Hausa Novels

FURAR Danko Hausa Novel Complete

hausa novel
Written by Aishat

FURAR Danko Hausa Novel Complete

‘…..

          

1

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*

_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

……..Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuƙar ɗauki ƙafar tata musamman da wandon ya kasance baije ƙasa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarƙar ƙafarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ɗar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara’a, sannan babu kwalliya ko ɗigo idan ka cire ɗan lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laɓɓanta. A kallo ɗaya zaka ɗauka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ƙabilar kudancin ƙasar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ƙasar musamman inda addinin Muslunci keda ƙarfi irin su kano.
A hankali taja ƙaramin tsaki dai-dai tana miƙewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ɗin kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ɓare ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaɗan harara, tun ɗazun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ɗinta ta fisga ta ɗora a kafaɗa ɗaya sannan ta ɗauka Apple laptop ɗin ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miƙe tai ficewarta cikin takunta na ƴammata marasa jin magana..

          Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ƴammatan kuwa kishine ya lulluɓesu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baƙar fata haihuwar Africa sai dai ɗabi’u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ƙamshi da duk wanda ke a kusa da ita kaɗan dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ɗinta a taunar chewing gum ɗin bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ɗaya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH…
*_Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ƙamshi_ ƙyaƙyƙyawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Itace ɗiya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma’il l. Jiƙamshi. Babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiƙamshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma’il Ibrahim Jiƙamshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiƙamshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanɗararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ƙamshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ɗin su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ɗin lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ƙyar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ɗaya karatunta a ƙasar ƙetare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ɓangaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ƙamshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ɗan uban waye a kuɗi ko nasabar zuri’a baka ishi Lulu ƙamshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaɗi tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ɗan taɓa samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuɓuta da ƙyar.

     Wannan itace Mawaddat Isma’il Jiƙamshi (Lulu ƙamshi) a taƙaice.

         Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauƙi da yanga. Wannan ita kaɗai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ɗaga murya wajen faɗin,
_“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._
Ɓuɗaɗɗiyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ɗin wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ƙoƙarin cimmata ƴammatan da duk suka juya garesa suka shiga taɓe baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ƙoƙarin cimmata da yake yi dai-dai tana ƙoƙarin isa ga inda motocin ɗaukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.
Fuska ya marairaice yana mai haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faɗin, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ɗaya ne Please. Address ko phone number abeg you”.
Cike da yauƙi da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.
Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ƙasashen Africa ya sansh…..”
“Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ɗin nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faɗa cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaƙa domin tarihi haka yay tsaye ƙiƙam yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko’a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ɗauki wani mataki…..

       “Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ɗin nan”.
Wani ɗan ƙyaƙyƙyawan yaro dake saman jibgegiyar mota baƙa siɗik ya faɗa yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ƙasa da keypad waya ƙirar Nokia a hanunsa ya ɗago a hankali tamkar mai ciwon wuya………

2️

……..Ƙyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara’a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya ɗaga shi cak ya sauke ƙasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu.
A hankali ta saki murmushi daya ƙara ƙawata ƙyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya ƙaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop ɗinta a saman akwatin dake ɗayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya ƙaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin ɓacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaƙanci. A fusace ta furta, “Halan kai babu zuciya a ƙirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy”.
_(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faɗawa ba. A hankali ya ɗago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai ɗauke da farce data ƙara a duk farautan hannuwan nata biyu da ƙafafu. Ɗauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baƙin ciki na tokare ƙirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har ƙasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu.
Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faɗin, “Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaƙantaka a wajen nan, mafi munin wulaƙanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANƘO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok”. Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top ɗin ta tai gaba batare data ja akwatin ba.
Babu alamar gargaɗin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ƙugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danƙo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haɗiye yana lumshe idanunsa da suka wani ƙanƙance tare da lashe lips ɗinsa.
A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ƙasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.
Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baƙin cikine ya sake turniƙe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ɗauke mun kai? kan bala’i…..!”
Da sauri yaron ya katseta da faɗin, “Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem…..”
“Kai dalla yimun shiru. Shi ɗin waye da baza’a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma”.
Ƙwal-ƙwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart ɗin da ya ɗauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buɗe motar ya shige abinsa, da wani irin ƙarfi ya fisgeta yay reverse ɗin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya ɓace da ga wajen yay hanyar fita airport ɗin baki ɗaya..

        Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin ƙarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy ɗin ya haɗu iya haɗuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform ɗin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaɓa mata baƙar magana musamman ganin wulaƙancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard ɗinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai.
Lulu da gaba ɗaya ta koma butum butumi da wulaƙancin driver ɗin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan ɓacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security ɗinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taɓa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da ƙyar ya iya furta, “Please calm down Babie…”
“Anƙi ai Calming down ɗin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy ɗin mai aikin tuƙi a gidanmu ƙarƙashin ikona zaima wannan walaƙancin? Mi yake taƙama da shi….?” Da sauri yaron nan yace, “To Aunty Lu bana faɗa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa…” Hannu ta ɗaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faɗin, “Please Babie karki aikata haka”. Idanu ta rumtse da masifar ƙarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baƙin ciki da tuƙuƙin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ƙoƙarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haƙura cikin bodyguard ɗin sa yay mata kiran ɗaya daga cikin taxi ɗin dake wajen da dama su aikinsu ɗaukar manyan mutanen. Nanma ƙin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roƙonta sannan. Kuɗin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin ɗar-ɗar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. “Hajiya ina zamuje…?”
“Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu”.
“ALLAH ya baki haƙuri”.
Mai taxi ya faɗa yana kunna mota……..

Kai kai wannan yarinya ta cika jaraba. Anya zan iya kuwa? Bara dai muga ko zamu iya cigaba da bin al’amarinta. Nasan dai Uncle Smart ya higa uku yau.

O 3️

……..Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ɗin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ɗin ya dubesa. Komai a gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ɗin. “Ranka ya daɗe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ƙamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ɗin ba. Kamarka ma ɗan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.
Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faɗamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.
Cikin rashin damuwa saurayin ya faɗa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ƙamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buɗe masa fuskarsa ƙawace da murmushi……

         *_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ɗan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ɗan kasuwa ne da kuɗi ke kaɗa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaɗar marasa ji na ƴaƴan manyar ƙasar sune ɓoyayyun limamai. Manemin mata ne ƙwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziƙi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko’ina yake yarda ya nuna halinsa mara ƙyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ƙaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai….

   Wannan kenan.

     ∆••••••∆ ★ ∆•••••∆

          Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma’aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma’aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu’a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu’ar tasu bata amsu ba dan gata ta dawo ɗin a bazata.
Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
“To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, “Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?…”
Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
“Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma’aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan…”.
Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ƙyawun fuskar tasa ne inaga ke ruɗarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!…..” Ta ƙarasa maganar a hankali cikin ƴar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya ɗakkokin ba?”.
“Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faɗa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ɗin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.
Cikin sauri dattijon ya miƙe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haƙuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ɗauki matakin dan bazan taɓa zama da wanda zai saɓa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ɓata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ɗin Daddynta yanzu zan nema Yousef ɗin ma ya dakatar da shi”.
Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ɗin, sauran yaran duk sai suka shiga taɓe baki. Hakama mamansu tsaki ta ɗan ja a hankali tama miƙe tabar falon. Shiko Daddy ko’a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haƙuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ƴar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaɗan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaɗarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaƙin yaƙin duniya, sai kuma zuwa can ta ɗan ɗago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ɗin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.
“Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.
“Thanks you sweet Papa..”
Ta faɗa tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miƙe, yatsu biyu ta ɗaya masa alamar bye ta nufi ɗakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ɓacema ganinsa. Bata zauna a ƙayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haɗaɗɗen gaske kuma ƙato. Dan bayan ƙaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ɗakin ya haɗu tare da amsa sunansa ɗaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faɗa da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a ɗakin da baki gama min ba har na shigo….?”
“A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma’aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ƙyau har jikin bangon da kikace”.
Kakkauran tsaki ta ƙara ja da ƙarasa shiga ɗakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ƙyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faɗa ta kwanta tana mai wargaza fillos ɗin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buɗe, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haɗamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ƙazamiya sai wani tsamin zufa kike”……..✍️

          ‘…..!!

          

4️⃣

……..Idanun dattijuwar cike da ƙwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ɗaga ƙafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma itafa da sauƙi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ɗaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ɗin ɗakin ita kaɗai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ƙamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki ƴarnan” ta faɗa cikin tausasawa tana ɗauke ƴar ƙwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaƙancin da Lulu ke mata tana ƙyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ƴaƴanta dake ƙauye da ƴan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, da2 in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ɗin ne ya ɗan fi cin nasararta, dan shi har faɗa yakan ɗan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ɗin bane ba….

  Wannan kenan

         ∆•••••∆ ★ ∆•••••∆

     Da ga airport babban kamfanin Jiƙamshi’s ya nufa ransa a ɓace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa’ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ƙara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ɗin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ɗan rubutu ya haɗa da key ɗin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ɗan taɓe baki…

      Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika’il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da’ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace…..
“Ɗan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..

       *_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika’il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al’amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana’a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al’amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika’il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu………

Karanta: Abban Sojoji Takun Karshe Complete

2 Comments

Leave a Comment