Hausa Novels

Abban Sojoji Takun Karshe Complete

hausa novel
Written by Aishat

Abban Sojoji Takun Karshe Complete

Zagayeta su kayi gaba ayansusu jahad na ambatar sunantafawan ne ya auko masu ruwa a fridge ya dawo ya mia ma uncle insukar6a yayi tare da bue murfin ya ebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskartanan take ta farka tana faman yin atishawaAlhamdulillah suka shiga fai suna kallontayunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo aya bayan aya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido.

Muryarta na rawa tacejajjahad hossanaku neko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba.

Ba aramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane suatare suka faa jikinta suka rungume juna suna kuka.

Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaae ba ma fuskar kowannansu na auke da murmushimusamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a asa yashahaka hajiya azeemarsu har cewa take yiyanzu nan waannan an ukun duka namu neaan mu neAllah abun godiyayau dole in yi nafilar dare don mia godiyata ga Allah SWA daya nuna mun aan abusufyan inmu da ranmu kuma da lafiyarmuAshe dae da rabon yara suga danginsubayin Allah sun sha wahalar rayuwaamma bakomai har yanzu lokaci bai ure mana bazamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarkuZamu baku duk wani jin dai na duniya da kuka rasazamu gatanta kusai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani unci da kuka ta6a fuskanta arayuwarkuwaanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun anani kuarsu sai sunji dama baa halicce su cikin duniyar nan ba

Abbansu junaid ya kar6e da cewaAe daga rana irin ta yau su fara irgen kwanakin mutuwarsusaboda arshen su yazosun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEINWallahi thumma tallahi aya daga cikinsu bazai sha ba ranshi amatuar 6ace yayi maganar

Abbas yaceAbba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosaisuna buatar hutuin yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai

Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka

Gyaran murya ya an yi masuatare suka ago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye

Kuyi kuka yara bazan hanaku badole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarkuan zalunce kuan untata makuan rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginkuduk akan laifin da baku kuka aikata basaboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu auki fansar su sae akan waannan bayin Allahn  Shiru ya anyi yana faman sauke ajiyar zuciya
abusufyan na zuunne akusa dasu ya sunnar da kanshi asahakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga

Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waanda aka zare ma lakkalokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu
duk wannan abun dake faruwa gwaggon katsinana zaune saman kujera tana ta faman matsar kwallahar lokacin bata daina tsinar dangin Sayyadi baharis sai faman lallashinta yake yi tana buge mashi hannu tana fainka rabu dani Harisuabun da ciwo wlhZuciyata tafarfasa takeyiaan abusufyan ina aka wulaanta kamar dabbobiwlh bazan ta6a daina tsinewa Sayyadi bamunafuki algungumi an wutaYa Allah ka tsine ma sayyadi da duk zuriyarshi harda unguwar zomar da ta yanke mashi cibinshi Ya Allah kayi mana maganinsuSayyadi ko an iskauwarshi ta haifa mana masifamunafuki lokacin da yake zuwa wurin abu har asa yake zukunnawa ya gaishe Nida wata guntuwar jallabiyarshi ta gadoafafun nan nashi kaman shebur sanye cikin silifar an ta shegiyaMuna yi mashi kallon Biri yana yi mana kallon ayaba
sai faman sambatu takeyi abun ba aramin ona mata rai yayi bacan kuma taceAllah sarki abunasan yanzu ta gane cewa Allah aya neyarinyar nan akwai taurin kai kamar kwallon goruba ga kafiyakunnuwan nan nata kamar na Zoman daji falo falo dasuba irin jan kunnan da banyi mata baamma tai ji naAe ga irinta nan yanzu majnun ya koya mata hankali yanzu tana can Saman bola tana sambatu baiwar Allahwama yasan uwa duniyar data shiga

Sehrish ku tashi ku tafi aki ku kwantagobe zamu arasa magana daku Abbansu ne yayi maganar

Miewa sukayi tsaye tare da yi masu sallama sannan suka wuce akin natagaba aya sehrish ta an shiga ruubatasan meya faru baamma bakomai yafi aure mata kai ba face ganinsu hosana da jahadtaya akai suka San inda take har suka zo wurintaabun kamar a mafarki take ganinshi

Atare suka shiga cikin akinanan fa suka tsaya suna kallon juna fuskar kowaccen su auke da tsantsar farin ciki mara misaltuwa

