Hausa Novels

Matsatsubi Hausa Novel Complete

Written by Aishat

Matsatsubi Hausa Novel Complete

Whatsapp.. 07034333288

Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace to sai ku kimtsa, kai mai rubutu ka aza alkalamin ka akan tkrd domin wannan hikayar da zan baku na dauke da matukar abubuwan al-ajabi.
Ni kai na ko tunowa nayi da lbrn sai nayi kuka.

Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira nazmir bin halad da gimbiya luzaiya yar sarki fahalul bahafus.

A wani zamani can mai tsawo da ya shude anyi wata babbar Qasa wadda ake kira duhamul.

Wannan kasa ta bunkasa da girma karfi da kuma mayaka.

A bisa wannan dalili ne kasar duhamul ta shahara kuma ta zama gagara badau a ckn dukkanin kasashen kewayenta.
Ya zamana ana matuakar tsoranta.
Sarkin da ke mulkin a wannan kasa ta duhamun wani azzalumin sarki ne ana kiransa Bashakur.
Sarki bashakur ba tsoho bane kuma ba yaro bane domin shekarunsa ba zasu gaza ar’ba’in da hudu ba. Zuwa da biyar.
Sbd zalunci irin na bashakur ko a ckn garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba ko kuma bai zamo daya daga ckn attajirai ba to yana ckn tashin hankali.
Domin ba ka da yancin kan ka. Dukiyarka da matanka zasu iya zama ba sarki a koda yaushe.
Haka kuma ana dorawa talakawa haraki mai yawa ta yadda ko kadan basa morar arzikin su baya ga wannan idan sarki bashakur ya bushi iska sai ya tura mayaka izuwa wata kasar ya basu izinin murkushe kasar a kamo masa bayi kuma a debo dukiya mai yawa.
Bisa wannan haliya ne ya tara dukiya mai tsananin yawa wacce shi kansa bai san abin da zai yi da ita ba.
A wannan zamanin na sarki bashakur tsafi baiyi shahara ba a ckn al’umma babu abinda ke tasiri face karfin damtse da yaki.
Sarkin yakin wannan birni na duhamul wani tsoho ne dan kimanin shekara saba’in da shida wanda yayi suna a duniya db tsagwaran jarumtarsa. Da kuma iya yakinsa a tarihin rayuwarsa bai taba jagorantar yaki an rasa nasara ba.
Ana kiran sa da suna Halufa…..
Zidane kd
Jafar ya kare nazarin kayan cikin kifin tsaf sannan yace “yau kuma a tsakiyar shuke-shuken teku aka watsamu Yanzu ta yaya zamu iya fita daga wajen nan nikam banga alamar akwai wata hanya ba.
Koda jin haka sai Gulzum ya bushe da dariyar karfin hali sannan yace amma dai ka cika dakiki kuma kidahumi, wa ya gaya maka cewa nan a cikin kifi muke tabbas rayuwarmu na ckn mugun hali domin ko zafin dake ckn kifin nan bai kashemu ba to kuwa yunwa da kishirwa sa kashemu. Nan da kwanaki da ba zasu gaza biyu ba.

 

Koda jin wannan batu sai gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abinda ke masa dadi.
Daga can sai Yelisa ta dubi Mazalish tace waike ina takamarki ta tsafi take? Me yasa baza ki cece mu ba daga ckn wannan masifa da muke ciki?
Mazalish tace ai kin san cewa gaba da gabanta ko? Inda tsafina zai iya cetonmu da tun kafin guguwar nan ta jefo mu cikin tekun zamu kubuta.

Jafar ya mike tsaye ya duba gaba da baya ya jinjina kai yace kai amma fa ubangijin da ya halicci wanna kifi ya cika tsoro…..koda labari ya riski sarkina sai ya tura aka kirani ya rufe ni da fada kuma yace lallai ynz a daren nan na zo na yanke kawunanku na kai masa.
Maimakon nayi hakan ne na yanke hukuncin na kubutar da ku.

