Daily News

Tarihin Rayuwar Jarumi Lawan Ahmad Izzar So

Written by Aishat

WAYE LAWAN  YAHAYA AHMAD

Lawan Yahaya Ahmad na daya daga cikin Jaruman Masana’antar shirya Fina-finan Hausa dake Kano, kuma yasamu shiga masana’antar ne da taimakon Jarumi Ali Nuhu.

 

HAIHUWARSA

Ana haifi Jarumi Lawan Ahmad a ranar 13 ga watan March din Shekarar Alib 1982, a karamar hukumar Bakori dake jihar Katsina a Najeriya.

 

KARATUNSA

Lawal Ahmad yayi karatunsa na Firamari a makarantar Nadabo Primary School Bakori, a shekarar alib 1987 zuwa shekarar alib 1993.

 

Lawal Ahmad yayi karatunsa na Karamar Sakandire a makarantar Gobnati ta Government Day Secondary School Bakori, sanan Sai ya wuce zuwa Makarantar Gobnati ta Sharada dake Kano wato Government Daya Secondary School Sharada, inda a nan ya mallaki takardar shaidar gama Sakandiri wato SSCE.

 

Hoton lawan ahmad izzar so tare DA dansa DA aka Haifa Mai kwanakinnan

 

 

Lawal Ahmad ya kuma fadada Iliminsa  a Boko yayinda ya shiga makarantar Federal College Of Education dake Kano a shekarar 2002 zuwa 2004. Daga nan kuma ya wuce zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule a shekarar 2016.

 

SHIGARSA MASANA’ANTAR FIM

Jarumi Lawan Ahmad ya shiga masana’antar Shirya fina-finan Hausa dake Kano a shekarar alib 1999, kuma yayi fim dinsa na farko mai suna SIRAD.

 

Lawal Ahmad ya mallaki Kamfanin shirya Fina-finan Hausa mai suna Bakori Entertainment

4 Comments

Leave a Comment