Sehrish Ashe da rabon zamu sake ganinki a duniyar nanjahad ce tayi maganar yayin da hawaye ke sauka a fuskarta ta aura da cewa Sehrish munyi kewarki sosaimunyi kukan rashinki atare damumunsha wahala sosai

abubuwa marasa dai sun faru damu bayan rabuwar mu dakeamma duk wani hali da muka shiga hakan baisa mun manta dake ba sehrish kullum kina aranmukoda yaushe muna cikin zullumin a wane hali kikekina raye kuwakina jin dain rayuwarkikina da oshin lpy ko akasin hakan

jin wannan maganar ta Jahad yasa ta fashe da kuka mai cin raijanyota jahad tayi jikinta sosai ta rungumetaitama hosana ta matsa tare da sanya hannayenta ta bayansusuka hae su ukunsun jima a wannan yanayin kafin daga bisani suka haye saman gadon su duka ukun suka zagaye junansu suna fuskantar juna a zaune
Sai lokacin sehrish ta bue bakinta tare da cewainaso ku faamun meya faru na daina samun wayar tsohuwasannan kuma inason jin yadda akai har ku ka san inda nakenayi mamakin yadda na manta daku gaba aya acikin rayuwatanasan ban kyauta maku baAmma kuyi hauri ku yafe mun
ta arasa maganar tare da kai hannunta ta shafo gefen fuskar hosana tana kallonta da idanunta waanda suka canza launi sosaisai lokacin ta gane cewa ashe sune yaran da Marshal Omar ke ruo a wurinshirashin sani yafi dare duhuhar waya suka yi dasu jahad amma bata ganesu basaboda bata acikin hayyacinta
Jahad ce ta kwashe dukkan abunda ya faru tun daga kan Jefa wayar tsohuwa da hosana tayi acikin Masai da kuma mutuwar tsohuwada kuma zamansu acikin cellhauwarsu da Marshal Omarzamansu a wurin gwaggon katsina da kuma rayuwarsu agidan Aunty babbakomai ta sanar mata
Sosai sehrish tayi kuka tamkar ranta zai fitahar zazza6i saida ya lullu6eta nan takebakomai yafi girgiza ta ba face mutuwar tsohuwada kuma zamansu hosana a gidan Aunty babbaabun ba aramin ta6a zuciyarta yayi bawani irin ciwon kai ne ya rufar mata mai raain gaskerarrafawa tayi ta koma gefe guda saman bed mattress in ta kwanta tare da janyo pillow ta rufe fuskarta dashiWurinta su jahad suka koma tare da kwantawa kusa da itakowanannsu na acikin yanayitabbas sunga rayuwa

Dayar bacci 6arawo ya sace suamma fa dukkansu babu wanda babu zazza6i ajikinshi

Kowa fa ya manta da cikinshi saboda lamarin su hosanaa gidan babu wanda yaci abincin daren shisaboda unci da takaicin yadda rayuwar aan uncle insu ta kasance

Lokacin da Azmee ta turo opar akin nasu samun su tayi kwance suna bacci kowacce fuskarta auke da hawayebacci sukeyi amma hawayen basu daina zuba daga idanunsu baba aramin tausayinsu taji bata jima tana kallonsu kafin ta rufe masu opar ta koma bedroom inta

Kwance yake asaman katafaren gadonshitunda ya dawo bedroom inshiya shiga toilet yayi wankaya dawo ya kwanta yana tunanin duniyajuyi kawai yake yi asaman gadon bacci yai aukarshihar lokacin zuciyarshi bata sauka baabun ya dame shi sosaeya tsani zalunci arayuwarshiya tsani mugun mutun mai hali irin na dabbobitabbas idan har sayyadi ya bari ya shigo hannunshi sai ya anani kuarshidaga baya kuma ya dawo yana tunanin wai yanzu ar yarinyar nan da take yi mashi aikiashe ar uwarshi cejinin shiiyar Uncle insuhakan na nufin cewa ita anwarshi ce
Wonders shall neva endya furta hakan tare da lumshe idanunshinan take kuma ya tuna da hoton da Uncle abusufyan ya basu lokacin da suke a Ushakan na nufin cewa Hoton yaran ne ya basu lokacin da suke ananazan tambayi uncle hoton wacece nai selecting acikinsuas I promised then zan taimaketa da kui ta sayi duk abunda takeso bazan fasa ba

Wasu dae sunyi bacci a wannan daren yayin da wasu kuma Baccin ya aurace ma idanunsua tsaye Abusufyan ya kwana idanunshi sun anance saboda raain da yake ji acikin zuciyarshibawan Allahwlh abunda ciwotaya ma zai iya bacciyasha kuka daega wani irin Matsanancin ciwon kai da yake fama dashiyawo yake ta yi acikin dakin yama rasa tunanin da zai yi yayin da tafin hannunshi na dama ke dafe da saitin zuciyarshiwani irin bugawa takeyi mashi mara dai