Yakai wannan sarki kayi sani cewa ban kubutar da kai don komai ba sai dan na ga kana da Qarama kuma kyakykyawar yarinya wadda kake matukar so itama kuma na fuskanci ta shaku da kai dan haka ba zan so na zama sanadin raba wannan soyayya ba ta da da mahaifi domin nima ina da da wanda nake matukar so fiye da komai a rayuwata.
Ba zan so a ce ya zama maraya tun yana Qarami ba.”
koda halufa yazo nan a zancensa sai kaunarsa ta mamaye zuciyar wannan sarki da jama’arsa.
Dukkaninsu basu san sa’adda idanunsu ya ciko da kwallah ba.
Nan take suka yiwa halufa gdy sannan suka yi bankwana dashi.
Halufa ya kamo musu dawakai suka haye suka kama gabansu.
Tafiyarsu keda wuya yayi sauri ya sauya kayan jknsa sannan yayi wa kansa raunuka a jiki ya koma gidan sarki.
Koda sarki bashakur yaga jini na zuba a jkn halufa sai ya mike zumbur ya tareshi cikin firgici yana mai cewa ya kai sarkin jarumai me ya faru gare ka?
Halufa yace” ya shugabana ai lokacin da na isa kurkukun sai na iske mayaka dubu biyu sun afkawa masu gadi har sun bude dakin da aka kulle fursunoninka sun fito dasu.
Koda nayi kokarina akan na hana su tfy da fursunoninka amma sai abu ya gagara don kasan sarkin yawa yafi sarkin karfi.

Da kyar ma na kubuta da kaina.
Kafin na dawo cikin gari na nemi mataimako tuni sunyi mana nisa.”
koda jin wannan mummunan lbr sai zuciyar sarki bashkur tayi bakirkirin ya cika da bakin ciki kawai sai ta sallami halufa ya shiga tunani mai zurfi.
Daga can sai ya mike ya yi hawa ya tafi can kurkukun da kansa.
Da zuwa ya iske masu gadin a kwankwance cikin jini magashiyan.
Da kyar ya samu mutum daya wanda bai raunata ba sosai.
Sarki ya durkusa gabansa ya cakumi wuyan rigarsa cikin tsawa yace ” wane ne ya zo yayi muku wannan dayan aiki?
Mai gadin ya bude baki da kyar…..mai gadin ya bude baki da kyar yace” ai wani mutm ne shi kadai ckn shigar bakaken kaya ya zo ya tarwatsamu ya fito da fursunoninka ya kubutar dasu.
Koda jin haka sai sarki bashkur yayi jifa da mai gadin yace wannan zancen banza ne duk fadin kasar mahazus babu wani sadauki mai irin wannan jarumtarkar. Lallai ka tabbata makaryaci.
Kawai sai sarki bashkur ya zare takobi ya fille kan wannan mai gadin. Nan take ya sake hawa dokinsa ya sukwane shi ckn fushi ya koma ckn gari.
Da zuwa bi zame ko’ina ba sai gdjn manya mayankan garin yana tmbyr su ko jarumi halufa yazo neman taimako su a ckn wannan daren bisa farmakin sumame da aka kaiwa kurkukunsa?
Kowa sai yace shi ba a neme shiba hasalima yanzu yake jin lbrn abinda ya faru.

Yayin sarki bashkur ya gaji da yawan tmby sai ya koma gd ya kwanta ckn tsananin bakin ciki kashe gari da safe sarki bashkur ya tara dukkan yan majalisar sa ya sanar dasu duk abind ya faru jiya da daddare kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma yayi bincikeya gano cewa ba kowanne ya aikata wannan mummunan aiki ba face jarumi hakufa.
Nan take ya kawo hujjojinsa guda biyu hujja ta farko itace babu wani sadauki a gaba daya wannan hahiya wanda zai iya tarwatsa barade dubu face jarumi halufa.

