Daily News

Ramadan: Abincin da ya kamata mai azumi ya ci da wanda bai kamata ba

Written by Aishat

Watan azumi lokaci ne da mutane suke kaurace wa abinci tun kafin ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

 

Hakan yana sanya mutane jin yunwa da kishirya.

Masu azumi sukan ci abinci nau’o’i daban-daban a lokutan sahur da na buda baki.

Sai dai likitoci sun bayyana nau’in abincin da ya kamata mai azumi ya ci da wanda ya kamata ya kaucewa.

Dr Lawan Musa Tahir, wani likita a asibitin Nizamiye da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya irin abincin da ya kamata masu azumi su ci da kuma wadanda suka kamata a kauracewa.

 

Masu fama da wasu cututtuka

Masu azumi sun kasu kashi-kashi: misali, akwai wanda da ma kafin azumin, saboda da wata larura a asibiti za a dora shi kan abincin da ya kamata ya ci ko kada ya ci.

 

Misali a nan shi kamar wanda yake da ciwon suga za a dora shi kan dokoki na yanayin abincin da zai ci, ko wanda yake da ciwon hanta, shi ma za a dora shi kan dokoki na abinci da zai ci.

 

Haka kuma wanda yake da food allergy, wato wanda jikinsa ba ya karbar wasu nau’o’in na abinci: to, ka ga wannan tun kafin azumi akwai dokoki na yanayin abincin da yake ci, don haka idan azumi ya zo zai ci gaba da bin dokokin.

 

Mutanen da lafiyarsu lau

Sai kuma mutanen da su da ma lafiyarsu kalau. Su ma ya danganta da inda suka samu kansu lokacin azumi.

 

Misali, idan mutum yana zaune a irin kasashenmu masu zafi inda mutane suke bukatar yawan shan ruwa akai-kai, su ma akwai yadda ya kamata su yi.

 

Ga jerin abinci da abubuwan dasuka kamata masu azumi su yi:

 

  • Guji cin abinci mai yaji da wanda yake da maiko sosai saboda zai kara musu kishirwa sannan akwai zafin gari
  • A ci abinci mai ruwa-ruwa, musamman ‘ya’yan itatuwa irin su ayaba, abarba, gwanda, da makamantansu
  • A sha ruwan zafi kamar shayi ko koko ko kunu domin suna gyara ciki musamman bayan an dade ba a ci abinci ba
  • A guji cika ciki fal da abinci – za ka ga wasu suna cin abinci sosai idan an sha ruwa. Hakan yana da matsala. An fi so ka ci abinci kadan sannan ka huta yadda idan an jima za ka iya sake ci
  • A guji shan taba da dangoginta saboda tana da illa

Babu laifi idan an motsa jiki lokaci azumi – amma a yi shi saisa-saisa.

Add Comment

Leave a Comment