Yana cikin tsayuwar ne har aka kira sallar asuba bai ankare basae da Yaji ana mashi knocking opamuryarshi ashae yaceWanene
Ni nemuryar Abban su junaid ce
Hakan yasa shi cewaopar abue take yaya ka shigo daga ciki
Tura opar Abba yayi ya shiga ciki yana ganin Abusufyan atsaye yacedama saida rai na ya bani cewar baka yi bacci ba abusufyan
Yayi maganar tare da arasawa ya dafa kafaarshi yana kallon fuskarshi da hawaye suka wanke ta sharkaf
Cikin sanyin murya yaceduk wanda yace maka kayi hauri tamkar ya cuce kaneamma ya zakayi abusufyandole haurin nan shi zakayinasan abun da ciworaainshi na iya zarce na unar wutaabusufyan bazan ce kayi laifi baamma kasan cewa dole ne dama kaga badai dai bakayi aure batare da sanin mahaifiyarka babaka sanar mata ba balle tasanya albarka acikin auren nakukunyi komai a6oye kai da gwaggon katsinasai gashi yau Allah ya bayyana mana komainasan kai kanka kayi mamakin ganin aanka su duka ukun a arashin kulawar gidan mukaan daga cikin Ikon Allah kenankwata kwata yaran basu san suna da dangi bagarari kawai sukeyi a wulaance cikin garimu ma haka bamu son cewa akwai wasu aa waanda suka kasance jinin mu ne su bababu wanda yasan hakaamma cikin ikon Allah da yake shi hakimun nesai gashi silar aikatau aya ta fao hannunmuyayin da silar ciwon aya daga cikinsu da aka kai asibiti Allah ya addara hauwarsu da Omar yayin da shi kuma yaje wurin an uwanshi Dr harislamarin ubangiji girma gare shigaba aya Allah ya haa yaran a wurinmu ta hanyar da bamu ta6a tsammani bakamar yadda kai da gwaggon katsina baku yi tsammanin abunda kuka aikata asirrance zai tonu batunda baku sanar mana ba sae gashi Allah ya sanar damusu kansu yaran basu yi tsammanin zasu hau da dangin ubansu na asali basu dama basu da masaniya akan wanine ubansu
Dakatawa abba yayi da maganar yana kallon abusufyan dake ta faman shesshear kuka muryarshi na kerma ya shiga cewaYa Allah ka yafe mun kuskuren dana aikata na auren abu batare da sanin mahaifiyata ba da kuma dangina batun farko nine silar jefa rayuwarsu Cikin halin da suka tsinci kansuda ace ban 6oye ma kowa baduk da ammi bazata barni in auri abu ba amma ina da tabbacin cewar Abbanmu salahuddeen zai aura mun ita inna nasanar mashiiyakaci dae Ammi zata zangwameta ne daga baya kuma nasan zata fara sontawlh ni sam tunanin hakan baizo mani ba a wannan lokacinidona ya makancekuma ba laifin gwaggon katsina baneSon da takeyi mun ne yasa ta aikata hakan don ta faranta mun ganin halin da na shiga a lokacin jin cewar Mommynmu ba zata bari in auri abu bagashi na mutu akan sonta
kaiconafashewa yayi da wani sabon kukandana sani kenan irin wadda baason yintaabun yayi ta maka ciwo azuciyarkashiyasa kullum muke cewa Allah ya tsare mu daga aikata aikin danasanisaboda bai da daiaci gare shi
Ba aramin tausayi yaba Abba batuni shima hawaye suka fara sauka akan fuskarshijanyo abusufyan yayi ajikinshi sosai ya rungume shi yana lallashinshi
A arshe yaceAbusufyan ka manta da duk wani abu daya faru dazunyanzu lokacin farin cikineyakamata ka nuna godiyarka ga Allah subhanahu wata ala daya nuna maka wannan ranar da ya haaka da triplet inka dukkansu da ransu kuma da lafiyarsuwlh abusufyan dana ga yaran nan amatsayin aanka kaan ya hana in buga tsalle saboda murnayayi maganar yayin da suka raba jikinsu dana juna
tallabo fuskarshi abba yayi cike da zolaya yaceKasan me
Abusufyan ya girgiza mashi kai alamar aa
Abba yacenifa azu dana ga ka firgita da ganin yarinyar nan nayi tunanin cewa ko ka yasa nehar ina cewa shikenan lokacin barin gwaurantakar abusufyan yayi aduniya ashe ashe uban ne gaba aya
Ya arasa maganar yana dariyamurmushi abusufyan ya anyi
Abba ya kuma cewaWai yanzu nan duk aikinka ne waannan abusufyanashe dae anin nawa bana wasa bane
fashewa da dariya abusufyan yayi tare da sunnar da kanshi asa
Hakan ba aramin dai yayi ma Abba badama so yake ya sanyashi farin ciki don ya gusar mashi da damuwar da yake ciki
dafa kaarshi abba ya kuma yi tare da cewaduk haihuwata yaya goma sha takwas akan su jahan ne kawai na samu an biyuamma kai da yake mai saa nena ku ba irin namu bane sai gashi ka haifa mana an uku rerasko Ya ammi zata ji in taga aan mara jin maganar nan nata abusufyannasan zata ce shegen bisa zai aika ae
Wannan karan atare suka fashe da dariya
Daga bisani Abusufyan yaceyaya hussein inaso naga yaran nan sosaina damu dasu wlh
Wani irin kallon rainin wayau Abba yayi mashi kafin yaceyau naga ikon Allahni kake fadama kana son ganin aankaYaran nan fa naka ne halak malakae ni nama yi tunanin a wurinsu zaka kwanasaboda suna buatarka sosai atare dasuyanzu basu da burin daya wuce suga mahaifinsu atare dasu
Wani irin dai ne ya lullu6e abusufyan yace
Zan iya zuwa wurinsu yanzu
Abba yaceKa bari mu dawo daga masallaci inyaso kai tsaye kawai sai ka wuce wurinsu
Fuskar shi auke da farin ciki yaceokeybari naje nayi alwala
Abba yacemuna jiranka a main palour in ka kammalaka same mu acan
Yana arasa maganar tashi ya juya tare da nufar opar akin nashi ya fuce tare da tura masa opar
Toilet abusufyan ya shiga batare da 6ata lokaci baya auro alwalar
Lokacin daya fito babban falon anan ya same su kowannansu ka kalla zakaga alamun damuwa a fuskokinsuwasu ma da alama basuyi bacci bamusamman Marshal Omar babu alamar yayi bacci adaren jiyahatta Sgr ma akwai alamun rashin isasshen bacci atattare dashitaya zaiyi bacci sayyadi na yawo acikin garishi fa in ya ullaci mutun irin haka har sai yaga bayanshi sannan yake samun kwanciyar hankalisu twins kuwa fuskokinsu sunyi jawur su da fawankowa dae da damuwa aranshi