Hujja ta biyu itace halufa yayi masa karyar cewa ya dawo ckn gari ya nemi taimakon wasu mayakan amma da aka tmy su sai suaka ce ba wanda ya nemi taimakonsu.
Duk wannan bayani da sarki bashkur yake halufa na zaune gefe guda yana saurari kawai sai yayi shiru bai ce komai ba yana muzurai kawai.
Sarki bashkur ya dubi fadawansa yace to kunji laifin halufa ya aikata don haka sai ku yanke masa hukunci da kan ku.
Gaba daya yan majalisar suka yi tsit aka rasa wanda zai ce wani abu. Daga can sai waziri yace ya sarkin sarakuna ai ni a ganina wannan hukuncin ba zai yanku ba yanzu muna bktr muyi zama na musamman.Sai da aka shafe arba’in ana mahawara a majalisa akan irin hukuncin da za.a yankewa halufa.
A karshe dai aka yanke masa hukunci cewa an dakatar dashi daga kan matsayin sa na sarkin yaki har tsawon shekara ashirin masu zuwa nan gaba.
Kuma dukiyarsa aka raba ta kaso biyu aka dauki kaso guda aka ravawa masu gadin gidan kurkukun aka bar masa guda.

Daga wannan rana halufa ya cire hankalinsa daga harkokin fada gaba daya ya maida nutsuwarsa akan dansa guda daya wanda suka haifa tare da matarsa zuwaisa.
Wannan da an rada masa suna Nazmir.
Nazmir ya taso yaro mai kwarjini kwazo da basira ya zamana mahaifinsa na koyar dashi kyawawan dabi’u kuma yana koya masa juriya jarumta da dabarun yaki.
Yayin da Nazmir ya cika shekara 14 sai ya zamo jarumin gsk kuma farin jininsa ya yawaita tsakanin mutane garin.
Sbd irin kyawawan halayensa na tausayi da jin kai da kuma biyayya ga na gaba dashi.
A bangren jarumta kuwa sai da yabar abin tarihi a kasar duhamul domin shi kadai yake shg daji ya yi farautar manyan dabbobin dawa masu hadari.
Sai dai aga yazo da gawarsu.
Tun yana jarraba jarumtarsa a tsakanin sa’anninsa har ta kai cewa yana tunkarar mayna baraden kasar daya bayan daya.
Duk wanda suka gwada yar kashi ko tsagwaron yaki sai ya sami galaba akan sa.

