da nasa ba dan ko haduwa akayi sai yaci zalinta, ya zage ta yace mata shegiya baka saboda duk yan uwanta sun fita hasken fata. Hannun sa taji a saman fuskar ta yana shafawa, tayi saurin bige shi tana watsa masa mugun kallo.

“Menene haka Malam!?”

“Comman sai kace wadda bata waye ba, kin ganki kuwa!? Haka kika chanja kamar bake ba.”

Hararar sa tayi tana sake matsawa baya, dan bata masa kallon me cikakken hankali ko a da ma, balle yanzu da yaje yayi rayuwar turai idon sa ya kara budewa.

Hayaniyar dawowar yaran daga school ya bata damar zamewa ta bar kitchen din tayi saurin zuwa daki ta dauko hijab din ta, ta saka sannan ta koma kitchen din, amma sai daga baya nan, tayi kwafa ta cigaba da aikin ta da sauri sauri karma ya dawo ya sake samunta dan ta lura bashi da kunya sam.

Fasa fita yayi wajen ya koma falon da ya baro su Abba yana zuwa zai shiga yaji Hajiya Mama na tambayar Abba akan maganar Asma’u ko har yanzu shiru, amsar da Abban ya bayar ya sakashi saurin fadawa dakin

“Uncle ni zan aureta.”

Duk suka bishi da kallo,

“Boy me kace?” Hajiya Mama tace fuskar ta kamar gonar auduga

“Yess Mom…”

Kallon Abba tayi, wanda shima yake kallon ta a daidai lokacin

“Kaji wani abun almara, Ashe Adam ne mijin shiyasa aka ta fama, kai Alhamdulillah nayi farin ciki sosai.”

Saurin sakin fuskar sa abba yayi duk da be san yadda zai misalta abinda yake ji a lokacin ba, farin ciki ko akasin sa? A zahiri babu abinda yafi so da ji kamar ace Ma’un sa ta samu miji, sai dai kuma be zaci haka ba, sannan be taba kawo mutum kamar Adam din a irin mijin da yake mata shaawa ba, amma kuma ta Yaya zai ki jinin Yaya Asabe!? Matar da ta so shi tamkar yadda uwa ke son dan ta?

“Alhamdulillah!.” Ya samu kansa da furtawa yana gida kansa duk da be ji abinda Yaya Asaben tace ba. Umma da ta kusan sakin abinda yake hannun ta sanda taji maganar ce ta karaso ta zauna tana kallon Abban amma sam yaki yarda su hada ido ma balle ya gane abinda take so ta nusar dashi.

“Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya.”

“Amin Ahmadu, sai a saka lokacin kad’an tunda dama abinda muke jira kenan, kaji al’amarin Allah, babu yadda banyi da shi ba akan ya fitar da matar aure tunda ya dawo yaki ashe ashe dai matar sa na nan tana jiran sa.”

“Haka dama al’amarin Allah yake.” Abban ya amsa cikin yak’e, sai ta waiga wajen da Umma ke zaune tace.

“Sai a fara shirye shirye kawai bilkisu, bari mu wuce dan tun a yau zan fara shiri auren yara ba.

“Haka ne. ”

Tace itama tana yak’en wanda sarai Hajiya Maman ta ga yadda dukkn su maganar ta dake su amma ya zatayi? Dole ta so abinda danta yake so duk kuwa da bashi ta nagartar da za’a bashi mace amma ai hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar dole sune zasu rufa mata asiri.

Duk abinda ake Adam na zaune a wajen sai da Hajiya Maman tace ya tashi su tafi sannan ya mike ransa fes yana haskilo irin hutuwar da zai da yarinyar dan ba k’aramar mace bace.

A harabar tsakar gidan ya tsaya yana sosa keya umma da ta rakosu ta kalle shi tana karewa shigar sa kallo cikin takaici

 

“Mah please bari na dan sake ganin ta, zan same ku a mota.”

 

Dariya ta saka ta kai masa duka ya goce,

 

“Mara kunya, tana ina ne bata zo ta gaishe mu ba ma ko bata ji shigowar mu bane?”