Bayan sun kammala hauwa suka wuce masallaci atare

Tura opar akin nasu azmee tayi don ta tashe su sallar asubaba aramin mamaki tayi baganinsu ajere suna sallahkowaccensu na sanye da dogon hijabi a jikinta hijjaban sehrish ne hosana da jahad suka sanyaabun ba aramin burgeta yayi badama indae suna tare su ukunmusamman in akace maka akwai jahad atare dasu tofa basa wasa da ibadaduk da itama Sehrish in ba daga baya baamma jahad in itace kan gabasaboda ita baa tashinta sallar asuba da zarar anfara kiran sallar asuba duk nisan baccin da tayi zata farka ne da kantaabun sama rai ne da kuma sabo da yida kuma imanin mutun

Murmushi kawai azmee ke saki tana kallonsu gwanin ban shaawaaan abusufyanjikokin Ammi da salahuddeeenaan anin Abban sojoji Abusufyananne ga Marshal Da Sgr duk su kaaeabun farin ciki abun murnayanzu su sun zama abunso wlhyayyansu gaba aya sojoji har goma sha takwasko sauro ne yayi gigin Cixon fatar jikinsu sae yaji saukar alburushin bindiga asaman goshin shi

Azmee na tsaye tana kallonsu taji alamun motsin mutun a bayantajin an dafa ta yasa tayi firgit ta an juyaHajiya azeema ce jikinta sanye da hijabi bluehannunta rue da carbifuskar nan auke da murmushi taceNazo ganin aanmu neidan ba damuwa ki bani hanya in wuce ciki
Murmushi azmee tayi tare da matsa mata hanya ta wuce cikisai da ta shiga ciki sannan azmee tabi bayanta tana cewasallah nazo in tashe su suyishi ne na same su ashe har sun tashi maabun ba aramin burgeni yayi ba dana gansu ajere su ukun suna sallah
Murmushi hajiya azeema tayi ayayin da take zama daga gefen gadon su taceAlbishirinkitayi maganar tana kallon azmee
Azmee taceGoro
Fari ko jacike da zolaya tayi maganar
Fari daeshi ne ke tare da alkhairiwannan launin jan alamace ta hatsari
Dariya hajiya azeema tayi kafin taceTab jiya anyi babu keLabari da umi uminsazazzafan gaske
A agare azmee taceMeya faru
A lokacin su jahad sun sallame sallahsuna zaune saman dardumar suna sauraransu
Nuna su hajiya azeema tayi tare da cewaKe wai ashe yaran nan aan abusufyan ne
Gaban azmee ne ya fai Rassssaboda yadda maganar ta dirar mata kai tsaye acikin kunnuwanta
Wai dagasketayi tambayar cike da mamaki
Hajiya azeema tacehmmmm ke dae bariwani iko sai ubangijidagaske fa nakebabu wanda baiyi mamakin wannan abun alajabin bayara dae aan aninmu ne sufyan
Juyawa azmee tayi tana kallonsu sehrish da sukayi zuru suna kallonsu musamman Sehrish da batasan kan zancen basaboda bata a hayyacinta lokacin da akayi maganaramma lokacin da jahad ke bada labarin rayuwarsu taji komai a kunnanta kuma daga nan ne Sihirin jikinta ya lalace saboda tunaninta daya rinjayi kwalwarta harta tariyo dukkan abunda ya faru arayuwarsu ga kuma adduar da Sgr keta yi mata acikin kunne