Ckn kankanin lokaci lbrn jarumi nazmir ya yadu ko’ina a fadin kasar ya zamana ana zuwa ganinsa daga gari-gari.
Lokacin da nazmir ya cika shekara 20 a duniya sai kyawunsa ya kara bayyana a fili karara.
Jarumtakarsa ta linka ta da ya zamana bashi da abokai sai yayan sarautar kasa amma da yake shi mutum ne na mutane mai saukin kai bai yar da wasu abokansa ba su shida wadanda suka taso tun yarinta.
Wandannan abokai gaba daya yayan talakawa ne.
Kuma dare da rana suna tare da nazmir duk da cewa mahaifinsa yafi iyayensu arziki da daukaka.
Daga cikinsu akwai Sharhil, Bagwan, Hasuf, Iklam, Bardil da kuma Huzaik…
Al’amarin su jafar kuwa lokacin da suka shige Qarkashin Qasa inda birnin Qira yake. Suka zube Qasa suna haki cikin mugun tashin hankali sai kawai suka ga sarki Azbir na tare dau.
Koda ya hada idanu da Mashrila sai yace” yake ma’abociyar hikima ynz dai kinga irin dabarar da muatanen galbasa suka zo da ita ma.ana sun zo da Qatuwar garkuwa da majaujawa wadanda ke lalata kibiyoyinmu ynz mene ne abinyi ? Wace hikima za ki sanar da mu hanzarta amfani da ita domin nan da rabin sa.a kacal za su gama da mu gaba daya.”
yayin da mashrila ta ji wannan tmby sai tayi shiru tswan dakika biyar tana tunani daga bisani ta dubi sarki azbir tace” ya kai wannan sarki ka yi sani cewa babu wata dabara face abu daya abin kuwa shine indai muna san mu sami galaba mu kwaci majaujawar dake hannayensu mu yake su da ita.”
koda jin haka sai ran Azbir ya baci yace “haba yarinya wannan wace irin mgn ce kike ta rashin hankali ta yaya zamu iya kwatar makami a hannun mutanen galbasa alhalin sun fi mu karfi kuma sun linkamu girma sau 10.”
Cikin fushi mashrila ta nuna Azbir da hannu tace” wacece yarinya shin kana tsammanin za ka girme nine? Dube kafa kamar a kife da kwando.”
koda jin haka sai Azbir ya yi murmushin karfin hali yace” au dan kin ganni dan guntu shine kike tsammanin ke sa.a ta ce. Ko kuwa dan kinga fuskata irinta yara? To tsaya kiji a wannan watan da muke ciki na cika shekara dubu daya da dari da hamsin.
Duk wannan nahiyar tamu Galbasa ne kawai ya girme ni.
Koda jin wannan batu sai jkn mashrila yai sanyi ta kasa cewa komai.
Gulzum ya dubi azbir ya ce kaga ku bar musun shekaru dan nasan a shekaruna baka dauki kaso daya ba.
Abin da nake so dakai shine mu yi amfani da shawarar yarinyar nan domin itace kadai mafita.
Ku sani cewa a barin tayi akan bar arha, kuma damu zauna a zo a ci mu da yaki gwara mu jaraba iya kokarinmu dan wani lkcn sai an gwada ake dacewa. Dan haka zan yi amfani da damata da kuma dabarun yakin da na koya irin namu na aljanu na kwato majajjawa daCikin Hanzari Jafar, Yelisa, Mashrila da azbir suka daka tsalle suka dane bayan aljani Gulzum.
Koda sauran mutanen Galbasa suka ga irin barnar da Gulzum ya soma yi muru sai dayawa suka yi kukan kura suka afka masa, amma kafin su cim masa tuni sun makara domin har ya sami damar finciko wadansu majajjawun guda biyu. Kawai sai ya mikawa su Jafar Guda sannan ya rike guda a hannunsa ya zamana yana amfani da guda biyu shi kadai.
Koda Jafar, Yelisa, da Mashrila suka kama majaujawar da niyyar riketa sai nauyinta ya rinjaye su, suka subuto daga kan aljani Gulzum za su fado Qasa.