 

Katse Maman yayi yace

 

“Ke da zata zo gidan ki gaba daya mah!”

 

“Auw kareta kake kenan, toh ai shikenan.” Tace tana cigaba da tafiya

 

“Muna jiran ka a mota.” Tace sanda sukayi sallama da Umma ta fita ita kuma ta shigo, ta tarar dashi a tsaye a inda suka barshi.

 

“Bari a kirawo ta.” Tace sannan tayi gaba, yayi saurin bin bayanta ganin ta nufi daki, tana shiga shima yana shiga Asma’u dake kwance ta mike da sauri, kafin tayi magana ta hangi mutum a bayan umman yana zuro kansa yana kokarin shigowa dakin da dukkan karfin sa.

 

“Kar a shigo!” Tace da karaji ya tsaya cikin jin tsoro, sai a sannan umma ta san ya biyo ta, ta juya da sauri mamakin rashin kunyar sa na neman kai ta kasa

 

“Kaje falo zata zo.” Kawai tace masa cikin takaici, ya juya ba dan ya so ba, ya fita yana taku dai-dai. Girgiza kai Umma tayi cikin tsananin bacin rai tace

 

“Ki je wajen sa a falo bari na samu Abban ku, jinkirin aure ai ba hauka bane da za’a dauki wannan mara tarbiyar a baki, ba zan yarda ba.”

 

Sam bata fuskanci in da maganganun  Umman suka dosa ba.

 

“Umma!”

 

“Kiyi abinda nace kawai ba sai ya sake dawowa ba, ki rik’e Areef ku je tare karki je ke kadai.”

 

Daga haka ta juya da sauri ta nufi wajen Abban dan a san wacce za’a yi, ta dade da sanin Hajiya Maman bata santa,amma bata san rashin son ya kai haka ba!

 

 

 

Rayuwar mace cike take da kalubale mabanbanta! Kaddara ce tsanin duk wata nasarar ta! Ba zata ce ita din rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale cike da rayuwar tata, wanda a karshe zata kirasu da matakin dukkan nasarar ta!

 

 

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

 

 

 

*RAYUWAR MACE*

_Hafsat Rano_

Free Page  (2)

 

***

A kofar dakin Umma ta tarar dashi, ta nuna masa falon da hannu sannan ta wuce falon Abban. Yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin tana shigowa ya bi ta da ido dan yasan abinda ya kawo ta.

 

“Alhaji..”

 

Da sauri ya dakatar da

 

“Maganar ba zata chanja komai ba, muyi mata addu’a kawai bamu san me Allah ya tsara ba.”

 

“Amma dai hakkin mu ne mu nema mata miji na gari, wanda muka yarda da addininsa da nagartar sa, amma Adam fa? Ya cika wannan sharadin?”

 

Zama yayi a nutse bayan ya cire babbar rigar jikin sa da hula sannan yace

 

” Mu bar wa Allah komai, ya fimu sanin komai akai, ba zan taba iya hana Yaya Asabe abinda take so ba, ba kuma zan taba kin danta wai don munin halin sa, ni ma ban fi karfin Allah ya jarraba ni da irin sa ba.”

 

” Yanzu shikenan muna ji muna gani saboda kawai muna so yar mu tayi aure za muyi mata zabin tumun dare!?”

 

” Idan da rabo sai kiga ta dalilin ta Allah ya shirye shi, sai tayi kokari ta sauya masa DABI’AR sa tunda mace tana da matukar tasiri a rayuwar namiji.”

 

Wani abu ne yazo ya tokare wuyan Umman, bata tare da masu ganin cewa mace zata iya gyara wa namiji Hali bayan ta same shi da girman sa, kawai idan kaji an ce haka toh fa lallai an shirya zalintar macen. Tana tsaye ya zo zai fita daga falon, ya kalle ta yana gyara hular kansa sannan yace

 

” Karki nuna mata wani abu da zai sa taki auren, muyi mata addu’a kawai dan babu abinda zai sa a fasa sai dai idan Yaya Asaben da kanta tace sun fasa, amma muddin bata ce ba, toh babu makawa sai anyi.”

