DA ƊUMI-ƊUMI: Iya mazauna Saudiya ne kawai za su yi aikin Hajjin bana

Iya mazauna Saudiya ne kawai za su yi aikin Hajjin bana

 

Iya mazauna Saudiya ne kawai za su yi aikin Hajjin bana – M’aikatar Harakokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta bayyana cewa iya ƴan ƙasa da mazauna Saudiya ne kaɗai za su yi aikin Hajjin bana (2021).

Haramain ta rawaito cewa alhazai dubu sittin (60,000) ne kaɗai, da ƴan ƙasa da baƙi na ƙasashe daban-daban da ke zaune a Saudiyya ɗin, sannan suka yi allurar rigakafin korona karo na ɗaya ko biyu, za su yi aikin Hajjin na .

Wannan Sanarwar dai ta Kawo Karshen jiran da aka dde ana yi na za’ayi Aikin Hajjin ko ba za’a yi ba, Kuma samarwar ta nuna cewa ba Wani maniyaci da Zai shiga Kasar Saudiyya a bana domin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Kadaura24 ta rawaito a Shekarar data gabata ma dai irin Wannan tsarin akai wajen gudanar da Aikin Hajji Saboda abun da ka Kira da Magance yaduwar Annobar cutar Corona.

Leave a Comment

error: Content is protected !!