Cikin tsananin zafin nama Azbir ya ruko jikin majaujawar da hannu daya sai ga su jafar suna rito a jikin majaujawar.
Azbir ya dawo da su kan gulzum kowannensu ya zauna daram sannan shi kuma ya kama majaujawar da hannu biyu ya fara kaiwa mutanen Galbasa farmaki kamar yadda aljani Gulzum ke yi.
Al’amarin da ya jefa su Jafar cikin matuqar mamaki kenan jafar ya dubi mashrila yace” ke kin ga wannan mutumin da kike rainawa ashe ma duk ya fi mu Qarfi ba mu sani ba. Lallai sai miya ta Qare ake sanin maci tuwo.
Yelisa tayi ajiyar zuciya sannan tace”Tab dijan daga yau na daina raina Qananan mutane ni kam ban taba tsammanin cewa wannan mutum zai iya daukar koda abu mai nauyi mutum ba. Sai ga shi yana sarrafa wannan Qatuwar majaujawar wadda nauyinta ya wuce gawarwakin bil’adama guda dubu, kuma manyan Qarata ababan kwatance.
cikin Qankanin lokaci gulzum da sarki Azbir suka tashi hankalin mutanen Galbasa suka Quntata musu, suka hana su sakat, duk da cewa kuwa suma ba su fa sa barna ba domin sun sha jinin sama da mutum miliyan uku da doriya.
Yayin da masifa tayi masifa,artabu,dauki ba dadi da tsananin turnuku ya yawaita, sai Dauduf ya Sake yin sama cikin tsananin gudu ya isa inda su sarki Galbasa suke wannan karan sai gashi ya zo cikin mugun tashin hankali yana ta haki ya risina gaban galbasa yace”Ya shugabana wani bakon aljani tare da Azbir da wadannan bakin bil’adama sun sami nasarar qwatar majaujawa guda uku daga hannun jama.ar mu har sun yi mana gagarumar barna.
Gaba dayanmu mun rasa yadda zamu yi da su lallai muna bukatar taimakonka cikin hanzari in ba haka ba kuwa nan da Qankanin lokaci za su iya Qarar da mu.
Koda jin wannan batu sai Galbasa ya bude fukafukansa yayi cikin Qasa cikin tsananin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya koda ganin haka sai kowa ya bi bayan su a wannan lokacin ne galbasa ya rinka Qwala ihu mai tsananin firgitarwa wanda amonsa ya haifar da faruwa wani irin rugugi a sararin sama tamkar tsawa. Wuta ta rinka fita daga bakinsa.
Lokacin da Mazalish ta ga kowa ya bi mahaifinta sai ta noke ta tsaya ita kadai shi kuwa dauduf sai ya noke a bayanta yana mai buya dan kar tasan da shi.
Abin da bai sani ba shine tuntuni ta gane manufarsa kuma har tayi tunanin hanyar da za ta yi maganinsa.
Sai da ya rage saura su kadai a wajen sannan mazalish ta yunkura ta juya ta soki idanuwan dauduf da faratan hannayenta. Take idanunsa sua fashe ya zama makaho.
Bai san sadda ya kwalla ihu ba sbd tsananin radadi da yake ji.
Kafin yayi wani yunkuri tuni mazalish ta fiddo wata igiyar tsafi ta daure shi tamau.
Nan ta bar shi a sararin sama iska na ta kulin kubura dashi sai ka ga yayi gaba yayi baya amma ya kasa yin sama ko Qasa sai Qara yake yi.
Cikin tsananin mugun gudu tamkar an harba tauraruwa mai wutsiya mazalish ta bi bayan su sarki Galbasa amma kafin ta isa tuni Galbasa ya riski su Gulzum.
Da zuwa yayi wani tsafi sai ga shi ya fincike majaujawar hannunsu tamkar mayan Qarfe ya zuke guntun Qarfe da ke ajiye a gefe guda nan take ya sake yin wani tsafin sai ga igiyar tsafi ta daddaure su tamau suka kasa motsi.