 

Kasa tanka masa tayi har ya fice, ta zauna dabas a wajen tana jin da gaske an cuce ta, ta kuma tabbatar da biyu Hajiya Maman tayi dan ta nuna mata ta isa da Abban da ma duk wani abu da ya dangance shi.

Da k’yar ta mike daga wajen ta fito bayan ta jawo masa falon, ta isa dakin Asma’un ta tarar da ita tana sallar azahar, sai kawai ta wuce dakin ta domin ta gabatar da tata sallar.

Tana idarwa Asma’un na shigowa, bata ce komai ba ta hau gadon umman ta kwanta rigingine tayi shiru tana tuna abinda ya faru bayan taje wajen sa. Kadan ya rage be rungume ta ba da ta shigo, ya hau surutan da ta kasa gane komai akai, haka ya karaci babatunsa ya tafi bayan yace mata zai dawo da daddare.

 

“Umma wai me ya faru?”

 

“Aina da?”

 

“Ya Adam, ban gane ba wallahi. ”

 

” Kinsan kowanne bawa da yadda Allah yake kaddaro masa rayuwar sa, sannan duk dan ta yayi ma iyayen sa biyayya toh fa ba zai taba tabewa ba, mahaifin ki ya yanke shawarar aura miki dan uwanki Adam… ”

 

A yadda ta mike daga kwancen sai da ta bawa umman tausayi,

 

” Umma Adam kuma? ”

 

Kai ta daga mata

 

” Innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma wallahi tallahi bana son shi, bashi da hali me kyau wallahi Umma, wallahi Allah bana son shi dan Allah Abba yayi hakuri. ”

 

Duk ta gigice ta rikice, hawayen da Umman take ta rikewa ne suka soma saukowa tayi saurin maida su tana karfafar kanta.

 

” Menene haka? Me kike haka? Ashe ba zaki iya yiwa mahaifin ki biyayya ba?”

 

” Umma Adam fa? Umma dan Allah kice yayi hakuri wallahi ba zan iya ba. ”

 

Wani kallo umma ta watsa mata

 

” Ki nutsu ki saurare ni, kinsan waye mahaifin ku, kin kuma san wacece Hajiya Mama a wajen sa, kukan ki da magiyar ki ba zasu taba sauya masa abinda yayi niyya ba sai dai idan su suka ce sun fasa, dan haka ba ruwana wallahi, ba zan bari ki hadu da fushin mahaifin ki ba, kiyi masa biyayya ku rabu lafiya nima na rabu da nawa lafiya, kuma in sha Allah zaki ga ribar biyayya. ”

 

Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta fice ta bar ta a dakin tana jin yadda take kuka wiwi, wayar ta ta dauka ta kira babbar ‘yarta hadiza ta sanar da ita komai sannan ta kira sauran yan uwan Asma’un da sukayi aure, kafin kace me sai gasu a gidan gaba dayan su, duk kansu kowa be ji dadin labarin ba, amma kuma sai Umma ta hana su fuskar da zasu kushe abun dan ta riga tasan halin Abban su sarai zai iya saba musu akan maganar, sannan tunda tasan babu fashi gwara kawai tayi kokarin ganin basu bawa Asma’un kofar da zata bijire wa mahaifin nasu ba.

Lallashi da ban baki suka dinga yi mata har suka samu ta dan nutsu amma bata bar kuka ba. A haka Abban da yan mazan suka dawo suka tarar dasu, Abban ya danyi fadan dalilin zuwan su haka sai suka ce ai zuwa sukayi su gaishe su, ya ji su ne kawai amma ya riga ya san umma ce ta kira su akan maganar.

Bayan sallar magriba Yaya hadiza ta samu Abban da maganar, ya nuna mata babu fashi su dai kawai su tayata da addu’a, haka ta baro dakin jikin ta a sanyaye bayan ta roke shi ya barta su tafi da Asma’un ya amince amma iya sati daya kawai dan sati uku ya saka bikin tunda babu wani shiri da za’a yi dan kowanne bangare a shirye suke dama.