Cike da mamaki azmee tacetaya akai hakan ya farudama abusufyan ya ta6a aure ne kenan
Ataaice azeema ta bata labarin yadda abusufyan ya auri abu batare da saninsu bahar suka samu aruwar an uku
Wani irin farin cikine ya lullu6e azmee saboda tsabar farin ciki bakinta yai rufuwa
Jahaddagaske ne abunda kunne na ke jiyo munsehrish ce tayi maganar tana kallon jahad da tsananin mamaki
Murmushi jahad tayi ta jinjina mata kai alamar ehta ara da cewarjiya duk baki a hayyacinkiabun farin cikin nan ya faruMun jima muna wahalar rayuwa ashe muna da dangi mai girma irin wannan bamu sani bacikin ikon Allah kuma sai gashi Allah ya haa mu dasu ta hanyar da bamuyi tsammani baina tunanin adduar da muka jima munayi ne Allah ya kar6a manaAshe oumman mu sai da ta fara auren uncle in su abusufyan sannan ta auri wannan fasiin mutumin sayyadida cikinmu ta shiga gidan shi
Arue sehrish tacetaya hakan zai yiwu
Hajiya azeema ce ta katse ta da cewar tabbas zancenta gaskiya ne sehrishku aan aninmu ne Abusufyansai da ya fara auren mahaifiyarku sannan Mugun mutumin nan daya untata rayuwarku ya auretagaba aya hajiya azeema ta kwashe labarin rayuwar mahaifiyarsu agidan gwaggon katsina da kuma hauwarsu da abusufyan har izuwa rabuwar aurensu ta auri sayyadi ta sanar ma Sehrish
tun kan takai arshen labarin nataSehrish tayi sujjadatana shesshear kukasaboda tsabar farin cikiAshe ita iyar uncle insu ce abusufyanhakan na nufin su Babban yaya an uwanta ne na jinihaba no wonder ae shauwar dake tsakaninta da junaid tayi yawakai kana ganin abun zakasan cewar akwai alaa ta jini ajikinsuta damu da mutanen gidan sosaiashe danginta ne su in
Jikin azmee ba aramin sanyi yayi ba bayan hajiya azeema ta sanar mata irin zaluncin da sayyadi yayi ma su Sehrishhar idanunta sai da suka cicciko da kwalla saboda tausayinsu da tajita jima tana tsinar sayyadi acikin zuciyarta
Muryarta tamkar zatayi kuka tacedama ina ta son mu samu lokaci Sehrish ta bani tarihinta wllhashe haka suka sha ukubar rayuwa bayin Allahkai koma wanene wannan mugun mutumin ya cika babban azzalumisaboda tsabar zalunci ya raba yara da mahaifinsu ya kuma untata rayuwarsuduniya ina zaki damuazmee na cikin maganaAbusufyan ya turo opar akin bakinshi auke da sallamagaba aya hankalin su sehrish ya dawo kanshishi ma kuma yana ago idanunshi suka sauka akan an ukun nashikwata kwata ma bai lura da hajiya azeema da kuma azmee dake a akin baSu sehrish kawai yake kallo cike da so da aunako kyaftawa baiyikamar ya haiye su haka yake jikamar yadda yake jinsu haka suma suke jinsusae are mashi kallo suke yi kamar su watsa a guje su rungumo shi haka suka dinga jita wani 6angaren kuwa abun ba aramin yawo yake yi masu akai baWai nan mahaifinsu ne halak malakubansu wanda yayi silar zuwansu duniwadama suna da uba da dangi a duniyatambayoyi iri iri suke shiga yiwa kansu
Ganin sun zubama juna ido tsakanin Abusufyan da kuma su sehrish dake zaune saman darduma suna kallon shihakan yasa hajiya azeema tayi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanta sannan taceZaman me kuke yi nebaku ga mahaifin naku baneba zaku zo ku rungume shi bakuji umin mahaifinku a jikinku
jin wannan maganar ta hajiya azeema yasa su miewa gaba dayansu jiki na rawa suka arasa wurin shi
Tunkan su araso ya bue masu hannayenshi alamar su shiga cikihaasu yayi dukansu ya rungume su sosai ajikinshi kamar zai maidasu cikin cikinshihawaye ne suka shiga gangarowa a idanuwanshi da kuma idanuwansu sehrishbai ta6a tunanin zaiga wannan ranar bayau gashi ga aanshi sun dawo wurinshitabbas Allah ne ya kar6i adduar daya jima yana yiatare suka ago idonsu cike tab da hawaye suka haa baki wurin cewaAbba
