Yadda Zaku Rage Kiba, Nauyi dakuma Tumbi Cikin Kwanaki
RAGE KIBA DA NAUYI
(simple remedie for weight loss )
Assalamu Alaikum Warahmatullahi wabarakatuh, Wato Munsha Cikaro DA tambayoyi dakuma binciken DA mutane keyi akan yanda zasu rage kiba koh tumbi dakuma nauyi. Bayan binciken damukayi mun samo wannan bayananin wanda nake tunanin zaiyi matukar tasiri agurin biyan Wannan Bukata ta rage nauyi koh tumbi.
YADDA ZA’A HADA MAGANIN
A Samu Danyar CITTA guda biyu masu kyau sai A yayyankata ko A dandakata Sai A Samu lemon Tsami guda Daya A matsa A hada su A Tafasa da Ruwa Kofi Daya idan ya Tafasa Sai A Tace
YADDA ZA’A SHA
Za’a Dunga Shan wannnan hadin sau biyu A Rana Tsawon sati biyu
KARIN BAYANI
Ga duk Mai son ya Rage KIBA da nauyi to yakamata yasan cewa Dole sai ya canza yanayin cin Abinci Da kuma yanayin yadda mutum yake Gudanar da Rayuwar Shi
-Rage cin Abinci Mai kitse (fat)
-A Dunga yawan motsa jiki (Exercise)
– A Dunga cin ganyayyaki da kayan marmari (fruits)
-Rage yawan Zama Ana kallon TV ko Danna computer
-Bada tazarar Awa biyu idan Anci Abincin Dare kafin A kwanta.
GARGADI
Mace Mai yaron Ciki ko masu fama da ulcer Mai tsanani su nisanci Amfani da wannan Hadi
SOURCE : (GAMJI HERBAL MEDICINE RESEARCH CENTER)
Ku Karanta :