Mijinta ne yazo ya dauke su wajen tara, a hanya take bashi labarin abinda ya faru, ya dan juyo yana sake bawa Asma’un baki yana tsokanar ta, ta dan yi murmushi kawai amma ita kadai ta san yadda take ji a ranta.

 

***Washegari bayan an makaranta sun tafi umma ta shirya Abbati ya kaita chan Mandawari gidan su ta samu Hajiyar su da maganar auren Asma’un da lokacin da Abban ya saka, duk basu ji dadin hukuncin Abban ba, da kuma rashin bawa Asma’un dama ta fadi ra’ayin ta dan kawai ana ganin kamar ko an barta ma ba wani ne zaizo neman auren nata ba.

 

“Toh yanzu dai ya riga ya gama yanke hukunci, namu kawai shine mu bi ta da addu’a, Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina.”

 

Hajiyan tace bayan sun gama magana da Umman.

 

“Amin, ni na rasa ta ina zan fara ba, sai a aika su miko su sanar da su umman Asiya da su Aunty Falila da gidajen su kawo muntari.”

 

“Eh yana shigowa zan aika shi, sati uku kamar yau ne ai, duk sai a sanar da dangi, Allah ya basu zaman lafiya.”

 

“Amin.” Tace a sanyaye.

 

***Bangaren gidan Hajiya Mama shiri take na ban mamaki, tuni zancen ya karade dangin su bangaren Abban da kuma bangaren Baban su Adam din, mutane da yawa suna tausayawa Asma’un saboda dai sam babu hali na nagarta da zai saka ka dauki yar ka, ka bawa Adam din, ciki kuwa har da yan uwa makusantan su Abban dan wani kawun su sai da yayi wa Abban magana kasancewar kowa ya riga ya san nutsuwa da kamala irin ta Asma’un dan kaf yan uwanta babu kamarta, duk da su ma basu da matsala amma kuma ita din daban ce, magana da koman ta a nutse take yin sa, bata da rawar kan yan mata dan ba zaka taba tunanin ta je jami’a ba ma, bata dauki duniyar da zafi ba haka kuma bata da son kyale kyalen duniya. Haka ya saka mutane suke ganin kamar akwai zalunci a dauke ta a hada ta da Adam wanda ake tunani hatta giya yana sha bayan mugun halin sa na neman mata da yayi shura akai, amma yadda Abban yayi biris da duk wannan ya saka kowa ya shafa ma kansa lafiya aka shiga bin su da addu’ar fatan alkhairi.

 

Zuwan Adam din uku tare da zugar abokai baya samun ta karshe dai ranar da yazo ya tarar da Abban nan yake gayawa Abba ai yazo baya samun ta, nan fa Abban ya shiga dakin Umma yayi ta mata fad’a sannan ya dauki waya ya kira Yaya hadizan yace ya fasa sati dayan gobe gobe ta dawo gida. Jiki a sanyaye ta amsa masa da toh, bayan ya kashe sai kuma yaga kamar ya zafafa da yawa, sai ya sake kiranta yace ta kyale ta zuwa satin amma zatayi bako gashi nan zaizo yanzo. Nan ma dai toh din tace ya kashe ya koma ya samu Adam din ya yi masa kwantancen gidan Yaya Hadizan sannan ya bashi number wayar Asma’un da ta Yaya Hadizan yace idan yaje ya kira. Bakin sa tamkar gonar auduga ya karba suka dauki hanyar gidan Yaya Hadizan baka jin komai a motar sa ife ifen su irin ma gogaggun yan duniya, burin sa kawai ya nuna musu kalar matar da zai aura ya san ba karamin taya shi farin ciki zasuyi ba, hutu kam zai huta a wajen sosai, yadda yake ji ma kamar sati ukun yayi masa mugun yawa amma haka zai hakura ya lallaba ya cigaba da maneji da su Fido kafin ranar da zai gwangwaje.

 

Gidan bashi da wahala suna zuwa suka gane, ya dauko wayar sa zai yi kira sai kuma ya fasa ya fito da kafar sa ya karasa gate din gidan ya kwankwasa da dan karfi saboda karar Gen, be jima yana bugun ba mijin Ya Hadizan yazo ya bud’e masa, ya bashi hannu suka gaisa sannan yace ya shigo ciki

 

“Owk tare muke da guys suna mota bari nayi musu magana.”

