Ban bancin da ke akwai tsakanin bakar macce da fara
Tsakanin bakar macce da farar macce wacce kake da muradin aure. wata muhawara da ta kaure kafafen sada zumunta na zamani a halin yanzu ita ce ta batun kalar fatar mata a wanna zamanin inda wasu samarin ke cewa sufa sun fi son bakar macce domin ita ce zabinsu, suna kafa dalilai kamar haka.
Wasu mazan na ganin ita bakar macce ta fi farar macce tsafta saboda ko a wajen wanka da gyara jiki zaka samu ita bakar macce ta fi tsayawa da kyau ta wanke jikinta saboda tabsan cewa ita baka ce zata wanke jikinta don ya haska.
yayin da a bangare guda ba zata rika muzgunawa mijinta ba saboda ta san cewa ita baka ce kuma ba ko wane namiji ne ke da murafin aure bakar maccen ba kamar yadda wasu mazan ke bayyana wa.
Su kuma masu son auren farar macce suna cewa, ai farar macce duniya ce kuma farar macce alkyabbar mata ce domin kuwa ta fi kwantarwa da mijinta halkali a duk lokacin daya kalleta zai ji wani farin ciki ya ratsa shi, suna kafa hujja da cewa ita farar macce ta fi dadin mu’amala a kan bakar macce.
Kunji fa menene ra’ayoyinku a kan wannan batu