Hausa Novels

Matar lameer Complete Hausa Novel

Written by Aishat

MATAR LAMEER HAUSA NOVEL COMPLETE

 

Rintse idonsa yayi da sauri yace “subhanallahi meye yasa bakije an wanke miki gurin ba?” Shiru tayi tana sharar hawaye kafin ya miqe yace “zo na wanke miki nasa miki magani” batayi jayayya dashi ba ta miqe tabishi yasa ta zauna a gefen motarsa shikuma ya dauko hydrogen da corton ya fara wanke Mata tana kuka tana ciccije leɓe yanayi Mata sannu lkc zuwa lkc yana ɗagowa yana kallon kyakkyawar fuskarta data jiqe sharƙaf da hawaye yanajin wani tausayinta yana kwarara a sassan jikinsa.

 

Koda ya gama yayi mata plasting ɗin zama yayi ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar halittar bafulanar yanajin wani shauqi na taso masa, a hankali cikin dashewar murya yace

“Ya sunanki?” haɗiye kukanta tayi tace “Jiddoh Arɗo Jibir” iska ya furzar ya miƙe yace “ok gobe kizonan idan kin ɗauko nonon ki kawo min zan siya zan taho da likita yayi miki allura kinsan cizo kare dafine dashi ƙafarki zata iya ruɓewa idan baayi miki allura ba, na nawane nonon dasu Idin suka shanye miki”
Shiru tayi kamar bazatayi mgn ba ta fara haɗe kayanta bayan ta gama ta miƙe zata tafi ya riƙe hijjab dinta fuskarsa murtuk ya zaro dubu biyu ya bata yace “ki ajiyemin canji na gobe zan karba kada Goggo ta dakarmin ke” ƙememe taƙi karɓar kudin wai dukanta zaayi nononta na jaka huɗu da rabi ne.

 

Kama gefen kallabinta yayi ya ɗaure mata dubu daya ya bata ɗaya a hannunta yace “kice da goggo wani ne ya siyi nono babu canji shine yace gobe kibashi na rabin jakar”
Dariya tayi tace “aradun Allah kaɗo kanada wayo sosai zaka tai dani burni na ƙaro wayo?”
dariya ta bashi ya shiga motarsa ya kunna tana tsaye har yayi kwana zai tafi ta bude baki tace “Kaɗo” juyowa yayi ya tsaya wai kaɗo sai kuma yayi murmushi ya daga mata hannu itama ta daga masa hannu ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo yana ajiyar zuciya a hankali yace “Hauwa’u kulu Maijiddah.

Figar motar yayi a guje ya fice daga lungun tundaga wannan lkc ya kasance kullum shine yake siye nononta idan ta dauko idan kuma zaiyi tafiya bazaizo ba to yakan bawa manajan gdan gonarsa kudin ya rinƙa bata kullum hakanne ya wanzar da shaƙuwa me ƙarfi tsakaninsu.

ASALIN LBR

Matar lameer complete hausa novel – yaciga da cewa Tananan zaune a wannan guri har duhun magaruba ya fara sawo kai ta miƙe a hankali ta fara fita daga saƙaƙiyar har ta fito titi sosai ta fara tafiya cikin rashin kuzari har ta isa rugarsu takuwa yi saa Allah bai haɗata da ƴan dumbule ba don ta lura nononta da Allah ya wadatata dasu suna mugun jan hankalin maza duk da cewa kullum cikin taresu takeyi da hannunta kasancewar ba bra suke sanyawa ba haka suke yawo da abunsu a tsaye cako cako wannan dalilin yasa kullum take taresu saboda kunya takeji taga sunyi cokal cokal dinnan.

Isarta gda kenan taga gilmawar wata baqar LAND GRUSSER ta bayan bukkokinsu a guje hakanan taji gabanta ya fadi tanason ganin waye a ciki amma babu dama da alamun na cikin ma a fusace yake.

Ƙwafa tayi ta shiga gdan nasu taja tayi turus ganin ƴan gidan nasu gabaɗaya tun daga kan baffansu har zuwa kakansu mahaifin baffansu kowa yayi cirko cirko suntada gemu da alamun wani abune mara daɗi ya hwaru batasan hawa ba balle sauka taji an fincikota tsakiyar filin da mutane sama da talatin sukayiwa da’ira wanda ko gutsuttsurata akayi ƙila wani bazai samu ba anyi cilli da ita an hau bugunta ta ko’ina suna haki kamar waɗanda aka sanyasu dole.

Itakuwa baiwar Allah Jiddoh sai ihu takeyi tana roƙonsu su bar dukanta zata mutu amma babu wanda yaji tausayinta ya ƙyaleta ita kuwa goggo tashi tayi tabar gurin saboda tanayin mgn kanta zaa dawo ace tayi rashin kunya.

Basu bar jibgar Jiddoh ba saida sukaga ta daina numfashi sannan kowa ya koma gefe yayi duru duru suna kallon kallo wannan yana faɗin kaine ka daketa a makasa wannsn yana faɗin aa kaine, baffane ya ƙuta yace “yo ba gwara a kashetan ba a huta da wannan abin kunyar da ta janyo mamu, wai ni Arɗo Jibo nine Kaɗo ya iya tarar cikin idona yace yanason irin mutum daga gareni wannan wanne irin tozarci ne Jiddoh tajamin a duniya”……………

 

UMMUH HAIRAN CE…

5 Comments

Leave a Comment