 

“Owk.” Yace ya wuce ciki ya bar musu kofar a bude, ya samu falon ba kowa an gama jera ruwa da lemo akan dan centre table din, ya dauki remote ya rage volume din tv daidai lokacin da suke shigowa, su hudu ne dukkan su sanye da kananan kaya daya ma daga ciki wandon sa da kad’an yafi guiwar sa, askin kansu kuwa kai kace gobara akayi a wani gefen kan nasu babu kyaun gani, hannu ya basu suka gaisa sannan ya wuce ciki cike da al’ajabin dalilin da zai sa Abba amincewa bayan ya san waye Abban da nagartar sa.

Da k’yar da ban baki Ya Hadiza ta sakata fita dan bata son fushin Abba akanta zai iya hadasu daga ita har Asma’un yayi musu tatas. Hijabi ne burmeme a jikinta har kasa, ta dauko facemasks ta dora akan fuskar ta sannan ta tura kofar falon kanta a k’asa ta shiga. Wata iriyar kunya ce ta kama Adam din da ya ganta da shigar, shi da yaso suga kalar matar da zai aura amma shine zata je ta burma uban hijabi kamar wadda zata zaman makoki.

Dariyar shakiyanci suka fara yi suna kallon sa, ya hade rai sosai yaki kallon ta, a k’asa chan ta rakube ta gaishe su suka amsa cikin dariya dan su basu ga  abinda yake ta musu kozozoto akai ba.

 

“Our wife kina lafiya?”

 

Daya daga ciki yace yana kunshe dariyar sa.

 

“Lafiya lou.”

 

Ta amsa a takaice kanta still a k’asa ba zata iya cewa ga adadin su bama balle kamar su, uban gayyar kawai ta gani sanda ta shigo taga ya wani diririce kamar wanda yayi karya aka gano shi, bata kuma kallon sa ba ta zauna. Tana jin su suna ta shakiyan ci suna tsokanarshi amma ko uffan be ce musu ba, sai da suka gama suka fita, ya taso yazo daidai kanta, ya saka hannu ya fuzge facemask din, ta kalle shi da sauri

 

“Wannan wane irin wulakanci ne na kawo guys dina su ga matar da zan aura shine zaki sako wannan buhun sannan ki wani toshe fuskar ki dan tsabar iskanci.”

 

“Kamar ya? Me yasa zasu ganni ko su din muharramaina ne?”

 

“Shit! A 21th century dama akwai mata villagers irin ki? Ke baki san civilization ba? Ko baki ga alamar mijin da zaki aura wayayye bane?”

 

“Ban san duk wannan ba, abu daya na sani shine abinda addinin musulunci ya koyar dani.”

 

Ta murguda masa baki tana jan facemask din zata mayar ya fuzge da karfi sannan ya buge mata baki

 

“Karki yarda kice zaki min rashin kunya wallahi, dan zan taimaka miki na aure ki, naga ma ai neman kai ake dake na taimaka nace zan aura, so watch your mouth wallahi, kuma na sake zuwa kika zumbulo min irin wannan Hijab din sai na cire shi ta karfi wallahi. Nonsense!”

 

Ya juya da sauri ya bar falon har da buga kofa, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, bakin ta da ya buge na mata zafi sosai, sai kuma maganganun sa da suka yi mata mugun ciwo, da gaske taimaka mata yayi? Kuma neman kai ake da ita shine ya tausaya mata zai aure ta. Wani kuka ne yazo mata, ta gwammace ta mutu ba aure akan ta auri mutum irin Adam, jinkirin aure ai ba shine zai saka mutum yayi wrong choice ba, gwara ma ace ka aura baka sani ba, amma wannan kowa ya san halin sa.

Ta jima a wajen tana kuka sosai, kafin ta tashi da k’yar bayan ta goge hawayen ta shiga ciki.

KARANTA: FURAR Danko Hausa Novel Complete

1 Comment

Leave a Comment