Daily News

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka’idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa a Tijjaniyya

Written by Aishat

Shararren malamin addanin Islama Shehu Dahiru Bauchi ya bayyana yadda ake nada Khalifa

Shehin ya bayyana wasu hanyoyi uku da ake bi wajen nada sabon Khalifa a darikar Tijjaniyya. Shehin ya kuma taya tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi II da zama Khalifan Tijjaniyya

 

Shararren Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce akwai matakai uku da ake bi wajen nada Khalifan Darikar Tijjaniyya. Shehin ya bayyana hakan bayan da ya tarbi Sarkin Kano kuma Khalifan Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi na II ranar Litinin a gidansa da ke Bauchi.

Shehin ya bayyana hanyoyi uku da ake bi wajen nada Khalifa a darikar Tijjaniyya kamar haka:

1. Wadanda Sheikh Ibrahim Inyass yake nadawa da kansa

2. Wadanda suka gaji wadanda Sheikh Inyass ya nada

3. Wadanda Shehunan darikar Tijjaniyya ta nada

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa, nadin Sarki Muhammadu Sanusi ya fada a mataki na uku a cewar Shehun na Bauchi.

Tun da farko, kafin ya gabatar da jawabinsa, Shehin ya bukaci da a karanta masa takardar da shi sabon Khalifan, Muhammadu Sanusi, ya zo da ita daga Kaulaha.

 

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa bayan da aka karanta takardar, a cikin jawabinsa ya ce: “Ina taya ka (Sarki Muhammadu Sanusi II) murna, na samun wannan takarda da wannan mukami na Khalifanci.

KU KARANTA : Tarihin Rayuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi – A hirarsa da Bbchausa.com

“Kuma muna maraba da wannan Babban Bako wanda nan gidansu…,” inji Shehin.

A cewarsa, asalin Khalifanci Sheikh Ibrahim Inyass ya bai wa Sarkin Kano Sanusi na I ya faru ne bayan an cire Sarkin daga sarauta.

 

“Wata rana mun je Makka, sai Shehu Ibrahim yana tambaya na labarin Najeriya ina ba shi har muka iso kan labarin Khalifa Muhammadu Sanusi I.

 

“Na ce masa an sauke shi daga sarautar Kano inda ya koma Azare… Sai Shehu ya ce tunda mutanen duniya sun raba shi da jama’a, sai Shehu ya hada shi da mutanensa.

 

“Ya aike ni na je na fadawa mukaddaman Kano musamman Shehu Tijjani.

 

“Na tara Shehunan Kano na fada musu cewa Shehu ya nada mana Khalifa bayan na fadawa Shehu Tijjani da sauransu.

 

“Da shekara ta kewayo Shehu ya aiko da takarda a rubuce ta nadin,” inji Shehu Dahiru.

Leave a Comment