Anan ne Yelisa ta tuna cewa ita ma fa matsafiya ce yar babban matsafi kawai sai ta rufe ido tayi kiraye-kiraye da yan tsatsube-tsatsube amma sai ta ji shiru kamar maye yaci shirwa sarki Galbasa ya dube ta ya tuntsire da dariya yace”Ke yarinya daina bata lokacin ki babu wani irin tsafi da zai yi aiki anan in ba irin namu ba.
Lallai zan tafi da ku izuwa fadata dan nayi muku mugun kisa sanadiyar barnar da kuka yi mini.
sarki galbasa na gama fadin haka ya bada umarni a cgb da shan jinin mutanen gari nan aka sa musu wawa tamkar an ajiyewa karnuka yankan nama guda faya kacal.
Nan fa gari ya sake hargitsewa da iface-iface sai dai ka ga jini na ambaliya da famtsamuwa tamkar teku ta balle.
Ana cikin haka mazalish ta iso tamkar walkiya cikin abinda bai wuce dakika guda ba ta tsitstsinka igiyar da ta daure su jafar da karfin tsafi sannan ta sure su ta dora su a gadan bayanta ta kuma suri kibiya guda irin wacce mazalish tasa aka kera tare da na’urar harbata duk da hannu daya ta sake cillawa da gudu ta bace a ckn sararin samaniya tamkar walkiya.
“kar ku yi zatan mun tsira da ni da ku daga yanzu zuwa kowane lokaci za ku iya ganin mahaifina sarki Galbasa domin shi kadai ne zai iya cim mani. Amma dai ckn baradansa babu wanda zai iya suwa nan ya riske mu.
Ai kuwa bata gama rufe bakinta ba sai suka ga Galbasa biye da su.Aikuwa mazalish bata gama rufe bakinta ba sai suka ga sarki Galbasa biye da su cikin tsananin gudu tamkar an harbo kibiya.
Jikinsu jafar na karkarwa suka shiga saita shi da kibiyar.
Amma da sun saita shi sai ya bace ko kuma ya zama haske.
Shi kuma sai ya dunga harbo musu kibiyoyin tsafi da wutar tsafi ba dan mazalish na zilliya da gocewa ba da tuni sun hallaka gaba dayansu.
Kai in da a ce mutum na ganin wannan artabu sai ka yi zatan kare ne ya biyo kyanwa a tsiyace tana neman tsira da rayuwarta.
Sai da aka shafe sa’a biyar cur ana wannan gumurzu Sarki Galbasa bai cin musu ba suma ba su sami damar harbinsa da kibiya ba.
Ba zato ba tsammani sai wutar tsafin Galbasa ta fara Qona su Jafar.
Yayin sa ya zamana babu wanda bai kone ba daga cikin su.
Yayin da mazalish ta tabbatar da cewa in dai aka cgb da wannan gumurzu a haka Galbasa zai samu nasarar hallakasu sai ta juyo cikin shammace da zafin nama ta kama bakin kunamar harba kibiyoyin nan da hannunta ta saita mahaifinta ta sakar masa harbi a tsakiyar Qirjinsa.
Nan take kibiyar ta huda Qirjinsa ta bullo gadan bayansa sai suka ji ya kurma uban ihu, sannan ya yi Qasa luuuuuu…………..
Tun suna hango shi har ya bace musu da gani dama a wannan lokacin mazalish ta tsaya cak a sararin samaniya.
Nan take idanunta suka ciko da Qwalla ta fara zubar da hawaye kafin waninsu yace wani abu ta she da kuka tana mai nadamar abinda ta aikata a wannan lokacin ne suka ga sarki azbir ya fashe da kuka jafar ya dafa kafadarsa yace ” ya kai wannan sarki ina dalilin kukan ka ?
Azbir yayi ajiyar zuciya sannan yace ” ba komai ne ya sani kuka ba face sanin cewa a halin yanzu gaba dayan mutanen Qasa ta sun zama mayu domin a tabbata babu wanda zai tsira daga sharrin mutanen Galbasa ni kam na san bani ba komawa Qasata har abada shi kenan na rasa iyalina dangina mutanena da mulkina da Qasata.
Yayin da Azbir ya zo nan a zancen sa sai tausayi ya kama su jafar gaba daya ita kuwa mazalish sai da taci kukanta ta koshi sannan ta ci gaba da tafiya a sararin samaniya, tana dauke da su jafar a gadan bayanta.
Bata gushe tana tafiya ba sai bayan sun shude sa’a bakwai,
