Uncategorized

Khaleel Hausa Novel Complete

Written by Aishat

KHALEEL HAUSA NOVEL COMPLETE

Written by Aishatu H Aliyu

Dedicated to Meesha luv

Bismillahir rahmanir rahim

PAGE

1&2

Da gudu ta rugo ta dale cinyar Ammi tana haki, idanunta cike da tsoro cikin tsawa Ammi tace.
“Ke lafiya kar ki karya ni mana!”
Ta kuma lafewa hade da fashewa da kuka.
“Don Allah Ammi ki ce kar yaya ya dake ni wallahi bazan kara ba”
Yarinya yar kimanin shekara sha daya ke wannan maganar.
Ammi tayi dariya kenan tana shirin yin magana ya shigo cikin tafiyarsa ta kasaita da zabgegiyar dorina a hannunsa.
“Wayyo Allah don Allah kar ka dakeni ni wallahi na tuba” Sanin halin Hanifah na rashin jin magana ya sanya Ammi bata tanka ba don kuwa inda sabo sun saba haka dashi. Yayo kanta gadan gadan da niyyar dukanta ta fasa wata irin gigitaciyar kara da tilas sai da Khaleel ya fasa dukannata, jawo ta yayi da karfin tsiya yayi dakinsa da ita sai ihu take tana tirje tirje, fuskarsa a murtuke yace.
“Wayace ki ta6a min laptop? Kin goge min assignment dina gaba daya dana 6ata lokaci inayi jiya da daddare, kinsan ko karfe nawa na kai ina yinsa?” Hanifa da hawaye sha6e sha6e a fuskanta tace. “Don Allah kayi hakuri na tuba bazan sake ba”
“Shut up! Sakarai marar jin magana, ke da ko an fada miki ki dena ba denawan zakiyi ba?”
Ta kuma fashewa da kuka.
Ammi ta shigo tana fadin.
“Lafiya Khaleel don Allah ka kyale yarinyar nan haka bazata kara ba”
“Ammi kinsan me tayi min?” Ya karashe kamar zeyi kuka.
“Koma meye dai kayi hakuri insha Allah bazata kara ba ko Hanifa?” Ta girgiza kai da sauri
“Shikenan tashi kije kuma wallahi kika kara sai na kakakkarya ki a gidannan” Wani lungu ta raku6e tana kuka cikin ranta in banda mugu ba abinda take kiran Khaleel, wani tsanarsa take ji a ranta, ita dama tunda suka taso kwata kwata jininsu bai hadu ba, shi Khaleel saboda rashin jin Hanifah ya sanya basu daidaita wa, sannan yana da wani attitude na irin nine babba bana son raini, sannan baya wasa da dariya da yaro, Hanifah zata iya kirga ko sau nawa ta ta6a ganin dariyarsa, ita kuma Hanifah gani take ya takura mata sheyasa ta tsane sa.
Saif (yayanta kuma kanin Khaleel) dan kimanin shekara sha biyar (15) yazo wucewa ya jiyo sautin kuka, murmushi yayi don kuwa yasan bazai wuce yar auta ba, yana zuwa yaganta ta baje kasa tana kuka, durkusawa yayi daidai saitinta yace.
“Auta” bata ansa ba sai ma kara sautin kukan da tayi. Dago ta yayi yana share mata hawaye.
“Auta kukan me kikeyi haka?”
Cikin sautin kuka tace
“Ba yaya bane” ta bashi labari
Yayi murmushi
“Dama nasan bai wuce yayan ay, dan Allah Hanifah ki dinga nutsuwa ki bar rashin ji, kuma ki dena shiga gonarsa ke kinsani sarai baya son raini, sannan kema da laifinki meyasa kika ta6a masa laptop? Ni shaida ne jiya baiyi bacci ba har kusan asuba kinga kuwa dole yayi fada”
Ta girgiza kanta tace to.
Hannunta ya kamo
“Kinyi home work?”
Ta girgiza kanta alamun a’a
Yace “maza kije kiyi kafin kisha bulala a makaranta”
Daga haka yaja hannunta ya raka ta dakinta wanda yaji adon pink and purple, komai na more rayuwa akwai a dakin, dakin ya hadu karshe. A falo Saif ya iske Khaleel da Ammi suna kallo ya samu wuri yayi ya zauna yayi joining dinsu suka cigaba da kallo.
Ba’a juma ba Halisa (mai aiki) ta shigo ta gaida su alamun gimamawa tace
“Ammi me za’a girka da daddare?”
Ammi tace “wallahi bansani ba Halisa, ki tambayi Su Saif” Nan suka ce ta girka jollof din taliya mai kifi. Bayan fitarta Ammi ta mike don tana son taje ta karanta wani littafin Hadith a dakinta, a yayinda Saif ya mike yayi waje don yana so ya je gidan wani abokinsa. Khaleel kuwa gyara zamansa yayi don akwai wani program da zai kalla don time yayi.
A 6angaren Hanifah kuwa sauri ta yi ta kammala homework dinta don tana so ta kalli wani series a Disney channel, sai doki takeyi don tana matukar son “Sony with a chance” da isarta ta dauki remote ta chanza channel da sauri don ita sam bata ga wani Khaleel a wurin ba.
Khaleel ya kalleta da mamaki yace
“Ke!”
A razane ta juyo har sai da remote din da ke hannunta ya fadi kasa”
Fuskarsa a murtuke yace
“Ke bakida hankali bakiga ina kallo ba ne zaki wani chanza?”
Da sauri tace
“Dan Allah yaya ka barni na kalla…”
A kafule ya mike yace
“Ai sai kiyi ta kallo” ya fice a zuciye. Ita kuwa ta daga kafada alamun oho ta cigaba da kallonta.
Bayan sallar isha’i ma koda Khaleel ya dawo ko kallonta baiyi ba ya wuce dakinsa don wani irin haushi take basa…”

 

Washe Gari…..!!!

Tunda Ammi tayi sallar asuba bata koma ba don yau Monday akwai school, yaranta ta tada su tashi suyi sallah banda Hanifa dake ta bacci, Ammi tayi tayi ta tashe ta taki tashi dama tasan halin Hanifah ba abinda ya kai tashinta daga bacci wahala, wani lokaci harda iskancinta, Ammi ta kule karshe ta dage ta rafta mata bugu a cinya, a razane ta tashi bakinta cikeda tsiwa.
“Ammi bacci fa nakeji”
Ammi tace “zaki tashi ko sai na kara miki”
Da sauri ta tashi tayi toilet,
Nan ma sai da ta 6ata minutes da yawa kafin ta fito wanka, koda ta kammala shirinta nan ta hau neman socks dinta, dama kullum da abinda zai 6ata, su Khaleel har sun gama shiri sun yi breakfast ita kawai suke jira, cike da jin haushin Hanifah yayi dakinta, tun kafin ya shiga ya fara kwala mata kira da karfin tsiya.

Add Comment

Leave a Comment