Har cikin zuciyarshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shimuryarshi akasalance yaceKu sake maimaitawa banji ba
Abbasuka maimaita mashi kamar yadda ya umarta
Wlh kunyarku nake jiduk wani abu daya faru arayuwarku ni ne silaNa cuci rayuwarkuNaji na tsani kaina aana suna a wani hali na rayuwa amma nagaza taimakonsuzan iya zuunnawa saman guiwaowina agabanku domin in nemi gafararkutunkan ya ara maganar gaba aya ya tafi zai zuunna saman guiwowinscikin sauri suka rurrue shi suna cewaAbba dan Allah kada kayi mana haka bamu soka daina aura laifin akankadama Allah ya riga da ya addara faruwar hakandan Allah kada ka zuunna agabanmumu fa aanka ne
Ganin dagaske kneel down zaiyi agabansu yasa suka riga shi zube wa saman guiwowinsutsayawa daga tsaye yayi yana kallonsuAzmee da hajiya azeema duk suna kallon abunda ke faruwaba aramin tausayi suka basu ba
Abusufyan Hajiya azeema ce ta ambaci sunanshiamsawa yayi yayin da ya mayar da idanunshi akanta
Anatse ta soma maganayanzu ba lokacin bain ciki bane ko lokacin tuna bayaLokacin farin ciki ne wannandariya yakamata in dinga gani a fuskar kowannanku ba hawaye bako ba haka ba azmeetayi tambayar tare da mayar da idanunta kan azmee
Murmushi azmee tayi kafin taceWannan haka yakeAbusufyan ina tayaka Murna sosainayi farin ciki mara misaltuwanaji dai da sehrish ta kasance arka ceko ince suka kasance aanka nelamarin ubangiji da girma yakebabu wanda ya ta6a tsammanin hakanaji ma ina ganin kamannin fuskarka a fuskar sehrish ashe ar kacemagana take hawayen farin ciki na gangarowa daga fuskarta
Murmushi kawai abusufyan ke sakia lokacin harsu Sehrish sun mie tsaye suna tsaye akusa dashihosana ta rurrue hanunshi kamar wani zai kwace mata shi
Hajiya azeema ce taceAzmee yakamata mu basu wuri su gana da junadon na lura da yadda Uban an ukun nan ke zumui akan aanshicike da zolaya ta arasa maganar tare da miewa taja hannun azmee suka fuce suna dariya
Ajiyar zuciya ya sauke tare da mayar da idanunshi kansu jahad yacekun samu bacci kuwa jiyaya tambayesu ne saboda fuskokinsu daya gani duk a yamutsemusamman idanunsu sun anance
Haa baki sukayi wurin cewaEh
Hosana taceabbadagaske kaine Abban mu ko
Ga zahiri kin ganiyayi maganar yana yi mata nuni da fuskarshimurmushi suka saki gaba ayansu
Sun jima atsaye tare dashi suna magana jefi jefi saboda basu saba da juna baduk jin abun suke wani iri hakakamar mafarki ne suke yi ba gaske ba
Ku koma ku kwantakuyi bacci ku hutaidan har akwai inda keyi maku ciwo ku sanar mun zansa aduba ku yanzun nanwannan maganar tashi ba aramin sanyaya masu jiki tayi ba
Abbalafiyarmu qalaubabu abunda ke damun musuka fai hakan atare
Gyaa kanshi yayi tare da kama hanya zai juya da nufi yabar akin nasu
Cikin sauri jahad ta ruo hannunshi tare da cewaAbbadan Alla kada ka tafi kabarmumuna buatarka a kusa damumuna so mu kasance tare da mahaifinmu
Sehrish ta kar6e da cewahakane Abbaka dawo mu zauna atare dakaimuna buatar kyakkyawar kulawa daga wurinka
tana kai arshen maganar hosana taceAbba plsko don saboda Ni
Wani irin murmushin farin ciki abusufyan ya saki yana kallontabatare da 6ata lokaci basuka wuce saman gadon nasua tsakiya suka sanya abusufyanyayin da suka kwanta gefe da gefenshisosai ya rungume hosana ajikinshiduk in ya tuna labarin yada ta samu ta6in hankalinta nan take sai yaji idonshi sun ciko da kwalla
Idan Allah ya kaimu gobeda kaina zan gyara maku gashin kanku inyi maku kalaba guda biyukamar yadda na ta6ayi maku Lokacin da kuna yaranasan ba zaku iya tunawa ba

