Hausa Novels

Itace Zabina Hausa Novel

Written by Aishat

Itace Zabina Hausa Novel

TAMBARI WRITER’S
ASSOCIATION

((home of expert and talented writer’s da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban al’umma))

T-W-A

Writing by
Zahra Ali

Bismillahir rahamanir rahim

page -4

____haba rumaisa kizama mai yadda da kaddara mai kyau ko akasinsa,sanna kizamo mai afuwa aka abunda kike da ikon ramawa sannan kika yafe Allah yanason masu mafiya.nace insha Allah anti amma saide karki matsan wajen dole saina koma duba shi pls anti nakare maganar kaman zan fashe mata dakuka,shiru tayi batare tayi maganaba ganin yanayina yacenza tace.

 

Kinsa rananda Dr yakawo ki gidannan, wallahi nadauka yamun irin halinsu na maza yayi aure bansani ba.dan dariya nayi tare dacewa haba anti tace kede bari rumaisa kinga wance makociyar tamu haka mijin yayi mata sai zuwa yayi da matarsa harda yaron cikin.rike ha’ba nayi tare da mamakin halin maza,hmm tace dai dai nan saiga ya harun yashigo sallama dauke abakin sa anti ta ansa mai sallamar ganin bakinsa yaki rufuwa ne tace damagana kenan?

Kaman jira yake yazauna tare da karkatar da kai gefe,hmm yace mum kede bari yau badan ina da karfin imani ba,da ruwana yahau sake baki mukai ni da anti muka zubamai idanu yace wallahi mum kinga wannan yana nunani da yatsan shi manuniya yace koda yaushe kokarin hada connection nake tsakanin mu amma wancen kodaddan yasace mata zuciya in anyi magana tace bahaka ba.

 

Dama shi mutum ne mai son barkonci,anti tace nadauka wani abun arziki zakace natsaya ina sauraron shiriritarka,oh mum shikenan amma gata ki tambaya kiji wancan guy din harya farajin kamshin caan amma kinganta kururuwa taringa yi tare dacewa karka tafi kabarni inka tafi mutuwa zanyi.saboda gulma mum I’m tellin you sai ga gogon nata yakawo numfashi yayinda nikuma nawa numfashin yadauke yadauke nawucin gadi.

 

Hmmm anti tasauke ajiyar zuciya tace kagama tatsuniyar naka,dan dariya yayi yace mum waiku meyasa ne bakwa daukar zancena da muhimmanci shikenan lover bird kice tak bakiyi kururuwa ba,ikon Allah cewar anti nide nakasa cewa komai nayi sai ido,shikenan mum amma duk randa kuka wayi gari ….anti katse shi tayi ta hanyan cewa toh matsassaku mai bakin magana yace nayi shiru mum amma de duk sanda ruwana yahau kece yana nunani anti tace ikon Allah harun kasake sai zuba kake kaman….no no no mum ina sweetheart dina yacanza akalan zance da tambayan twice dina cikin jindadi anti tana shafa kansu tace sunyi bacci tun suna zaman jiranku.

 

Daga nan yayi mana saida safe yatafi nima tashi nayi nadauki hasina yayinda anti kuma tadauki husna muka wuce dasu daki anti nasake jaddamun muhimmanci hakuri dakuma yafiya,bayan mun kwantar dasune akan gadone anti takama hannuna tazaunar dani baki gadon tare dacewa rumaisa alfarma daya nakeman kimun dasauri nace anti karki damu insha Allah inde betsaba hukuncin Shari’a ba zanyi.dan murmushi tayi tare dashafa gefen kuncina da hannu tace inason kidage tafiyar nan gobe,zanso jin tarihin yaruwar ki dan murmushi nayi nace inde wannan ne gimbiya tawajen Dr angama dan dariya tayi tare da cewan naga kema harun yakoya miki nidinma dariya nayi tare da cewan zama da madaukin kanwa….mikewa tayi tamun sai da safe tana cewa kiyi wanka sai kisha koda tea ne dan nasan warhaka bazaki ci abinci ba so amma karki kwanta da yunwa da toh na amsa tare da jin kaunar matar da ahalinta har cikin raina, sun taimaka mun a lokacin da wasu suke kokarin tozartani nadaga hannuna sama tare dayi musu adu’a.sannan nashiga nayi wanka nafuto agaban mirror nazauna nashafa jina a hadaddan mayuka tare da feshe jikina da turare sannan nazura riga tare da long hijab nabatar da ramuwar sallar isha’i da bansamu nayi akan lokaci ba,nakuma tashi nayi shafa’i da wutiri sannan nayi adu’oin da nasaba tare da azkar ganin nafara gangedi yasani shafa fatiha nalinke hijabin nahau gado nasa yarana agaba ina kallonsu tare da godewa Allah da ni’imar da yamun nasamun ‘ya’ya biyu lokacin daya batare da wayona ko dabara ba.wannan kyauta ce daga indillah.

Wasu Littafan :

Bacci barawo bansan lokacin da yadauke ni,can cikin bacci nayi wani mummunar mafarki a firgice natashi tare da yin adu’ar da manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata gashi yakoyar har najuya zan kara kwanciyan,sai kuma nafasa natashi nayi nafila sannan nakwanta.

 

Washe gari bayan nayi sallah nasake kwanciya sai karfe takwas natashi,nayi wanka yasauko falo anti hanan nazaune tana kallo gaisheta nayi tare da cewa anti karde harsun wuce skul?

Eh tace tare da cewa ae kinsha bacci uncle dr yace kije kiduba amaan idan zeyu amishi aiki yau saboda cikinsa yakumbura sosai dr sabiu ne yake sanar dashi dazu…..abincin da nagagara ci kenan sai tsakura nayi shidin ma dan kada anti tazargeni da cewan har yanzu inason sa amma namakaro dan tuni taharbo jirgina…

Pls don’t forget
Comment &share

Leave a Comment