sannan ta sauko Qasa suka dire a tsakiyar wani irin jeji mai ababan al’ajabi kala-kala.
Bayan su jafar sun sauka daga kanta sai ta girgiza ta dawo cikakkiyar siffa irinta mutane sosai.
Mazalish ta dubi su jafar har yanzu hawaye na zuba a idanunta tace ” yanzu na dawo cikin ainihin halittata siffar da kuka ganni da ita dazu ba komai ba ce face sirrin tsafi.”
yayin da mzalish ta zo nan a zancenta sai jafar ya dubeta yace” yake yar.uwa ya akai kika zama mutum kamar mu alhalin kin kasance jinsin mayu ?”
nan take mazalish ta basu lbrn yadda aka yi mahaifinta ya cire mata maita da kuma yadda ya raba rabin karfin damtsensa da rabin tsafinsa.
Jafar ya sake dubanta ya to mene ne dalilin da yasa kika ceci rayuwarmu har kika harbi mahaifin ki da hannunki ?”
Zidane kd
Nan take jafar ya kwashe labarin su kaf tun daga farko har Qarshe ya sanar da mazalish.
Bayan ya gama ne ta cika da tsananin mamaki kuma ta dauki alkawarin tafiya tare da su har a gama karanta shafukan kundin tsatsuba dan ta hadu da masoyinta Hubairu bin mas’ud wanda ba ta taba ganinsa ba sai a mudubin tsafi.
Bayan jafar ya gama baiwa mazalish labarinsu sai suka mike gaba daya suka nausa ckn wannan jeji suka yi ta tafiya ba tare da sanin inda suka dosa ba.
Kwatsam sai suka ga wata rijiya dama kishirwa suke ji.
Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da Qatan murfi karfe a bakinta an yi rubutu kamar haka” babu mai bude wannan rijiya yasha ruwan cikinta sai bakin da suka zo daga wata duniyar.”
koda gama krnt wannan jawabi sai Jafar ya dubi Yelisa da Gulzum yayi murmushi yace”ai domin mu aka yi rijiyar nan. Yakai gulzum maza ka bude mana mu sha ruwa ko ma huta da kishirwa.”
cikin fushi gulzum yace waye bawanka har da za ka bani umarni?
Koda jin haka sai yelisa tace…ba zato ba tsammani kuma sai ga sarki lu’umanu bisa dardumar tsafi ta sauke shi daf da jarumi hubairu suka fuskanci juna sai ya murtuke fuska yace” ya kai babban makiyina kayi sani cewa babu inda zaka shiga a ckn duniya nan ka boye mini, ka tuna cewa munyi gagarumin fada ni da kai har sau 2 ko kuma nace sau uku munyi kare jini biri jini, ina tabbatar maka da cewa wannan karan na zo da cikakken shirin irin wanda bantaba yi ba don haka dolee ne naga bayanka. Tabbas yau sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinka.
Ita kuwa masoyiyar taka dole na mallaketa ko tana so ko bata so.
Jarumi hubairu ya dakawa lu’umanu tsawa yace” kai tsohon makiyin ALLAH babban mushiriki ma.abocin fasikanci domin ina tare da ubangijin musulunci addinin gsky.
Duk wanda ya rukeshi yafi karfin masu yin waninsa da izinin allah zan samu rinjaye akanka kuma da sannu zamu Qarar da ire-irenku a doran kasa mu kawar da kafirci mu shimfida musulunci ya baibaye duniya gaba daya.
Koda jin wannan batu sai sarki lu.umanu ya…
kafin su jarumi hubairu suyi wani yunkuri tuni sarki lu’umanu dun bace kuma sun bacene tare da gimbiya sima.
Cikin hanzari jarumi hubairu ya krnt wata addu’a sai wannan duhu ya yaye haske ya baibaye tamkar ba’a taba yin duhuba.
Koda hubairu yaga babu su lu’umanu kuma babu gimbiya sima sai hankalinsa ya tashi ckn sauri ya bada umarni abi sawun su.
Ai kamar an harba kibiyoyi dakarun musuluncin suka harba jukkunansu suka luluka ckn gajimare suna masu tsananin gudu ckn sahu sahu abin gwanin ban sha’awa kaikace tsuntsaye ne ke bikin gsar gwada tsere,
wannan shine abina ya faru tsakanin su jarumi hubairu da su sarki lu’umanu yayin da aka fafata bakin gumurzu a gdn bokanya samaratu don daukar gimbiya sima.

Add Comment

Leave a Comment