Jikinsu ne yayi wani irin sanyi wani irin yanayi suka shiga gaba ayansu

319 256 PM 234 810 388 4440 Boss Bature

 

Join this link to follow my tiktok acct

httpswwwtiktokcomboss_bature_t8WKx0lm4jaP_r1

 

Father of soldiers

TAKUN ARSHE

_Ga duk maison karanta littafin Abban sojojizai biya 300 nezaa tura mashi tundaga farko har inda muka tsayakuma zai cigaba da samun update dinshi akai akaiga wanda ke buata zai tura mun message ta whatsapp ina 08103884440 kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayataWasu suna aukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin nibayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_

Nagode sosai da adduoinku agare nida kuma uzurin da kukayimunhar zuwa wannan lokacinAllah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna

nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fagemai yasa baku arasa masu labarin bakuma kenan saida kuka jira niae nayi tunanin cewa zaku arasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss

Bismillah

Kai tsaye sautin ringing in wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Baccia lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanuntayatsina fuska tayi alamar an takura mata
Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya an gyara murya tare da cewaMadam ki daure ki tashi ki aga kiran nanda alama kira ne mai muhimmanci tun azu wayar ke ta ringing
Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunurawa dayar ta tashi daga zaunejikinta na sanye da sleeping dressriga da wando purple colour
Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausahannu takai tare da aukar wayar dake ajiye saman bedside drawerduba screen in wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ara tamke fuska kamar ta shanuaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnantarai a6ace taceMeyasa kika kirani fitsararrako kin kira ne don ki arasa yimun rashin kunyar taki don ubanki
on the other hand hayam tacehaba aunty lailani harna manta da abunda ya faru atsakanin mutunkan hayaam ta arasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewaIdan kin manta ae ni ban manta baKi faamun uban miyasa kika kira niidan ba haka ba ni zan kashe wayar
Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yaceZagi kamar ar maguzawako kunyata bata jisae faman ura ashar take yini dae Allah ya haani da Guyaba
cike da damuwa hayaam ta sassauta muryartatare da cewaAunty lailana shiga ukuko ince mun shiga ukuAkwai gagarumar matsalaGaba daya duk wani plan inmu ya tashi aiki
Tunda Aunty babba taji hakangabanta ya fai rasssasa asa da murya tayi taceHayaam meya faruwata irin matsala kike magana akai
Aunty lailaAshe yarinyar nan mai aikin gidansuiyar uncle insu ce Abusufyan tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuar gigice ta mie tsaye tana cewa
kutumar ubainji ubanwayaushe Abusufyan ya ta6a aureWlh aryane koma wani an aniyar ne ya fai maki hakan babban maaryaci ne
Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kantamaganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi
Wani abusufyan din kuke magana akai
Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin akin
Hankali a matuar tashe ta mie tsaye da nufin ta fuce daga cikin akinSaboda tsabar ruu ta nufi hanyar shiga toilet
gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewakada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki
A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruu yasa ta manta hanyar fita daga akinzuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiimar da tayito ko lafiyaya tambayi kansa
Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasusannan ta gane inda ta dosaRai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakinsaukowa downstairs tayi ta mii hanyar wannan tsohon store in data ta6a garame su hosana acikianan corridor in ta tsaya tana sauraran Hayaam
Wlh Aunty laila da gaske neNi shaidaceNaji komai lokacin da Uncle in nasu yake korama junaid bayanibama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakanBabban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashekuma dukkansu Mata ne kyawawan gaskekamannin su sak iri ayaKuma kina kallonsu zaki gane cewa aanshi ne
Hannu aya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kantayayin da dayan hannun ke rue da wayarta data kara a kunnanta
Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki baTaya hakan ma zata farumutumin da bai ta6a yin aure baShi zaace yana da aa har an ukuCikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same suNi ban yarda da kalamanki baHayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmiIdan wasa kike mun ki daina
6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar
Fashewa da kuka tayi saboda ululun bain cikin daya tokare mata maoshintaga zuciyarta dake ta faman tafarfasaGaba daya bata jin dain jikinta
Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta
Tsoki taja tana jinjina kai tacedama saida raina ya bani cewa arya take yi muntayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukkoShashasha kawai
Mommy kin farka kenan
Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata
Juyowa tayi tana kallontaatsaye take fuskar nan auke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeansta aure sumar kanta da ribbomyayin da hannunta ke rue da Cup mai auke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi
Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsalahakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya
aalo murmushin yae Aunty babba tayi tare da cewaLafiya naga kina murmushi
Lafiya lou mommykawai wani abun farin ciki ne ya farunasan cewa muddin kema kika jizaki yi farin ciki sosai
Murya asanyaye aunty babba taceFaamun daughter har na osa naji wannan abun farin cikinhalan an ara maku albashi neko matsayi aka ara maki wurin aiki
Dariya hafsat tayi tana girgiza kai taceMommy baki canka dai dai bawannan albishir in da nakeso inyi maki yafi arfin duk waannan abubuwan da kika lissafokar6i tea in nan ki fara korawa kafin na faa maki
Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take mia mataa hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea inkusan sau uku tana kur6arsakafin ta an jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tacedaughter dan Allah ki faamun wannan wani abun farin ciki newlh duk na osa naji
Zan faa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna
Ba inda zanjeidan zaki faamun ki faamun kawaiSae ja mun rai kikeyi tayi maganar tana faman tamke fuska
Hafsat tacebada jimawa baNa kira Aunty azeemadon in gaishe da itaAnan take sanar dani cewa aan uncle abusufyan Sun bayyana
Tunkan ta arasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannuntaYa tarwatse asaRuwan tean dake ciki ya fallatsar masu a afa
ja da baya hafsat ta anyi tana kallonta tacehaba mommyso kike ki onamin afa tadaga fain abun farin ciki
Rai amatuar 6ace taceKi 6ace mun da gani sakarya kawaiMaaryatan banzabazan ta6a yadda da kalamanku baduk bakinku aya da Hayaam
Ta fai hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi samaranta duk a jagulebin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairsta6e baki tayi tare da watsa hannayenta taceI dont care Ni dae farin ciki nakeyiDaddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga aan uncle inmu Abusufyantunkan na gansu har naji ina sonsu sosaiin ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi
Cike da farin ciki hafsat take maganarzuunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa

Lokacin da Aunty babba ta arasa bedroom in nasuhar ta aga afarta zata zura acikin akin taji muryar ishaq yana cewaAlhamdulillahAlhamdulillahAlhamdulillahAbba nayi farin ciki sosaiMeyasa tun jiya baa sanar dani baae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiyaAmma ina taya uncle murnar ganin aanshikuma ina tayamu murnar samuwar an uku acikin zuriar mugaskiya bazan ma iya jurewa baZan shirya nazo ne kawaisaboda na qosa naga an ukun mu bayin Allah
Abba yacewani abun ma sai kayi tozali da yarankyawawan an mata dasuYadda kasan photo copy in abusufyan haka sukekamanninsu sak iri aya da nashi
Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yaceAbba kafin na arasodan Allah a isar musu da saon gaisuwataAce yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosaikuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman
Insha Allah zan sanar masu yanzun nanAllah ya kawoka lfy
Ameen Abbana
Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar
tashin hankalin da baa sama shi date
Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faa mataTabijancan
Dakyar ta iya shiga cikin akinlokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati aya
Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haaiyar shadda
Ganin yana oarin bue baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewaNaji abunda ya faruHafsat ta sanar dani komaiina tayaku murnako amsar shi bata tsaya ji bata faa cikin toilet
Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom in yana cewaNi yanzu zan wuce Abuja neinyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi hakaduk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat
daga cikin toilet taceAllah ya sauke ka lpyin anje agaishe mana da mutanen gidan
zasuji insha Allah ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga akin

 

Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad
jiki asanyaye yaceAmma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu bameyasa Abbauncle whycike da tuhuma yake maganar yana kallonsuyayin da fuskarshi ke auke da damuwa
abban su ne yaceJunaidmu kanmu bamu san dasu bada ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru baaddara ce kawai ta riga fata
Shiru junaid ya anyi yana are ma su Jahad kalloyaso ace tun fil azal tare da yaran ya tasoda ba aramin kulawa zasu samu a wurin an uwansu baAllah sarki rayuwa kenanRashin sani yafi dare duhusu kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family in daba abunda zai hana su nemi danginsuTabbas an cuci rayuwarsu iri iri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsuwata shariar dae sae a lahira

Nasan yanzu kowa yana jin yunwasaboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin muYakamata yanzu komai ya wuceLokacin farin ciki neZaa shirya gagarumar walima saboda an ukun mumunaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su addara cewa tamkar yau ne suka fao duniyako ba haka ba Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsayeKowannansu fuskarshi asakesu fawan ne suka haa baki wurin cewaWannan haka yake AbbaIn sha Allah zamu nuna masu soyayyar an uwantakahar sai sun manta da dukkan wani unci da suka fuskanta na rayuwarsu murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba aramin dai yaji ba
Marshal Omar yace Sannan kuma muna ara baku hauri game da halin da kuka tsinci kankuduk da ba laifin mu baneamma mun aura ma kanmu laifinMuna neman afwarkuHosana Sehrish and Jahadforgive us pls
gaba aya jikinsu yayi sanyilokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar an uwansu ta kamasu
Jahad ce tayi oarin cewaduk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen neAllah ya riga da ya addara faruwan hakanmun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawarda juriya kuma da hauriyanzu gashi gaba ayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haamu da danginmuBabban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiin mutumin bakasa arasa maganar tayi saboda kukan daya zo mataJanyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshiyana an bubbuga bayanta
Ya Omar hosana ce ta ambaci sunan shitana faman kumshe dariya abakintagaba aya suka mayar da hankalinsu akantanuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kantakafin ta hae yatsun wuri guda ta ullasuAlamar ita dashi sun zama  an uwan juna ayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta
Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsayeya goya hannayenshi asaman wide chest insaHar lokacin bai sauko bahankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI

Karanta: Raggon Namiji Hausa Novel Complete Document Download

1 Comment

Leave a Comment